Ticker

6/recent/ticker-posts

Dalilin Da Ya Sa Mijin Ki Ba Ya Ba Ki Kulawa

TAMBAYA (220)

Don Allah ina son na san mene ne laifi na don na faɗa wa miji na cewar na bawa kishiyata kwanana la'akari da cewar yau za ta dawo daga wata tafiya da ta yi. Me ya sa ya rufe ni da zagi cewar abin da nake fada wai jahilci ne

AMSA

Da farko dai ina roqon Allaah ya baki ladan wannan manufar taki

Yayinda wasu suke fada da kishiya wasu kuma suke zuwa wajen boka don a mallake miji a cutar da kishiya amman ke anan kin duba maslaha ne la'akari da cewar idan kinawa kishiyar taki kwadayin wannan kwanan ne tunda za ta dawo ne daga tafiyar da tayi

Wannan tunani ne mai kyau in dai har an yi shi da kyakkyawar niyya kuma ba kowacce mace ba ce take da irin wannan tunanin ba. Sai ki godewa Allaah

Dangane da batun hukuncin yin hakan a shari'ah kuma, wannan ya halatta tunda daman haqqin ki ne kuma ki ka ga dacewar bada kwanan ga abokiyar zamanki ta yanda tana dawowa za ta amshe mijin ya koma dakinta

Maganar da ya fada cewar wannan jahilci ne, a'a ba jahilci bane ba domin kuwa Saudat Bint Zam'ah (Radiyallahu anha), daya daga cikin matan Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) a lokacin da ta ga ta tsufa kuma tana tsoron kada ya sallame ta sai tace masa: "Ya Rasulullah, na bawa Aisha gaba daya kwana na". Sai kuma Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya aminta da hakan

(Abu Dawood #2135 sannan kuma Shaikh Muhammad Nasiriddeen al - Albaany ya sahhaha hadisin a cikin Saheeh Abu Dawood)

Kinga anan bai fada mata bakar magana ba ballanta kuma ya zage ta saboda ai hakkin ta ne ba na Nana Aisha din ba

Don haka wannan kalubale ne ga maza akan yakamata su karanta yanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya gudanar da mu'amalar sa da iyalan sa

To amman kinsan dalilin da ya sa mijinnaki yake zagin ki da kuma rashin yaba miki ?

Abu daya ne !

Qareen !

Qareen shi ne Aljanin dake jikin sa. Wannan Aljanin shi ne yake son ya ga ya raba aurenku. Babban burin kafiran Aljanu, Shaidanu, Maridai, Ifritai da kuma oga kwata kwata wato Iblees shi ne a samu sakin aure tsakanin mata da miji

Kisa, caca, zina da sauransu duk Allaah yana iya yafewa bayinSa amman yin saki kuwa yana nufin an dakatar da yiwuwar samun bani Adama wadanda za su shiga Aljannah. Shi ne babban target din Iblees, a shiga wuta tare da shi saboda shi daman sunyi hannun riga da shiga Aljannah

An karbo daga Abdullahi Ibn Mas'ud (Radiyallahu anhu) ya ce: Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: "Kowanne dan Adam yana da Aljani (Qareen)"

Sai sahabbai suka ce: Ya Rasulullah, har kai ?

Sai ya ce: "Har ni, saidai ni Allaah ya taimake ni nawa ya musulunta kuma yana kwadaitar da ni ayyukan alkhairi ne"

(Sahihu Muslim #2814)

Musamman Imam an - Nawawy ya kulla babi mai suna: "Bab Tahrish al-Shaytan wa Ba’thihi Sarayahu li Fitnat il-Nas wa anna ma’a kulli insanin Qarin", bi ma'ana: "Babin sharrin Shaidan da kuma yanda yake tura rundunarsa don su halakar da yan Adam da kuma hujjar cewar kowa yana da Aljaninsa"

Akwai kuma hadisin Jabir Ibn Abdullahi (Radiyallahu anhu) wanda ya ce: Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: "Al'arshin Iblees tana saman ruwa. Yana tura rundunoninsa, wanda yafi kusanci dashi shi ne wanda ya zama silar raba aure"

(Sahihu Muslim 2813b)

Sannan kuma a ranar Lahira lokacin da za a jefa dan Adam cikin wuta sai ya zargi abokin hadin nasa wato Qareen kenan:

( قَالَ قَرِينُهُ رَبَّنَا مَا أَطْغَيْتُهُ وَلَٰكِن كَانَ فِي ضَلَالٍ بَعِيدٍ )

ق (27) Qaaf

Abõkin haɗinsa ya ce: "Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya kasance a cikin ɓata mai nĩsa."

( قَالَ لَا تَخْتَصِمُوا لَدَيَّ وَقَدْ قَدَّمْتُ إِلَيْكُم بِالْوَعِيدِ )

ق (28) Qaaf

Ya ce: "Kada ku yi husũma a wuriNa, hakika tuni na gabatar muku da gargadin azaba."

( مَا يُبَدَّلُ الْقَوْلُ لَدَيَّ وَمَا أَنَا بِظَلَّامٍ لِّلْعَبِيدِ )

ق (29) Qaaf

"Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zãlunci ba ga bãyiNa."

Ibn Khathir (Rahimahullah) ya ce: "Abdullahi Ibn Abbas, Qatadah, Mujahid da wasun su duk sun ce wannan Qareen din na nufin abokin hadi ko kuma Aljanin kowanne mutum"

To kinga anan idan mijin naki bai canza halin sa ba akwai yiwuwar Qareen dinsa zai nasara akansa, yanda za su shiga wuta tare. Allaah ya kiyaye. Musamman ma idan ya zamana ba ya adalci a tsakanin ke da ragowar matan sa. Ana gudun kada ranar lahira ya tashi da cutar barin jiki (Paralyze) kamar yanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya fada a cikin Sahihayn

Akwai hadisin Abdullahi Ibn Umar (Radiyallahu anhu) wanda ya ce: "Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: "Idan dayanku yana sallah ka da ya bari wani ya gifta masa, idan duk da haka mutum ya yi kokarin giftawa to ka yake shi domin kuwa yana tare da Qareen ne"

Imam ash - Shawkany (Rahimahullah) ya ce: "Kalmar Qareen, a cikin kamus din larabci na nufin abokin hadi, kuma abune sananne cewar ko da yaushe shaidan yana tare da dan Adam ne, duk inda zai je baya barin sa"

* (Nayl al-Awtar, 3/7)*

Muna rokon Allaah ya sa wannan sakon yaje kunnuwan mazaje musamman wadanda suke zagi da kuma rashin nuna kulawa ga matan su. Ku tuna cewar shaidan ne yake son raba ku la'akari da ai lokacin da kana neman auren ta tarairayarta kake harma ba ka son ka bata mata rai to don me kuma bayan shekara da shekaru da shafa fatihar Daurin auren ku kake son Qareen ya rusa niyyarka ta aure don kiyaye mutuncin kanka

Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ba irin wannan rayuwar ya yi da iyalansa ba. Wannan lamarin qalubale ne babba ga maza baki daya !

Zan so kowanne Namiji ya karanta littattafan nan guda 3 kacal. In dai ka ga rayuwar ka ba ta sauya ba to ba ka karanta su bane ba:

1) "Shama'ilil Muhammadiyya" na Abu Isah at - Tirmidhi

2) "How He Treated Them" by Shaikh Muhammad Saleh al - Munajjid

3) "Men Around The Messenger" by Khalid Muhammad Khalid

Wallaahu taala aalam

Masu buqatar shiga Telegram Class na littafin da muka fara: "KURA KURAI 100 A CIKIN SALLAR MU", ku shiga Telegram dinku kuyi searching:

USMANNOOR ACADEMY

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments