ANNABI MAI GASKIYA NE
Abu ne sananne a Addinin Muslunci, Musluncin mutum ba zai inganta ba matukar bai shaida Annabi Muhammad (saw) Manzon Allah ne ba. Dole sai ya yi imanin cewa; Annabi (saw) Allah ne ya aiko shi da sako ya isar ga mutane.
Kuma yana cikin Imani da Manzon Allah (saw) imani
da cewa; shi mai gaskiya ne, ba ya karya.
Lallai babu sabani a kan wannan tsakanin Musulmai.
To inda matsalar take shi ne; da yawa daga cikin
Musulmai ba su san hakikanin Shaidawa Annabi Muhammad (saw) Manzon Allah ne ba.
Sun dauka kawai shi ne shaidawa da baki kadai. Wannan ya sa Ibnu Taimiyya ya yi
mana bayani kamar haka ya ce
((الشهادة بأن محمدا رسول الله، تتضمن: تصديقه في كل ما أخبر،
وطاعته في كل ما أمر. فما أثبته وجب إثباته، وما نفاه وجب نفيه)).
اقتضاء الصراط المستقيم لمخالفة أصحاب الجحيم (2/ 374
- 375)
((Shaidawa cewa; Annabi Muhammad Manzon Allah ne
ya kunshi: Gaskata shi cikin dukkan abin da ya ba da labari. Da yi masa da'a
cikin dukkan abin da ya ba da umurni. Duk abin da Annabi (saw) ya tabbatar to
tabbatar da shi wajibi ne. Duk abin da ya kore to kore shi wajibi ne)).
To ka ga kenan a Shari'ance, ba za ka zama mai
shaidawa Annabi (saw) Manzon Allah ne ba, har sai ka gaskata shi a dukkan
labarin da ya bayar, kuma ka tabbatar da duk abin da ya tabbatar.
A hankale, idan ka yarda cewa; Malam Wane mutum ne
mai gaskiya. To ma'anar hakan shi ne; duk abin da ya fada za ka gaskata shi, ka
yarda da shi.
Saboda haka matukar ka yarda Annabi (saw) mai
gaskiya ne, to dole ka gaskata shi. Idan har ba za ka gaskata abin da ya fada
ka yarda da shi ka tabbatar da shi ba, miye amfanin shaidawarka Annabi mai
gaskiya ne?
Shaikhul Islami ya ce
((ومن المعلوم أن العلم بأنه صادق مقصوده تصديق أخباره،
والمقصود بتصديق الأخبار التصديق بمضمونها، فإذا كان لم يصدق بمضمون أخبار الرسول
صلى الله عليه وسلم، كان بمنزلة من آمن بالوسيلة، ولم يحصل له المقصود.
ولو قال الحاكم: إن هؤلاء الشهود صادقون في كل ما يشهدون
به، وهو لا يثبت بشهادة أحد منهم حقا، لم يكن في تعديلهم فائدة))
درء تعارض العقل والنقل (5/ 338)
((Abu ne sananne, sanin cewa; Annabi (saw) mai
gaskiya ne, amfanin hakan shi ne gaskata shi cikin dukkan Hadisansa. Abin nufi
da gaskata Hadisansa shi ne gaskata abin da suka kunsa na labarin da ya bayar.
Idan mutum bai gaskata abin da Hadisan Annabi (saw) suka kunsa ba to ya zama
tamkar wanda ya yarda da hanyar samun abu ne, amma kuma bai samu biyan bukatar
samun abun ba.
(Misali a kan haka): Idan Alkali ya yarda da
shaidun da aka gabatar a gabansa, ya ce: wadannan shaidun masu gaskiya ne a
dukkan shaidar da za su bayar, amma kuma da suka bayar da shaidar bai karbi
shaidar ko daya daga cikinsu a matsayin gaskiya ce ba, to ina amfanin shaidar
da ya yi musu a farko cewa; su masu gaskiya ne?)).
Saboda haka ashe matukar za ba za mu gaskata
Annabi (saw) a labarun da ya ba mu a Hadisansa ba, kowane irin labari da ya
bayar, sawa'un na Siffofin Allah ne, ko na al'ummomi da suka gabata, ko na abin
da zai zo nan gaba, ko labarin makomar wasu mutane a Lahira, to shaidawarmu
gare shi a matsayin Manzon Allah tauyayye ne matuka. Haka kuma fadinmu cewa;
shi mai gaskiya ne ba shi da amfani. Saboda da ma amfanin hakan shi ne mu
gaskata shi, mu yarda da abin da ya fada, mu tabbatar da abin da ya tabbatar.
✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.