Ticker

6/recent/ticker-posts

Daukar Hoto Ya Zama Ruwan Dare Game Duniya

ƊAUKAR HOTO YA ZAMA RUWAN DARE GAME DUNIYA

Duk da cewa; Hadisai masu yawa sun zo da gargadi mai tsanani a kan yin hoto da rikansa da yin amfani da shi, da ajiyarsa, da tanadin azaba mai tsanani a kan masu yinsa, amma sai da aka samu tattaunawa a kan Hoton da ake dauka da Kemara (Na'ura).

Amma ni bayan nazarin maganganun masu halastawa tare da hujjojinsu, da kuma na masu haramtawa tare da hujjojinsu, sai na gamsu da NISANTAR DAUKAR HOTON GWARGWADON HALI. Saboda dalilai kamar haka

1- Karfin dalilai da hujjojin masu haramtawa.

2- Yana daga cikin Addini nisantar rikitattun lamura.

3- Fita daga tsakanin sabanin malamai abin so ne matuka.

Me ake nufi da lamba ta uku?

* Ma'ana, in wasu malamai sun ce; kaza Halal ne, wasu kuma sun ce; a'a, Haram ne.

To za ka fita daga tsakanin wannan sabani ne idan ka bar abin, saboda in ka aikata abin a matsayin cewa; halal ne, alhali kuma Haram ne, to ba ka dace da dadai ba. Amma kuma in ka bar abin, alhali kuma halal ne, to ba ka da wata matsala, saboda ba dole ne sai ka aikata abin da yake halal ba, balle ka zama mai laifi idan ba ka aikata shi ba.

Allahu A'alam.

✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments