Ticker

6/recent/ticker-posts

Bidi'a Ita Ce Kirkira A Addini

BIDI'A ITA CE ƘIRƘIRA A ADDINI

Addini shi ne abin da Manzon Allah (saw) ya zo mana da shi daga wajen Allah a cikin Alkur'ani da Sunna. Duk abin da suka yi nuni a kansa yana cikin Addini, duk abin da kuma ya saba musu ya zama Bidi'a.

Allah ya ce

{ أَمْ لَهُمْ شُرَكَاءُ شَرَعُوا لَهُمْ مِنَ الدِّينِ مَا لَمْ يَأْذَنْ بِهِ اللَّهُ } [الشورى: 21]

"Ko suna da wasu abokan tarayya wa Allah ne, suka shar'anta musu abubuwa na Addini, abin da Allah bai yi izni da shi ba?".

Annabi (saw) ya ce

«من أحدث في أمرنا هذا ما ليس فيه، فهو رد» البخاري ومسلم

"Duk wanda ya fari wani abu a cikin wannan lamari namu na Addini abin ba ya cikinsa to an mayar masa".

Bidi'a ta kasu kashi biyu

1- Bidi'o'in Aqida.

Dalili a kan Bidi'a ta Aqida shi ne fadin Annabi (saw)

«إن بني إسرائيل تفرقت على ثنتين وسبعين ملة، وتفترق أمتي على ثلاث وسبعين ملة، كلهم في النار إلا ملة واحدة»، قالوا: ومن هي يا رسول الله؟ قال: «ما أنا عليه وأصحابي»

سنن الترمذي ت شاكر (5/ 26)

"Lallai Bani Isra'ila sun rarrabu kungiya 72, al'ummata kuma za ta rarrabu kungiya 73, dukkansu sun cancanci shiga wuta sai dai Kungiya guda daya".

Sai suka ce: wacce ce ya Manzon Allah?

Sai ya ce: "Abin nake kai Ni da Sahabbaina".

Ahlus Sunna tsantsa su ne wadanda suke kan abin da Annabi (saw) da Sahabbansa suke kai, a Babin Tauhidi da Manzanci da Qaddara da Mas'alolin Imani da da'a ma shugabanni da matsayin Sahabbai da makamantansu.

Amma wadanda suka saba musu na kungiyoyin Sufaye, Asha'ira, Khawarijawa, Mu'utazilawa, Qadariyya, Murji'a, Jahamiyya da Rafidha da dukkan rassansu da kungiyoyinsu 'Yan Bidi'a ne ta Aqida. Hukunce - hukuncensu yana banbanta, kowanne gwargwadon nisansa daga Usul na Addini da kusacinsu da su, kuma gwargwadon girman Bidi'o'in nasu da Tawile - tawilensu, da kuma banbancinsu wajen karban Nassi da binsa da kuma jefar da shi. Da kuma gwargwadon kubutan Ahlus Sunna daga sharri da Ta'addancinsu a magana da aiyuka ko rashinsa.

2- Bidi'o'i na Aiki.

Dalili a kan Bidi'a ta Aiki shi ne fadin Annabi (saw)

«من عمل عملا ليس عليه أمرنا فهو رد» صحيح مسلم

"Duk wanda ya aikata wani aiki wanda babu umurninmu a kansa to an mayar masa".

Wannan ya sa yana daga cikin Ka'idojin Fiqhun Malaman Sunna

الأصل في العبادات الحظر والمنع، والأصل في المعاملات والعادات الإباحة

"Asali a Ibada shi ne hani (ba za a aikata Ibada ba sai akwai dalili na Shari'a), asali kuma a Mu'amala da Al'adu shi ne halasci".

Don haka ba za a shar'anta komai a Addini ba sai abin da Allah ya shar'anta a cikin Littafinsa ko Sunnar Manzonsa (saw), haka ba za a haramta komai na Mu'amala da Al'adu ba sai abin da Allah ya haramta cikin Littafinsa ko ta harshen Manzonsa (saw).

Saboda haka wajibi ne mu nisanci Bidi'o'in Aqida, na ra'ayoyin Sufaye, 'Yan Shi'a, Khawarijawa, Mu'utazilawa da Jahamiyya da makamantansu. Kuma mu nisanci Bidi'o'i na aiki kamar Bidi'ar Maulidi da makamancinta, saboda Bidi'o'i da fararrrun abubuwa cikin Addini sharri ne da bata

«وشر الأمور محدثاتها، وكل بدعة ضلالة» صحيح مسلم

✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments