Ticker

6/recent/ticker-posts

Kallon Tiktok Da Azumi

TAMBAYA (221)

Assalam Alaikum malan Usmannoor Barka da Warhaka Ya ibada ? Ya halatta cikin watan Ramadan mutum ya shiga tik tok dan sauraron Wa'azi da malamai da ake dorawa

AMSA

Ya halatta amman da sharadin ba zai kalli abubuwan da Allaah ya haramta a kalla ba dogaro da ayar:

 ۚإِنَّ السَّمْعَ وَالْبَصَرَ وَالْفُؤَادَ كُلُّ أُولَٰئِكَ كَانَ عَنْهُ مَسْئُولًا

الإسراء (36) Al-Israa

Lalle ne jĩ da gani da zũciya, dukan waɗancan (mutum) yã kasance daga gare shi wanda ake tambaya.

Ka ga kenan idan mutum ya shagala da kallon abubuwan da ba za su amfane shi ba a Tiktok to ya shirya amsar da zai bawa Allaah a ranar Lahira akan ni'imar ido da aka yi masa

Sannan kuma anso idan mutum ya ci karo da karatu akan Allaah yace Annabi yace to a daure a yi sharing dinsa don wasu suma su gani suyi aiki da ilimin domin dacewa da ladan yada alkhairi

Kuma wannan yana daga cikin dalilan da ya sa bayan Ramadan in sha Allaahu zamu fara dora Video a Tiktok akan gyaran Sallaah. Burinmu shi ne mu zama silar da za a rage aikata barnar da ake a manhajar Tiktok. A maimakon asarar data wajen kallace kallacen da ba zasu amfanar da mutum a duniya da lahirar ba sai a maye gurbin hakan da kallon abin da zai amfane mu fiddunya wal akhira wato gyaran Sallah da sauran Ibadu. Za ku iya bibiyarmu a Tiktok ta hanyar searching:

USMANNOOR ACADEMY

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments