DA MUNGUWAR RAWA GARA ƘIN TASHI… (6)
TSAKANIN SAYYID QUTUB DA DR. SANI R/LEMO
Tun bayan bayyana cewa; Akidar Sayyid Qutub Akida ce ta Khawarijawa, saboda ya tabbatar da cewa; Hakikanin Imani da Addini abu ne dunkulalle, wanda ba ya rarrabuwa, Mabiya Sayyid Qutub suka kasa zaune suka kasa tsaye, suna ta kame - kamen shubuhohi a dole sai sun kare shi. Daga cikin wadannan shubuhohin akwai wata magana ta Dr. Sani R/Lemo da suka samu, wacce suka raya cewa magana ce iri daya da ta Sayyid Qutub ba banbanci. Don haka suke kafa hujja da maganar ta Dr. Sani don nuna cewa; maganar Sayyid Qutub daidai ce.
To a bisa hakika maganar Dr. Sani tarjama ce ta
maganar Sayyid Qutub. Ga asalin maganar ta Sayyid Qutub kamar haka inda ya ce
((إن شريعة الله كل لا يتجزأ. كل متكامل.
سواء فيه ما يختص بالتصور والاعتقاد وما يختص بالشعائر
والعبادات وما يختص بالحلال والحرام وما يختص بالتنظيمات الاجتماعية والدولية. وأن
هذا في مجموعه هو «الدين» الذي يقول الله عنه في هذه الآية
إنه أكمله. وهو «النعمة» التي يقول الله للذين آمنوا: إنه
أتمها عليهم. وأنه لا فرق في هذا الدين بين ما يختص بالتصور والاعتقاد وما يختص
بالشعائر والعبادات وما يختص بالحلال والحرام وما يختص بالتنظيمات الاجتماعية
والدولية.. فكلها في مجموعها تكوّن المنهج الرباني الذي ارتضاه الله للذين آمنوا
والخروج عن هذا المنهج في جزئية منه، كالخروج عليه كله، خروج على هذا «الدين»
وخروج من هذا الدين بالتبعية..)).
في ظلال القرآن (2/ 841)
Idan an duba wannar magana ta Sayyid Qutub, aka
kuma duba maganar Dr. Sani wacce take rubuce a hoton da yake kasan wannan
rubutu, za a tabbatar cewa; maganar Dr. Sani tarjama ce ta maganar Sayyid
Qutub.
Shi dai Sayyid Qutub ya yi maganar tasa ce a
karkashin Ayar
{الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ
نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ دِينًا} [المائدة: 3]
Amma ban san karkashin wace Aya ce Dr. Sani ya yi
tasa maganar ba.
To su dai masu kare Sayyid Qutub suna kafa hujja
ne da dacewar Dr. Sani da Sayyid Qutub a kan maganar tasa, alhali wannan ba
hujja ba ne saboda dalilai kamar haka
1- A ka'ida ta Ilimi mujarradin maganar Dr. Sani
ba hujja ba ce, ita ma kanta tana bukatar a nema mata hujja, balle kuma da ma
ita ma tarjama ce ta maganar Sayyid Qutub din.
2- Idan an lura, Dr. Sani ba tarjama kai tsaye ya
yi wa maganar Sayyid Qutub ba, a'a, ya yi kwaskwarima da gyara wa Sayyid Qutub,
inda Dr. Sani ya cire Khawarijancin da ke cikin maganar ta hanyoyi guda biyu
A) Ya yi amfani da kalmar "Yarda", a
inda Dr. ya ce
((... A yarda da wani bangare, a yi watsi da wani;
dole ne a yarda da shi a dunkulensa...)).
Idan an ce yarda, wannan shi ake kira da (الإقرار والاعتقاد والتصديق القلبي). Wato
shi ne gaskatawa da yin imani da shi da yarda da shi a zuciya. Shi ya sa Allah
ya ce
{أَفَتُؤْمِنُونَ بِبَعْضِ الْكِتَابِ وَتَكْفُرُونَ بِبَعْضٍ}
[البقرة: 85]
((Shin za ku yi imani da bangare na Littafi, ku
kafirce ma wani bangaren?)).
Shi ya sa Ibnu Jarir ya fassara "Imani"
a cikin wannar Ayar da gaskatawa (التصديق), inda
ya ce: (فتصدقون به), "kafirci" kuma ya fassara da ma'anar
"musawa" (الجحود), inda ya ce: (فتجحدونه). Ga maganar tasa kamar haka
((أفتؤمنون ببعض الكتاب - الذي فرضت عليكم فيه فرائضي، وبينت
لكم فيه حدودي، وأخذت عليكم بالعمل بما فيه ميثاقي - فتصدقون به، فتفادون أسراكم
من أيدي عدوكم; وتكفرون ببعضه، فتجحدونه)).
تفسير الطبري = جامع البيان ت شاكر (2/
309)
Don haka a nan gaskatawa ake nufi, mutum ba zai yi
imani na gaskatawa da shashe ya kafirce da sashe ba. Dole ne ya yarda da
Shari'ar Muslunci gaba dayanta, ya gaskata dukkan abin da Allah ya saukar. Ba
zai yiwu ya yarda da sashe ya ki yarda da wani sashe ba, ko da kuwa a aikace
yana saba Shari'ar. Misali mutum ya yarda zina haramun ne, amma kuma yana
aikatawa. Wannan ba zai fitar da shi daga Muslunci ba, sabanin yadda lamarin
yake a wajen Khawarijawa. Su kam idan ka bar wani bangare to ka fita daga Muslunci,
kamar yadda Sayyid Qutub ya ce
((يصبح المنهج الإلهي وحدة واحدة. لا تتجزأ ولا تتفرق. ويصبح
ترك جانب منه وإعمال جانب، إيماناً ببعض الكتاب وكفراً ببعض.. فهو الكفر في
النهاية)).
في ظلال القرآن (1/ 177)
Ka ga a nan sai Sayyid Qutub ya nuna cewa;
Manhajin Allah, wato Shari'a kenan, abu ne guda daya, ba ya rarrabuwa. Idan
mutum ya bar wani bangare nasa ya aikata wani bangare to kafirci ne, saboda
imani ne da sashe, da kafirce ma sashe.
To ka ga a nan Sayyid Qutub ya dauki Ayar da take
magana a kan Imani na gaskatawa, da kafirci na musawa da inkari ya dora shi a
wajen barin aiki da wani bangare na Shari'a, alhali barin aikata wani bangare
na Shari'a ba kafirci ba ne, ba ya fitar da mutum kai tsaye daga Muslunci, sai
wasu daga cikin aiyuka sanannu, wadanda suka tabbatar barinsu kafirci ne, kamar
barin Sallah d.s. Ma'ana ba kowane abu ne barinsa a Shari'a yake fitar da mutum
daga Muslunci ba, sabanin abin da Sayyid Qutub ya fada. Don haka cewa; barin
aikata wani bangare na Shari'a kafirci ne, wannar Akida ce ta Khawarijawa.
A wani wajen kuma ya ce
((والإسلام منهج للحياة كلها. من اتبعه كله فهو مؤمن وفي دين
الله. ومن اتبع غيره ولو في حكم واحد فقد رفض الإيمان واعتدى على ألوهية الله،
وخرج من دين الله. مهما أعلن أنه يحترم العقيدة وأنه مسلم. فاتباعه شريعة غير
شريعة الله، يكذب زعمه ويدمغه بالخروج من دين الله.))
في ظلال القرآن (2/ 972)
A nan ma sai Sayyid Qutub ya nuna cewa; Muslunci
tsarin rayuwa ne gaba dayanta, sai wanda ya bi shi gaba daya ne zai zama
Mumini. Wanda kuma ya bi wani abu ba Muslunci ba a rayuwarsa, ko da a hukunci
ne guda daya to ya yi watsi da imanin, kuma ya fita daga Addinin Muslunci, ko
da ya ce: shi Musulmi ne, kuma yana girmama Akidar Muslunci.
To ka ga a nan, tunda Dr. Sani ya yi amfani da
kalmar "YARDA", to ya nuna cewa: GASKATAWA yake nufi, don haka
maganarsa ba ta da matsala. Sabanin maganar Sayyid Qutub wacce ta ginu a kan
aiki ba gaskatawa kawai ba.
B ) Dr. Sani ya cire karshen maganar Sayyid wacce
take kunshe da Khawarijancin, inda Sayyid din ya ce
((والخروج عن هذا المنهج في جزئية منه، كالخروج عليه كله،
خروج على هذا «الدين» وخروج من هذا الدين بالتبعية..))
((Fita daga wannan tsari a wani GUTSURE nasa,
kamar fita ne daga tsarin gaba dayansa, tawaye ne ga wannan Addini, fita ne
daga wannan Addini, saboda gutsuren yana bin dukkan Addinin ne)).
Ka ga wannar magana tana da hatsari, Khawarijanci
ne tsantsa. Saboda ya nuna idan mutum ya bar abu daya, wani juz'i na Shari'a,
bai yi aiki da ita ba to ya fita daga Addini.
To ka ga wadannan abubuwa guda biyu su suke nuna
cewa; Dr. Sani ya saba ma Sayyid Qutub, ya yi gyara wa maganarsa don ta dace da
Akidar Ahlus Sunna.
Saboda haka da a ce masu kare Sayyid Qutub suna da
lura, da za su ga cewa; ashe maganar Dr. Sani raddi ce ga Sayyid Qutub a
fakaice, ya juya maganarsa ta Khawarijanci ta koma Sunnanci. Dr. Sani tsarki ya
yi wa maganar Sayyid Qutub.
Saboda haka babu wanda zai ce maganar Dr. Sani da
ta Sayyid Qutub kwabo da kwabo suke sai gafili wanda ba ya fahimtar jance ko
kuma da ma jahili ne.
Kuma wannan shi yake nuna maka illar da ke cikin
littatafan Sayyid Qutub, "Fi Zilal" dinsa kamar Tafsirin
al-Zamakhshariy yake, mutumin da ba Malami masani ko Dalibi mai basira ba, idan
ya ce zai karanta shi to Bidi'o'i kawai zai kwankwandi ba tare da ya sani ba.
Saboda haka wannar Shari'ar da za a yarda da ita,
a gaskata ta, idan aka ce a dunkule take ba ta rarrabuwa, to abin nufi shi ne;
mutum ba zai yi imani ya gaskata shashe na Shari'ar ya kafirce da sashe ba.
Ma'ana; ba za ka rarraba Shari'ar ka yarda da wani bangare ka ki yarda da wani
bangare nata ba. Don haka ba za a karbi gaskatawan daga gare ka a tauye ba,
dole sai ka gaskata Shari'ar a kammalenta a hade gaba daya. Kamar yadda ya zo a
Ayar Baqara da ta gabata.
Amma kuma duk da haka shi wannan gaskatawan a
hakikaninsa yana rarrabuwa zuwa ga abubuwan da suka wajaba a yi imani da su, a
yarda da su, kuma yana karuwa ta hanyar karfi kamar yadda yake raguwa idan
gaskatawar ta yi rauni. Wannan ya sa Imanin Annabawa na gaskata Allah da
Maganarsa da Shari'arsa ba dadai yake da gaskatawa da imanin sauran bayi ba.
Haka na Sahabbai ba dadai yake da na sauran al'umma ba. Haka na Abubakar (ra)
ba dadai yake da na sauran Sahabbai ba. Imam al-Nawawiy ya ce
((إن نفس التصديق يزيد بكثرة النظر وتظاهر الأدلة، ولهذا يكون
إيمان الصديقين أقوى من إيمان غيرهم، بحيث لا تعتريهم الشبه ولا يتزلزل إيمانهم
بعارض، بل لا تزال قلوبهم منشرحة نيرة، وإن اختلفت عليهم الأحوال. وأما غيرهم من
المؤلفة ومن قاربهم ونحوهم فليسوا كذلك، فهذا مما لا يمكن إنكاره، ولا يتشكك عاقل
في أن نفس تصديق أبي بكر الصديق رضي الله عنه لا يساويه تصديق آحاد الناس. ولهذا
قال البخارى فى صحيحه: {قال بن أبي مليكة: "أدركت ثلاثين من أصحاب النبي صلى
الله عليه وسلم كلهم يخاف النفاق على نفسه، ما منهم أحد يقول إنه على إيمان جبريل
وميكائيل"})).
شرح النووي على مسلم (1/ 148 - 149)
Imam al-Nawawiy sai ya tabbatar da cewa;
gaskatawan zuciya yana karuwa, kuma yana raguwa, kuma akwai fifiko tsakanin
mutane a cikinsa, don haka ashe yana rarrabuwa kenan.
Haka Ibnu Taimiyya ya tabbatar da haka inda ya ce
((إن التصديق نفسه يتفاضل كنهه؛ فليس ما أثنى عليه البرهان بل
تشهد له الأعيان وأميط عنه كل أذى وحسبان حتى بلغ أعلى الدرجات؛ درجات الإيقان
كتصديق زعزعته الشبهات وصدفته الشهوات ولعب به التقليد ويضعف لشبه المعاند العنيد،
وهذا أمر يجده من نفسه كل منصف رشيد)).
مجموع الفتاوى (6/ 480 - 481)
Kuma ya ce
((إن العلم والتصديق نفسه يكون بعضه أقوى من بعض وأثبت وأبعد
عن الشك والريب، وهذا أمر يشهده كل أحد من نفسه؛ كما أن الحس الظاهر بالشيء الواحد
مثل رؤية الناس للهلال وإن اشتركوا فيها فبعضهم تكون رؤيته أتم من بعض؛ وكذلك سماع
الصوت الواحد وشم الرائحة الواحدة وذوق النوع الواحد من الطعام، فكذلك معرفة القلب
وتصديقه يتفاضل أعظم من ذلك من وجوه متعددة. والمعاني التي يؤمن بها من معاني
أسماء الرب وكلامه يتفاضل الناس في معرفتها أعظم من تفاضلهم في معرفة غيرها)).
مجموع الفتاوى (7/ 234)
Sai Ibnu Taimiyya ya nuna cewa gaskatawan zuciya
kansa yana da fifiko a hakikaninsa, daraja - daraja yake, yana karuwa ya yi karfi,
kuma yana raguwa ya yi rauni. Don haka hakikaninsa yana rarrabuwa, ba kawai abu
daya ne da yake dunkule ba.
Wadannan Imaman da ma wasunsu duka sun tabbatar da
cewa; Imanin da ke zuciya "iqrari da gaskatawa" ba abu ne guda daya
dunkulalle wanda ba ya rarrabuwa ba, a'a, yana rarrabuwa, shi ya sa yake karuwa
da raguwa ta hanyar karfi ko raunin Imani da yakini da ilimin da suke zuciya.
Amma duk wanda zai ce: Imani na gaskatawan zuciya
abu ne wanda hakikaninsa ba ya rarrabuwa to wannan ra'ayi ne na 'Yan Bidi'a
Murji'a, ga maganarsu kamar haka kamar yadda Ibnu Taimiyya ya hakaito
((قالت "المرجئة والجهمية": ليس الإيمان إلا شيئا
واحدا لا يتبعض؛ إما مجرد تصديق القلب كقول الجهمية أو تصديق القلب واللسان كقول
المرجئة، قالوا: لأنا إذا أدخلنا فيه الأعمال صارت جزءا منه، فإذا ذهبت ذهب بعضه،
فيلزم إخراج ذي الكبيرة من الإيمان، وهو قول المعتزلة والخوارج)).
مجموع الفتاوى (7/ 510)
Kuma bayan ya yi raddi ga Akidar Murji'an sai ya
ce
((وبهذا وغيره يتبين فساد قول جهم والصالحي ومن اتبعهما في
"الإيمان" كالأشعري في أشهر قوليه وأكثر أصحابه وطائفة من متأخري أصحاب
أبي حنيفة كالماتريدي ونحوه، حيث جعلوه مجرد تصديق في القلب يتساوى فيه العباد،
وأنه إما أن يعدم، وإما أن يوجد لا يتبعض)).
مجموع الفتاوى (7/ 582)
Ka ga sai Murji'a suka ce: Imani shi ne gaskatawan
zuci, kuma ba ya rarrabuwa.
Ibnu Hazm ma yana cikin Murji'a shi ya sa ya
tabbatar da cewa; lallai gaskatawan ba ya rarrabuwa inda ya ce
((قال أبو محمد: ولو نقص من التصديق شيء لبطل عن أن يكون
تصديقا لأن التصديق لا يتبعض أصلا، ولصار شكا. وبالله تعالى التوفيق. وهم مقرون
بأن امرأ لو لم يصدق بآية من القرآن أو بسورة منه وصدق بسائره لبطل إيمانه، فصح أن
التصديق لا يتبعض أصلا))
الفصل في الملل والأهواء والنحل (3/ 110)
A takaice, duk mai ilimi, wanda ya san "Babin
Mas'alolin Imani" (باب مسائل الإيمان), ko
mai lura ba gafili ba, idan ya karanta maganar Sayyid Qutub da maganar Dr. Sani
ya san akwai banbanci tsakaninsu.
Eh, gaskiya ne, maganar Sayyid Qutub ce Dr. Sani
ya dauko ta, amma kuma ya yi mata gyara, maganar ta canza daga maganar da take
bisa Akidar Khawarijawa, zuwa ga maganar da ba ta saba Mazhabar Ahlus Sunna a
Babin Hakikanin Imani ba.
Don haka masu kare Sayyid Qutub bisa Akidarsa ta
Khawarijanci ku hakura da wannar shubuhar ku nemo wata.
✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.