Ticker

6/recent/ticker-posts

Da Munguwar Rawa Gara Kin Tashi – Kashi Na Bakwai

DA MUNGUWAR RAWA GARA ƘIN TASHI… (7)

KARIN DALILAI DA SUKE TABBATAR DA CEWA: AQIDAR SAYYID QUTUB TA KHAWARIJAWA CE

Idan ba a manta ba, tun bayan lokacin da masu kare barnar Sayyid Qutub suka fara tuhumar Manyan Malaman Sunna da Akidar Sayyid Qutub ta "Hakimiyya" muka yi kokarin banbance tsakanin tafarkin Sayyid Qutub daga tafarkin wadancan Malamai ta hanyar bayyana Akidarsu ta Sunna, shi kuma muka tabbatar da cewa Akidarsa ta Khawarijawa ce, saboda dalilai kamar haka

1- Kasancewar ya tabbatar da Akidar Khawarijawa a "Hakikanin Imani", wato ya ce: Imani abu ne guda daya dunkulalle, ba ya rarrabuwa, idan mutum ya bar wani yanki nasa to ya fita daga Muslunci.

2- Kasancewar ya kafirta dukkan al'ummar Musulmi, don cewa ya yi: dukkan Mutanen Duniya (البشرية) gaba daya sun koma Jahiliyya sun yi ridda daga Addinin Muslunci.

To a yau kuma da iznin Allah za mu kara kawo wasu dalilan ne da suke kara tabbatar da Akidar tasa ta Khawarijawa ce. Ga su kamar haka

1) Sukarsa ga mas'alar karuwar Imani da raguwarsa.

2) Kore samuwar Mumini mai raunin Imani.

3) Ba ya ganin halascin Sallar Juma'a.

4) Yankan Musulmai kamar yankan Ahlul Kitabi ne, saboda ba musulmai ba ne.

Kowane daya daga cikin wadannan yana daga cikin Akidun Khawarijawa, wadanda rassa ne na abubuwa guda biyu da muka ambata a baya na tushen Khawarijanci.

Za mu dauki wadannan daya bayan daya mu tabbatar da su da iznin Allah.

(1) SUKAR AKIDAR KARUWAR IMANI DA RAGUWARSA

Abu ne sananne a Akidar Ahlus Sunna cewa Imani yana karuwa kuma yana raguwa, saboda dalilai masu yawa na Shari'a. Saboda su Ahlus Sunna a wajensu Imanin rassa ne, yana rarrabuwa. Kamar yadda Annabi (saw) ya ce

«الإيمان بضع وستون شعبة، والحياء شعبة من الإيمان» وفي رواية: «بضع وسبعون شعبة».

صحيح البخاري (1/ 11) صحيح مسلم (1/ 63)

((Imani rassa sittin da wani abu ne, - ko saba'in da wani abu - kunya reshe ne na Imani)).

Shaikhul Islami yana bayanin tushen da a kansa Ahlus Sunna suka gina Akidarsu a Hakikanin Imani sai ya ce

((وأصلهم أن الإيمان يتبعض فيذهب بعضه ويبقى بعضه كما في قوله عليه الصلاة والسلام {يخرج من النار من كان في قلبه مثقال ذرة من إيمان}، ولهذا مذهبهم أن الإيمان يتفاضل ويتبعض، هذا مذهب مالك والشافعي وأحمد وغيرهم)).

مجموع الفتاوى (18/ 270)

((Tushen Akidar Ahlus Sunna; Imani yana rarrabuwa, sashensa yana tafiya, sashe ya saura, kamar yadda Annabi (saw) ya ce: {Wanda akwai kwatankwacin kwayar zarra na imani a zuciyarsa zai fita daga wuta (ba zai dawwama a cikinta ba, saboda shi ba kafiri ba ne)}. Wannan ya sa Mazhabar Ahlus Sunna ita ce: Imani yana fifiko, kuma yana rarrabuwa, wannan shi ne Mazhabar Malik, Shafi'iy da Ahmad da wasunsu)).

A dalilin Imani yana rarrabuwa rassa – rassa shi ya sa ya zama za a iya rasa reshi na imanin, sai imanin ya ragu, idan kuma wannan reshen da aka rasa ya dawo sai imanin ya karu. Maganganun jagororin Sunna a kan haka suna da yawa, inda suka ce: «الإيمان قول وعمل، يزيد وينقص، حتى لا يبقى منه شيء»

Saboda Nassoshi masu yawa da suka zo suka tabbatar da haka.

Amma kasancewar Murji'a da Khawarijawa da Mu'utazila sun gina Akidarsu game da Hakikanin Imani a kan cewa; Imani abu ne guda daya a dunkule, ba ya rarrabuwa, shi ya sa suka ce: Imanin ba ya karuwa, kuma ba ya raguwa. Sai Murji'a suka ce: Idan bangare na Imanin ya tabbata ga mutum to cikakken Imanin ya tabbata. Su kuma Khawarijawa da Mu'utazila suka ce: Idan bangare na Imani ya tafi, aka rasa shi to an rasa Imanin gaba daya, mutum ya zama kafiri. Shi ya sa suke kafirta duk wanda ya aikata sabo. Khawarijawan zamani kuma, wadanda suka tasirantu da Fikrorin Sayyid Qutub suke kafirta Musulmai da abin da bai kai kafirci ba, karkashin Mafhumin "Hakimiyya" a wajensu.

Wannan ya sa a wajen Murji'a da Khawarijawa Imani ba ya raguwa kuma ba ya karuwa, sai suka saba ma Alkur'ani da Sunna da Ijma'in Salaf Ahlus Sunna a kan haka.

To idan mun duba mas'alar a wajen Sayyid Qutub kuma za mu ga shi kuma bai ba wa mas'alar muhimmanci ba, sai ya nuna cewa; kawai wata kadhiyya ce ta Ilmul Kalam, aka tattauna ta lokacin walwalar hankali da kuma rashin bai wa aiki muhimmanci. Ya fadi haka ne a "hashiya" a cikin littafinsa, inda ya ce

((هنا تعرض قضية: «الإيمان يزيد وينقص» وهي قضية من قضايا الفرق وقضايا علم الكلام في فترة الترف العقلي والفراغ من الاهتمامات العملية الجادة.. فلا ندخل نحن الآن فيها!!!))

في ظلال القرآن (3/ 1475)

Lallai wannar magana ba dadai ba ce, mas'alar karuwan Imani da raguwarsa Alkur'ani da Sunna ne suka zo da ita, Salaf suka yi Ijma'i a kanta. Babu masu inkarinta ko sukarta sai 'Yan Bidi'a.

(2) KORE SAMUWAR MUMINI MAI RAUNIN IMANI

Mas'alar farko da aka fara sabani a kanta a cikin al'umma ita ce mas'alar "Mumini mai sabo", inda al'umma ta kasu kashi uku

a) Khawarijawa suka ce: Mutane biyu ake da su, Imma Mumini ko Kafiri.

b) Mu'utazilawa su ma suka ce: Mutane biyu ake da su, Imma Mumini ko kuma wanda yake "Manzila baina Manzilataini", wato; wanda ya fita daga Imani amma bai shiga kafirci ba. Ma'ana; yana tsakanin Imani da kafirci.

c) Su kuma Ahlus Sunna suka ce: Mai sabo Mumini ne amma mai tauyayyen Imani.

Ibnu Taimiyya yana bayanin Akidar Ahlus Sunna a cikin "Wasidiyya" sai ya ce

((ولا يسلبون الفاسق الملي اسم الإيمان بالكلية ولا يخلدونه في النار كما تقوله المعتزلة، بل الفاسق يدخل في اسم الإيمان في مثل قوله تعالى: {فتحرير رقبة مؤمنة}، وقد لا يدخل في اسم الإيمان المطلق كما في قوله تعالى: {إنما المؤمنون الذين إذا ذكر الله وجلت قلوبهم وإذا تليت عليهم آياته زادتهم إيمانا}، وقوله صلى الله عليه وسلم: {لا يزني الزاني حين يزني وهو مؤمن ولا يسرق السارق حين يسرق وهو مؤمن ولا يشرب الخمر حين يشربها وهو مؤمن ولا ينتهب نهبة ذات شرف يرفع الناس إليه فيها أبصارهم حين ينتهبها وهو مؤمن}. ويقولون: هو مؤمن ناقص الإيمان، أو مؤمن بإيمانه فاسق بكبيرته؛ فلا يعطى الاسم المطلق، ولا يسلب مطلق الاسم)).

مجموع الفتاوى (3/ 151 - 152)

A wani wajen kuma ya ce

((قوله صلى الله عليه وسلم: {لا يدخل الجنة إلا نفس مؤمنة} حق، إذا أريد به الدخول المطلق الكامل أريد بالمومن الكامل المطلق، وإذا أريد بالدخول مطلق الدخول فقد يتناول الدخول بعد العذاب، فإنه يراد به مطلق المؤمن، حتى يتناول الفاسق الذي في قلبه مثقال ذرة من إيمان، فإن هذا يدخل في مطلق المومن كقوله تعالى: {فتحرير رقبة مؤمنة}، ولا يدخل في المؤمن المطلق كقوله تعالى: {إنما المؤمنون الذين إذا ذكر الله وجلت قلوبهم وإذا تليت عليهم آياته زادتهم إيمانا} الآية.

ومثل هذا كثير في الكتاب والسنة ينتفى الاسم عن المسمى تارة لنفي حقيقته وكماله، ويثبت له تارة لوجود أصله وبعضه)).

مختصر الفتاوى المصرية (ص: 206)

A bayanin Ibnu Taimiyya ya bayyana mana cewa; Muminai nau'i biyu suke

1. Mumini mai cikakken Imani (المؤمن المطلق) (المؤمن حقا) (المؤمن كامل الإيمان).

2. Mumini mai tauyayyen Imani (مطلق المؤمن) (مؤمن ناقص الإيمان) (مؤمن بإيمانه فاسق بكبيرته).

To amma shi kuma Sayyid Qutub da ya zo yana magana a kan wannar Ayar

{إِنَّمَا الْمُؤْمِنُونَ الَّذِينَ إِذَا ذُكِرَ اللَّهُ وَجِلَتْ قُلُوبُهُمْ وَإِذَا تُلِيَتْ عَلَيْهِمْ آيَاتُهُ زَادَتْهُمْ إِيمَانًا وَعَلَى رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ (2) الَّذِينَ يُقِيمُونَ الصَّلَاةَ وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنْفِقُونَ (3) أُولَئِكَ هُمُ الْمُؤْمِنُونَ حَقًّا} [الأنفال: 2 - 4]

Sai ya kore samuwar duk wani Mumini in ba wanda yake nau'i na farko ba, wato; Mumini mai cikakken Imani. Inda ya ce

((إن التعبير القرآني دقيق في بنائه اللفظي ليدل دلالة دقيقة على مدلوله المعنوي. وفي العبارة هنا قصر بلفظ

«إنما» . وليس هنالك مبرر لتأويله- وفيه هذا الجزم الدقيق- ليقال: إن المقصود هو «الإيمان الكامل» ! فلو شاء الله- سبحانه- أن يقول هذا لقاله. إنما هو تعبير محدد دقيق الدلالة. إن هؤلاء الذين هذه صفاتهم وأعمالهم ومشاعرهم هم المؤمنون. فغيرهم ممن ليس له هذه الصفات بجملتها ليسوا بالمؤمنين. والتوكيد في آخر الآيات: «أُولئِكَ هُمُ الْمُؤْمِنُونَ حَقًّا» يقرر هذه الحقيقة. فغير المؤمنين «حقاً» لا يكونون مؤمنين أصلاً.. والتعبيرات القرآنية يفسر بعضها بعضاً. والله يقول: «فَماذا بَعْدَ الْحَقِّ إِلَّا الضَّلالُ» فما لم يكن حقاً فهو الضلال. وليس المقابل لوصف: «المؤمنون حقاً» هو المؤمنون إيماناً غير كامل! ولا يجوز أن يصبح التعبير القرآني الدقيق عرضة لمثل هذه التأويلات المميعة لكل تصور ولكل تعبير!)).

في ظلال القرآن (3/ 1474)

Sai Sayyid Qutub ya nuna cewa; Wannar Ayar ba magana take yi a kan cikakken Imani ba, kawai duk wanda ba shi da wadannan Siffofi na Muminai da Allah ya ambata a Ayar to kwata – kwata shi ba Mumini ba ne. Don haka duk wanda bai zamo Mumini "hakkan" ba to kwata – kwata shi ba Mumini ba ne. Don haka babu wani abu da yake Imani ba cikakke ba, wanda yake kishiyar Imani "hakkan".

Ka ga wannan shi yake fassara abin da ya fada cewa; Imani abu daya ne dunkulalle. Wato shi ne Imanin Muminai "hakkan". Kuma shi bai ma yarda a kira su da masu cikakken Imani ba, don shi a wajensa kwata-kwata babu wani Imani wanda ba cikakke ba.

To ka ga maganarsa ta saba Akidar Ahlus Sunna, tunda ba ta Mu'utazilawa ba ce to ta Khawarijawa ce.

(3) YANKAN MUSULMAI KAMAR YANKAN AHLUL KITABI NE, SABODA BA MUSULMAI BA NE

Akwai wani mutum mai suna Aliyu Ash'amawiy, wanda shi ne Kwamandan Rundunar Sirri ta Ikhwan na karshe, wanda ya ba da labarin irin mummunan tasirin da Fikrorin Sayyid Qutub suka yi wa matasan Ikhwan. A sakamakon tasirin irin karantarwan da Sayyid Qutub yake yi wa matasan har ya kai ga suna tunanin zartas da hukunce – hukuncen kafirtawan da yake yi wa Musulmai, har wata rana wani ya tambayi Aliy Ashmawiy a kan cin yankan wadannan Musulman, ga abin da ya ce

((جاءنى أحد الإخوان وقال لي: إنه سوف يرفض أكل ذبيحة المسلمين الموجودين حاليًا، فذهبت إلى الأستاذ سيد قطب وسألته عن ذلك فقال: دعهم يأكلوها، فليعتبروها ذبيحة "أهل كتاب"، فعلى الأقل المسلمون الآن هم "أهل كتاب")).

التاريخ السري لجماعة الإخوان المسلمين (ص: 172)

((Daya daga cikin 'yan'uwa ya zo ya ce min: shi zai bar cin yankan wadannan Musulman da suke nan a yanzu, sai na tafi wajen Sayyid Qutub na tambaye shi a kan haka sai ya ce: Barsu su ci, su dauki yankan nasu a matsayin yankan "Ahlul Kitabi", saboda mafi karancin halin Musulman yanzu su "Ahlul Kitabi" ne)).

To ka ga ya gina rashin cin yankan ne bisa cewa; su ba Musulmai ba ne.

(4) BA YA GANIN HALASCIN SALLAR JUMA'A

A wata ranar Juma'a Aliy Ashmawiy yana tare da Sayyid Qutub a gidansa, suna shirin karbo makamai da aka tura musu daga wata kasa, a wannar ranar ya tabbata masa cewa: Sayyid Qutub ba ya halartan Sallar Juma'a, saboda yanzu ba lokacinta ba ne, yanzu zamanin Jahiliyya ne, babu Khalifanci na Muslunci. Ashmawiy ya ce

((وجاء وقت صلاة الجمعة، فقلت له: دعنا نقم ونصلى، وكانت المفاجأة أن علمت ولأول مرة أنه لا يصلى الجمعة، وقال: إنه يرى فقهياً أن صلاة الجمعة تسقط إذا سقطت الخلافة، وأنه لا جمعة إلا بخلافة. وكان هذا الرأى غريباً علي، ولكني قبلته لأنه فيما أحسب أعلم مني)).

التاريخ السري لجماعة الإخوان المسلمين (ص: 209)

((Lokacin Sallar Juma'a ya yi, sai na ce masa: barmu mu tashi mu je Sallah, abin mamaki da ya faru shi ne a karo na farko kenan da na san ba ya yin Sallar Juma'a. Sai ya ce: "Shi yana ganin a Fiqhance, Sallar Juma'a ta fadi idan Khalifanci ya fadi, babu Sallar Juma'a idan babu Khalifanci".

To wannan ra'ayi ya yi mini banbarakwai, amma sai na karba a haka, saboda ina ganin ya fi ni ilimi)).

Wannan ya saba ma Akidar Ahlus Sunna.

Imamu Ahmad da Aliyu bnu al-Madiniy suka ce

((وصلاة الجمعة خلفه وخلف من ولى جائزة تامة ركعتين، من أعادهما فهو مبتدع، تارك للآثار، مخالف للسنة، ليس له من فضل الجمعة شيء إذا لم ير الصلاة خلف الأئمة من كانوا برهم وفاجرهم)).

شرح أصول اعتقاد أهل السنة والجماعة (1/ 181)

((Sallar Juma'a a bayan shugaba - nagari ne ko fajiri - da bayan Limamin da ya nada ta halasta, cikakkiya ce raka'a biyu. Duk wanda ya je gida ya sake to Dan Bidi'a ne, ya bar "athaar" ya saba ma Sunna, kuma ba shi da komai na falalar Juma'ar, matukar ba ya ganin halascin yin Sallah a bayan shugabanni, nagari suke ko fajirai)).

Ibnu Taimiyya a cikin "Wasidiyya" ya ce

((يأمرون بالمعروف وينهون عن المنكر على ما توجبه الشريعة. ويرون إقامة الحج والجهاد والجمع والأعياد مع الأمراء أبرارا كانوا أو فجارا)).

مجموع الفتاوى (3/ 158)

((Ahlus Sunna suna umurni da kyakkyawa suna hani a kan mummuna, bisa ka'idojin Shari'a. Kuma suna da Akidar gabatar da Aikin Hajji da Jihadi da Sallar Juma'a da Eidi tare da Sarakuna, nagari suke ko fajirai)).

A takaice, da wadannan misalai ya kara tabbata cewa; Sayyid Qutub Akidunsa na Khawarijawa ne.

✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments