An haifi Alhaji Umar Adamu da aka fi sani da Alhaji Sanda Adamu Tsafe a garin Tsafe, Jihar Zamfara a shekarar 1948. Ya yi karatun addinin Musulunci da na zamani a garin Tsafe. Ya halarci LEA Primary School, Tsafe da Senior Primary School, Kwatarkwashi da Makarantar Lardi ta Sakkwato (Nagarta College) da SBS /Ahmadu Bello University, Zaria da School of Journalism ta London inda ya koyi aikin Jarida.
Ya yi aikin Jarida a Gidan Rediyon BBC London da Radio Nigeria Kaduna har ma ya riƙe muƙamin Babban Manajan Gidan Rediyon Rima na Gwamnatin Jihar Sakkwato. Ya kuma riƙe muƙamin Kwamishinan Zaɓe mai kula da Birnin Tarayya, Abuja a Hukumar Zaɓe ta Ƙasa.
Masarautar Tsafe a lokacin mulkin Marigayi Mai martaba Yandoton Tsafe, Alh. Habibu Aliyu ta karrama shi da Sarautar "Sarkin Yaƙin Tsafe". Mutum ne mai himma da hazaƙa da basira da ya bayar da gudunmuwa wajen ci gaban addinin Musulunci da aikin jarida da kuma al'ummarsa.
Ya rasu a ranar Asabar, 8/2/25 yana da shekaru 77 a duniya, a Asibitin Koyarwa ta Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto sanadiyar rashin lafiya. Ya bar matan aure 2 da ya'ya /ɗiya 29 da jikoki 36. Allah ya jiƙan sa da rahama, amin.
Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara.
08149388452, 08027484815
birninbagaji4040@gmail.com
Lahadi, 09/02/2025.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.