Hukuncin Kallon Tsiraici Ga Mai Karbar Haihuwa

HUKUNCIN KALLON TSIRAICI GA MAI KARƁAR HAIHUWA

TAMBAYA (250)

Aslm malam an tashi lpya, kallon tsiraici babu kyau,a musulunci, kuma haramcin ne, malam idan kuma aikin asibiti kake yi kuma kana (conducting labour) karban haifuwa fa🤔🙏

AMSA

Waalaikumus salam

Tabbas kallon tsiraici haramun ne idan ka dauke wanda ke tsakanin mata da miji sai kuma na larura kamar irin na karbar haihuwa din har bukatar hakan ta taso

Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: "Al'aurar namiji tana farawa ne daga cibiya zuwa gwiwa"

(Ahmad, Abu Dawud da Daruqutni)

Haka kuma gaba ki daya mace al'aura ce kuma ya zama dole ta rufe jikinta in dai tana gaban wadanda ba muharramanta ba saboda fadin Allaah Azzawajallah:

ۚ وَإِذَا سَأَلْتُمُوهُنَّ مَتَاعًا فَاسْأَلُوهُنَّ مِن وَرَاءِ حِجَابٍ ۚ

الأحزاب (53) Al-Ahzaab

Kuma idan zã ku tambaye su waɗansu kãyã, to, ku tambaye su daga bãyan shãmaki.

Da kuma hadisin: "Dukkan mace al'aura ce"

(Tirmidhi da isnadi sahihi)

Sai dai da fuskarta da kuma tafukan hannayenta wadannan biyun ba al'aura bane ba

Idan ya zamana babu wata larura ta rashin lafiya to haramun ne ganin al'aurar ta amman idan akwai larura kamar ta karban haihuwa wanda ba makawa sai an ga al'aurar ta to wannan ya zama larura saidai kuma duk da haka za a iya kalla ne kadai da manufar karbar haihuwar bawai wata mummunar manufa ba

Shi ya sa malamai suke bada shawara akan mata su dage da karatun bangaren lafiya ko don irin wannan matsalar wadda babu dadi ace namiji ne zai karbi haihuwar mace

Wallaahu taala aalam

Masu bukatar shiga Telegram Class na littafin "KURA KURAI 100 A CIKIN SALLAR MU", ku shiga Telegram kuyi searching:

USMANNOOR ACADEMY

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments