Ticker

6/recent/ticker-posts

Al'umma Maras Manufa A Rayuwa Tana Cikin Babban Hatsari Da Fiskantar Gagarumar Halaka

AL'UMMA MARAS MANUFA A RAYUWA TANA CIKIN BABBAN HATSARI DA FISKANTAR GAGARUMAR HALAKA

Alal hakika Allah ya haliccemu ne saboda manufa mai girma, ita ce mu bauta masa shi kadai ba tare da yi masa shirka ba.

Haka Allah (T) ya kasance, yana da hikima, kuma yana da nufi, duk abin da zai yi yana da manufa, kuma akwai hikima a cikinsa.

Haka su ma bayin Allah, Allah ya haliccesu ne don su zama masu manufa a cikin rayuwarsu, ba su zauna kara - zube babu manufa ba, shi ya sa ya halitta musu hankali da tunani da nufi.

Lallai babbar manufar da ya wajaba a kan mutane, al'ummominsu da daidaikunsu su nufeta a cikin rayuwarsu, ita ce; NEMAN RABO DA DAUKAKA DA TSIRA A RAYUWAR DUNIYA DA TA LAHIRA.

Saboda haka, duk al'ummar da ta wayi gari kara - zube, ba tsari, ba ta da shugabanni masu dattaku, masu manufar nema wa al'ummarsu rabo da tsira da daukaka da cigaba a duniya da lahira, jama'ar al'ummar suka zama ba su da manyan da suke ganin girmansu, kuma masu fada aji, kuma masu tsara masu makomarsu ta duniya da lahira, masu kokarin kare mata daukakarta da manufofinta da mutuncinta, da kokarin samar mata da cigaba a halin rayuwa, to alal hakika wannar al'umma tana cikin hatsari mai girman gaske, hatsarin da zai kaita ga halaka mai girma a duniya da lahira.

Wannan ya sa, a yau in ka dauki al'ummar Musulmin Arewacin Nigeria, al'umma ce da ta rasa manufa, ta rasa manya da shugabanni masu manufa kuma masu fada aji, wadanda za su iya shata mata makomarta a tattalin arziki da zamantakewa da siyasa, musamman a kasancewarta a kasa ta hadaka, wacce take da Addinai mabanbanta, da kabilu mabanbanta, da bangarori mabanbanta.

Yanzu in ka dauki sauran al'ummomin Nigeria, sai ka ga mabiya Addinin Kiristanci suna da shugabanci mai tasiri a kan mabiyansa, haka in ka dauki al'ummar Yorabawa sai ka samu suna da manufofi da shugabanci mai fada aji, haka Kabilar Igbo, su ma suna da manufofi da jagoranci mai kare musu manufofinsu, da sauran bangarori da kabilu na Nigeria, sawa'un manufofi na siyasa ko na zamantakewa ko na tattalin arziki ko na makobtaka da sauran al'ummomi, don samar musu da cigaba a cikin tarayyar Nigeria.

Amma in ka dawo kan Al'ummar Musulmin Arewacin Nigeria, sai ka samu ba ta da wata manufa a wannar rayuwa, musamman a kasancewarta tana zaune tare da bangarori daban - daban, ba ta da wani jagoranci na dattaku mai fada aji, mai kare mata daukakarta da mutuncinta, ya samar mata da cigaba da tsira a rayuwarta.

Alal hakika, wajibi ne a kan wadanda ake ganin su ne manya a cikin Al'ummar Musulmin Arewacin Nigeria, su tsaya su haddade MUNUFOFIN AL'UMMARSU, na sama mata rabo da daukaka da cigaba da tsira a duniya da lahira, sa'annan su yi kokarin dawo da martabarsu a cikin jama'ar al'ummarsu, har su zama masu iya fada aji, daga nan al'ummar za ta iya tashi ta tinkari duk wani kalu - bale, ta iya tsare jama'arta daga wannan bala'i da babban halaka da yake tinkarosu, ta dawo musu da daukaka da mutunci da 'yanci da kwarjini a idon sauran al'ummomi makobtanta.

In an ce manyan Arewa su ne; sarakunan gargajiya, da wadanda suka rike manyan mukaman gomnati a da, da wadanda suke rike da su a yanzu, da manyan malaman Addini, da manyan 'yan siyasa, da sauran shugabannin al'ummomi da suke da kima a idon jama'arsu.

Ya Allah ka kare wa al'ummar Musulmin Arewacin Nigeria mutuncinsu, ya Allah ka dawo musu da daukakarsu, ya Allah ka hada kansu a kan gaskiya, ya Allah ka ba su shugabanni masu manufa, manufar da za ta kai al'ummar zuwa ga samun rabo da daukaka da cigaba da tsira a rayuwarta na Duniya da Lahira.

Ya Allah ka yi mana tsari da fitinu, ya Allah ya karemu daga wannan babban bala'i da yake kokarin ganin bayan wannar al'umma mai albarka.

✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments