A INA ALLAH YAKE?
Wannar tambaya tana kan hanya, hasali ma tambaya ce da Annabi (saw) ya taba yi ma wata baiwa, sai ta ba da amsa da cewa: "Allahn yana sama", sai Annabi (saw) ya yi mata shaida da cewa; lallai ita Mumina ce.
To amma duk da haka an samu wasu suna ganin -wai-
wannar tambaya ba ta dace ba - duk da cewa; Annabi (saw) ne ya fara yinta -,
suka ce ba a tambaya game da Allah da lafazin "a ina", saboda ana
tambaya ne da shi a kan wuri, -wai- Allahn kuma ba shi da wuri.
To wannar magana ba dadai ba ce. Saboda lafazin
tambaya "a ina" ana tambaya da shi ga dukkan abu samamme. Allah kuma
samamme ne.
Kuma shin me suke nufi da wuri?
Idan suna nufin wuri shi ne cikin wani abin
halitta, to sai mu ce: lallai haka ne, Allah ba ya cikin wani abu na halitta.
Amma in kuma suna nufin wuri shi ne SAMAN DUKKAN
HALITTA, sai mu ce: a'a, ba haka ba ne, lallai Allah yana da wuri bisa wannar
ma'ana, ta cewa yana saman dukkan halitta.
Saboda haka Allah Madaukaki yana SAMA.
To ina ne SAMAN?
Akwai wata tsohuwar shubuha ta Malaman Bidi'a masu
kore kasancewar Allah a sama, suke cewa: -wai- Allah ba a sama yake ba, saboda
in an ce a sama yake, to a wace saman, saman wace kasa kenan?
Saboda ai ita Duniya a mulmule take kamar kwallo,
saman kowace kasa daban yake, sama a wata kasar, kasa ne a wata kasar. Misali;
wadanda suke kudancin Duniya a kasa suke dangane da wadanda suke arewacin
Duniya. Haka su ma wadanda suke arewacin a kasa suke dangane da wadanda suke
kudancinta.
Saboda haka idan dan arewacin Duniya ya ce: Allah
yana sama, to zai zama a kasa yake a wajen wanda yake kudancin Duniya, haka
kuma idan ka juya abin.
Wannar shubuha kar a dauka sabuwa ce, a ce: an
gano ta ne bayan bayyanar ilimin Kimiyya wanda Turawan Yamma suka isa gare
shi. Wannan ya sa har na ga wani Malami
dan gidan Nasiru Kabara, ya dauko kwallon hoton Duniya yana baza wannar
shubuha. Alhali tun tuni, tun kusan shekara ta 600 bayan Hijira an samu
Fakhrudden al-Raziy ya baza wannar shubuha a cikin littatafansa, kuma tun tuni
Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya ya masa kwaf daya shi da shubuhar tasa.
Al-Raziy ya ce
"الحجة السادسة: العالم كرة، وإذا كان كذلك وجب أن لا يكون
في الجهة أصلا...
نقول: الجهة التي فوق رأسنا هي بعينها أسفل لأولئك الذين
يكونون على ذلك الوجه الآخر من الأرض. فلو كان تعالى فوقنا لكان أسفل بالنسبة إلى
سكان ذلك الجانب الآخر من الأرض. ولو كان فوقا لهم لكان أسفل بالنسبة إلينا. فثبت
أنه لو كان في جهة لوجب أن يكون أسفل بالنسبة إلى بعض الجوانب، ولما كان ذلك باطلا
ثبت أنه يمتنع كونه تعالى في المكان والجهة".
الأربعين في أصول الدين (1/ 160)
To a zahiri za ka yi zaton wannar wata hujja ce ta
a zo a gani, alhali ko kadan ba hujja ba ce, sai ka karanta raddin da Ibnu
Taimiyya ya yi masa za ka san cewa; wannar magana ce ta kuntataccen hankali da
tunani.
Na kawo wannar magana ce don kar a rudu, a dauka
abin da ake yadawa a yanzu wani sabon ilimi ne, wanda 'yan bidi'ar wannan
zamani suka gano ta hanyar ilimin Kimiyyan Turawa, a'a, tun tuni an yi maganar,
kuma tun tuni Ibnu Taimiyya ya kakkabe ta, ya bayyana jahilcin wannan tunanin.
Sai Ibnu Taimiyya ya yi masa raddi ta fiskoki masu
yawa, daga ciki ya ce
"والاعتراض على هذا من
وجوه
أحدها: أن يقال: القائلون بأن العالم كرة يقولون: إن المحيط
هو الأعلى، وإن المركز الذي هو جوف الأرض هو الأسفل، ويقولون: إن السماء عالية على
الأرض من جميع الجهات، والأرض تحتها من جميع الجهات.
ويقولون: إن الجهات قسمان: حقيقية وإضافية، فالحقيقية
جهتان: وهما العلو والسفل، فالأفلاك وما فوقها هو العالي مطلقا، وما في جوفها هو
السافل مطلقا.
وأما الإضافية فهي بالنسبة إلى الحيوان، فما حاذى رأسه كان
فوقه، وما حاذى رجليه كان تحته، وما حاذى جهته اليمنى كان عن يمينه، وما حاذى
اليسرى كان عن يساره، وما كان قدامه كان أمامه، وما كان خلفه كان وراءه.
وقالوا هذه الجهات تتبدل، فإن ما كان علوا له قد يصير سفلا
له، كالسقف مثلا: يكون تارة فوقه، وتارة تحته، وعلي هذا التقدير فإذا علق رجل جعلت
رجلاه إلى السماء ورأسه إلى الأرض، أو مشت نملة تحت سقف: رجلاها إلى السقف، وظهرها
إلى الأرض، كان هذا الحيوان باعتبار الجهة الحقيقية، السماء فوقه، والأرض تحته، لم
يتغير الحكم، وأما باعتبار الإضافة إلى رأسه ورجليه، فيقال: إن السماء والأرض فوقه".
درء تعارض العقل والنقل (6/ 327 - 328)
"Fiska ta farko: Masu cewa (Masana ilimin
Falaki "Astronomy"): Duniya a mulmule take kamar kwallo ai kuma sun
ce; sararin da yake kewaye da Duniyar shi ne sama, shi kuma cikin cikin Duniyar
(inda ake tonawa a binne mutum) shi ne kasa. Kuma suke cewa; sama a daukake
take a kan Duniya ta kowane bangare, Duniya kuma a karkashin saman take ta
kowane bangare.
Kuma suke cewa: Bangarori kashi biyu ne: Bangare
na hakika, da kuma bangare madanganci.
Bangare na hakika bangarori biyu ne;
"daukaka" da kuma "kasa". Taurari da abin da ke sama da su
duka daukaka ne (sama ne), amma abin da ke cikinsu (inda ake tonawa a binne
mutum) nan kuma shi ne kasa.
Amma bangare madanganci kuma shi ne: Idan an
danganta bangarorin zuwa ga halittu (mutane da dabbobi), bangaren da yake biye
da kan mutum shi ne bangaren sama, bangaren da yake biye da kafafunsa kuma shi
ne bangaren kasa, bangaren da yake biye da hanun damansa shi ne bangaren dama,
bangaren da yake biye da hanunsa na hagu shi ne bangaren hagu, bangaren da yake
biye da gabansa shi ne bangaren gaba, bangaren da yake biye da bayansa shi ne
bangaren baya. (Wato bangarori guda shida da suke dangance da mutum).
Kuma suka ce: Wadannan bangarori guda shida suna
iya canzawa, bangaren da yake sama da halitta zai iya zama a kasa da shi, kamar
rufi, wani lokacin zai iya zama sama da mutum, wani lokacin kuma ya zama a kasa
da shi. Bisa wannan idan aka rataye mutum, aka daure kafafunsa a sama, kansa
kuma yana reto ta kasa, ko idan tururuwa tana tafiya a jikin rufi ta cikin
daki, kafafunta suna manne da rufin, amma bayanta yana kallon kasa. To ka ga
wadannan halittu idan an yi la'akari da bangare na hakika to sama tana samansu
ne, kasa kuma tana karkashinsu ne, babu canji. Amma idan an yi la'akari da
bangare madanganci zuwa ga kansu da kafafunsu, sai a ce: sama da kasan duka sun
kasance a sama da su".
Abin nufi a nan, shi al-Raziy da ya tashi sai ya
yi la'akari da bangarori madanganta kawai, wadanda suke da alaka da kan mutum
da kafafunsa, sai ya manta da bangarori biyu na hakika - wato wadanda ba a
danganta su ga komai ba - wadanda suke nuni zuwa ga cewa; duk abin da yake
kewaye da kwallon Duniya da sauran Taurari duka sama ne ta kowane bangare, abin
da kuma ke cikin cikin Duniya (inda ake tonawa a binne mutum) shi ne kasa.
To a takaice, su masu wannar shubuha, suna gina
abin ne a kan Bangare Madanganci kawai, wato bangaren da yake biye da kan mutum
ko kafafunsa, alhali wannan ba shi ne bangare na hakika ba. Shi ya sa Ibnu
Taimiyya ya yi mana misali da mutumin da aka rataye kafafunsa a sama kansa yana
kasa, ko kuma tururuwa mai tafiya a jikin rufin daki, kafafunta suna manne da
rufin, bayanta kuma yana ta kasa. Kun ga a bisa wadannan misalai biyu, mun
fahimci ashe bangare madanganci ba shi ne bangare na hakika ba, saboda bangaren
yana iya canzawa, sama ya koma shi ne kasa. Alhali sama ta hakika ba ta
canzawa, kamar yadda kasa na hakika ba ta canzawa.
Don haka idan an ce: saman Duniya, to shi ne
dukkan sararin da ya kewaye Duniya ta kowane bangare. Kasan Duniya kuma shi ne
cikin cikinta, inda ake tona rami a binne mutum ko wani abu daban.
Saboda haka, idan an ce: saman wani bangare na
Duniya kasan wani bangaren ne daban, ba hujja ba ne na kore cewa; Allah yana
sama. Saboda wannan bangare ne madanganci, wanda ya danganta da kan mutum ko
kafafaunsa. Amma a bisa bangare na hakika, Allah yana saman Duniya da dukkan
taurari.
Za mu cigaba insha Allahu...
✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.