Ticker

6/recent/ticker-posts

Game Da Salatul Gha'ib

Game Da "Salatul Gha'ib"

Daga cikin abubuwa da suke ba ni mamaki a mas'alolin ilimi akwai daukar zafi da tsananta wa abokin sabani a kan mas'alolin Ijtihadi. Mas'alolin Ijtihadi fa mas'aloli ne da wanda ya yi kuskure a cikinsu yana da lada daya. To yaushe za ka zo kana daukan zafi, kana zargin mutumin da lada yake da shi a dalilin mas'alar da ya saba maka a cikinta?!

Wannar mas'ala fa ta "Salatul Gha'ib" sabani a kanta ya kasance ne tun zamanin magabata. Shi ya sa za ka ji ana ambaton Limaman Mazhabobin Fiqhu a kanta; Abu Hanifa, Malik, Shafi'iy da Ahmad. Na baya-bayansu shi ne Ibnu Taimiyya.

To don Allah mas'alar da wadannan jagororin "Sunna" da "Salafiyya" suka yi sabani a kanta, miye dalilin da zai sa kai kuma a yau ka tsananta ma wanda ya saba maka?!

Hatta mas'alar hoto, Shaikh Ibnu Uthaimeen ya saba wa Shaikh Albaniy, a lokacin da Shaikh Ibnu Bazz yake tsakiya. Sun saba wa juna, saboda mas'ala ce ta Ijtihadi.

Saboda haka akwai takaici yadda wasu daga cikin Malamai suke mu'amalantar mas'alolin Ijtihadi kamar mas'alolin Nassi da Ijma'i, su zo suna tsanantawa a kansu.

Wannan yana faruwa ne bisa sababin rashin fahimta wa "Sunna" da "Salafiyya" da wasu suka yi, wanda har hakan ya haifar da watsi da ilimin Fiqhu, alhali Limaman Fiqhun suna cikin Limaman "Sunna" da "Salafiyya", wato "al-A'immatul Arba'ah".

Alhali a can Saudiyya tushen Wahabiyanci, kusan dukkan Malaman da muka gani, za ka samu kowannensu kwararre ne a fannoni guda biyu; Akida da Fiqhu, amma za ka iya samu wasu ba su yi zurfi sosai a sauran fannonin ba, amma ban da wadannan guda biyun. Amma mu a nan gida sai ka ji Ustazu, har bugan kirji yake yi yana cewa; shi ba ruwansa da Fiqhu! Shi kawai Sunna zalla, ko Salafiyya zalla. Alhali ya fi dacewa a kira shi da jahilci zalla!

Ala ayyi halin, galibin mas'alolin Fiqhu mas'aloli ne na Ijtihadi, sabani a cikinsu ba abin zargi ba ne, rahma ce ga bayin Allah, kamar yadda Umar bn Abdul'azeez (r) ya fada.

✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments