DAGA FIQHUN IBNU TAIMIYYA
Za ka samu Shehin Darika fajiri makaryaci, mai karyar karamomi, amma sai a samu wasu kafirai sun zo masa, sai ya kira su ga Muslunci sai su Muslunta, su zama Sufaye, sai su zama sun fi alheri fiye da halin da suke a baya.
Kamar haka Malaman Ilmul Kalam, sukan iya cin
nasara a kan masu yakar Addini da irin nasu dalilai da hujjoji na Bidi'a, sai a
samu Imani ya kara karfi a zukatan Musulmai mabiya gaskiya, duk da cewa;
hujjojin nasu sun saba Qur'ani da Sunna, amma hakan ya fi alheri. Saboda shi
alheri da sharri matakai suke, sharri ne amma sai wasu mutane su amfana da shi,
sai su kasance mafi alheri fiye da yadda suke a baya.
Haka wasu Sarakunan azzalumai ne, masu sabo, amma
duk da haka ana samun alheri a tare da su, mutane da yawa suna amfana da
alheran da suka kawo, har a samu kafirai sun muslunta ta sanadinsu.
Haka a kan samu wasu su yi ta watsa raunanan
Hadisai na falalan aiyuka, kai, wasu kam ma Hadisan karya ne, amma sai wasu su
ji su amfana da su, rayuwarsu ta canza, su koma mutanen kirki fiye da yadda
suke a baya. A karshe sai ya ce
((والله تعالى بعث الرسل بتحصيل المصالح وتكميلها وتعطيل
المفاسد وتقليلها والنبي صلى الله عليه وسلم دعا الخلق بغاية الإمكان ونقل كل شخص
إلى خير مما كان عليه بحسب الإمكان {ولكل درجات مما عملوا وليوفيهم أعمالهم وهم لا
يظلمون})).
مجموع الفتاوى (13/ 95 - 97)
((Allah ya aiko Manzanni ne don su samar da gyara,
su cika ta, su lalata barna su karantar da ita, Annabi (saw) ya kira mutane ga
Addini da iyakar kokarinsa, ya cirata kowane mutum daga abin da yake kai zuwa
ga abin da ya fi alheri, gwargwadon iko…)).
To haka 'Yan Shi'a ma, za su iya shigar da kafirai
Muslunci, su zama Musulmai 'Yan Shi'a, sai hakan ya zama ya fi alheri fiye da
cigaba da zamansu cikin kafirci. Yake cewa
((وقد ذهب كثير من مبتدعة المسلمين: من الرافضة والجهمية
وغيرهم إلى بلاد الكفار فأسلم على يديه خلق كثير وانتفعوا بذلك وصاروا مسلمين
مبتدعين وهو خير من أن يكونوا كفارا)).
مجموع الفتاوى (13/ 96)
((Hakika da yawa cikin 'Yan Bidi'a Musulmai, cikin
Rafidha 'Yan Shi'a da 'Yan Jahamiyya da wasunsu, suna tafiya garuruwan kafirai,
har mutane da yawa daga cikinsu su muslunta, su amfana da hakan, sai su zama
Musulmai amma 'yan bidi'a, alhali hakan ya fi alheri fiye a kan su cigaba da
zama a kan kafirci)).
Kai, an yi masa Fatawa a kan mai fifita Yahudawa
da Nasara a kan Rafidha 'Yan Shi'a, sai ya ba da amsa kamar haka ya ce
((كل من كان مؤمنا بما جاء به محمد صلى الله عليه وسلم فهو
خير من كل من كفر به؛ وإن كان في المؤمن بذلك نوع من البدعة سواء كانت بدعة
الخوارج والشيعة والمرجئة والقدرية أو غيرهم؛ فإن اليهود والنصارى كفار كفرا
معلوما بالاضطرار من دين الإسلام. والمبتدع إذا كان يحسب أنه موافق للرسول صلى
الله عليه وسلم لا مخالف له لم يكن كافرا به؛ ولو قدر أنه يكفر فليس كفره مثل كفر
من كذب الرسول صلى الله عليه وسلم)).
مجموع الفتاوى (35/ 201)
((Duk wanda ya yi imani da abin da Annabi Muhammad
(saw) ya zo da shi ya fi alheri fiye da dukkan wanda ya kafirce wa Annabi
(saw), ko da kuwa shi wanda ya yi imani da shi din yana da wata bidi'a a tare
da shi, sawa'un Bidi'ar Khawarijawa ce, ko ta 'Yan Shi'a, ko ta Murji'ah, ko ta
Qadariyya da wasunsu. Saboda Yahudawa da Nasara kafirai ne kafirci sananne a
Addinin Muslunci. Amma Dan Bidi'a kuma idan ana zaton ya yarda da Annabi (saw)
bai mai saba masa a yarda da Muslunci ba, bai kasance kafiri da shi ba. Kai, ko
da an kaddara ya kafirta, to kafircinsa ba irin kafircin wanda ya karyata
Manzancin Annabi (saw) ba ne)).
Wannan shi yake nuna mana cewa; ashe ko da Bidi'ar
mutum ta kafirci ce to kafircin nasa ba irin na asalin kafirai ba ne. Haka kuma
su 'Yan Bidi'a za su iya yin aikin da alheri ne, kamar musluntar da kafirai su
zama Musulmai 'yan bidi'a.
Amma fa wannan ba ya hana cigaba da tsoratar da
mutane miyagun Akidun 'Yan Bidi'a, da kuma zarginsu, don su tuba su dawo kan
Sunna.
✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.