Ticker

6/recent/ticker-posts

Game Da Matsalar Da Ta Shafi Dutsen Tanshi

GAME DA MATSALAR DA TA SHAFI DUTSEN TANSHI

Daga cikin manyan abin takaici a social media, a wannan zamani akwai yadda ake karon batta tsakanin Ahlus Sunna a junansu, musamman idan aka bar ilimi aka yi magana da jahilci, aka bar adalci sashe ya zalunci sashe, aka bar ladabin sabani aka koma jafa'i da rashin mutunci.

Wajibi ne a kowane hali ka zama mai da'a ma Allah.

Idan kuna da sabani da wani, sai ya saba ma Allah a kanka, ya zage ka, ya yi maka karya, ya zalunce ka, to kai kuma ka yi da'a ma Allah a kansa, ka yi hakuri, ka yi masa adalci, ka tausaya masa, ka yi masa nasiha. Saboda ba a rama sabon Allah da sabon Allah.

Idan ka yi masa haka sai ka zama mai riba a duniya da lahira.

Amma idan ka rama ta hanyar saba ma Allah, to ka zama daya da shi. Don mutum ya yi zina da 'yarka ba za ka ce kai ma sai ka rama, ka yi zina ta tasa 'yar ba. Sai dai ka rama ta hanyar da'a ma Allah.

To haka idan abokin sabaninka ya zalunce ka, to ka yi masa raddi na ilimi, ka tausaya masa, ka yi hakuri, ka yi masa nasiha, wannan sai ya fi muku amfani duka bangarori biyun.

Amma su mabiya da suke ta sharhi a Facebook, nasihata gare su, kowa ya ji tsoron Allah ya rubuta alheri ko ya yi shiru. Saboda duk abin da muke rubutawa za a yi mana hisabi a kansa.

Idan za ka yi magana ka yi magana ta ilimi da adalci tare da ladabi, ba magana ta jahilci da zalunci da izgilanci da cin mutunci ba. Annabi (saw) cewa ya yi

"وكونوا عباد الله إخوانا".

"Ku kasance bayin Allah 'yan'uwan juna".

Malaminmu al-Abbad ya ce

"رفقا أهل السنة بأهل السنة".

"Ahlus Sunna ku tausasa wa 'yan'uwanku Ahlus Sunna yayin sabani".

Don haka 'yan'uwana daliban ilimi, ku lazimci magana ta ilimi, da adalci da ladabi. Ku nisanci akasin haka. Saboda babu abin da yake haifar da fitina tsakanin Musulmi - musamman Ahlus Sunna - sai jahilci da zalunci. Babu magani kuwa sai ilimi da adalci da hakuri da tausasawa.

Allah ya kyauta.

✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments