KU FAƊA WA PROF. MAQARI: DAULAR SAUDIYYA RANA TA SAMU...
A cikin wani karatunsa na littafin Muwadda Malik, tun da ya iso kan "Hadisul Jariya" - Hadisin da Annabi (saw) ya tambayi baiwa; "A ina Allah yake?" sai ta ce: "Yana sama" - Prof. hankalinsa ya tashi, ya shiga damuwa. Ya kore abin da Hadisin ya fada, ya ce: ai ko'ina ma sama ne. Saboda duniya a kewaye take kamar kwallo, don haka samanka kasan wani ne, a wancan bangare. Kamar yadda shi ma wancan mutumin da yake daya bangaren, samansa shi ne kasanka. Wannar tsohuwar shubuha ce ta irin su Raziy, kuma tun tuni Shaikhul Islam Ibnu Taimiyya ya markade ta, a cikin littafinsa: (كتاب العرش).
Kai, tun tuni Imam Abul Hassan al-Ash'ariy ya yi
raddi wa su Maqari, ya ce
"والسماء بإجماع الناس ليست الأرض".
الإبانة عن أصول الديانة (ص: 113)
"Bisa Ijma'in mutane gaba daya, kowa ya san
cewa sama ba kasa ba ce".
Haka kuma Prof. ya shigo da maganar saukowar
Allah, zuwa sama ta duniya, wanda muka yi masa raddi a kanta.
Kuma ya shigo da mas'alar "Tawili" da
"Tafwidhi", kawai ya yi ta cakuda takardu a cikinta ya wuce.
Daga karshe ya bayyana kullin da yake damunsa a
cikin zuciyarsa, wato shi ne bayyanar littatafan Malamai Ahlus Sunna mabiya
Salaf, da watsuwarsu cikin al'umma, da yaduwar Mazhabar Salaf, a tsakanin
al'umma - bayan sun dade suna boye littatafan da konawa -, har aka zo ana
bayyana munin Akidun bidi'a na Asha'ira da Maturidiyya.
Lallai idan ka saurare shi za ka fahimci irin
damuwar da take damunsa a cikin zuciyarsa, saboda Kasar Saudiyya ta yada
littatafan Ahlus Sunna Mabiya Salaf. Saboda yadda ya yi magana zafi-zafi, cikin
daga murya, da nuna takaici a fili.
To shi Maqari ya yi ta fada ne, yana zargin
Saudiyya ta saye injin din bincike na google (search engine), ta yadda da zaran
ka yi searching to littatafan Malaman Ahlus Sunna Mabiya Salaf ne za su
bayyana. Ko fatawa ka yi, to fatawowin Malaman Wahabiyawa ne za su fito maka.
Ya ce: sun yi amfani da kudin fetur, sun saye
komai na yada ilimi. Sun saye kamfanonin buga littatafai da yada su, sun hana
su buga na kowa sai na Malaman Wahabiyawa. Kuma ko an buga na wasu, kamar na
wasu Malaman Asha'ira, kamar "Fathul Bariy" na Ibnu Hajar, to a kasa, sai an cika
"Hashiyar" da ta'alikin Sahaikh Ibnu Baaz, ko waninsa, yana warware
Akidun Asha'ira da suke cikin littafin na "Fathul Bariy".
To haka dai Prof. ya yi ta magana, cikin zafafawa,
yana zargin Gomnatin Saudiyya, har da canza wasu littatafan.
To, amma shin Prof. bai sani ba ne, ko dai ya
manta ne?!
Ya manta abin dauloli masu ra'ayin bidi'a suka yi
wa Ahlus Sunna, na lalata littatafansu da salwantar da su?!
Littatafai nawa aka salwantar, har suka zama (في عداد المفقودات)?!
Sai kana karanta littatafan "Tarjaman"
Malamai, misali; sai ka ga an kirgo littatafan Malami wane, a ce yana da
littatafai kusan 20, amma ba a same su ba sai 2 ko 3, ko makamancin haka.
Aka boye littatafan Ahlus Sunna, har ya zama ba a
san ra'ayoyinsu na Akida ba. Shi ya sa a yau, idan ka dauki irin su (الفرق بين الفرق للبغدادي), (الملل والنحل للشهرستاني), da
sauransu, ba za ka ga an nakalto Akidar Malaman Ahlus Sunna Mabiya Salaf ba,
sai dai a kawo maka Akidar Asha'ira, sai a ce ita ce: Akidar Ahlus Sunna! Imam
Abul Hasan al-Ash'ariy ne kawai ya hakaito Akidar Salaf Ahlul Hadith a cikin
littafinsa (مقالات الإسلاميين).
Ka dawo baya, ka dauki daular "Mamalik",
ka binciki abin da aka yi wa Malaman Sunna da littatafansu. Musamman Shaikhul
Islam Ibnu Taimiyya, suka hana shi rubutu. Suka kona littatafansa, aka haramta
yada littatafansa. Idan an kama ka da littafin Ibnu Taimiyya to kamar an kama
dan kidnaping ne!
Ibnu Taimiyya yana daga cikin Malamai guda ukun da
suka fi kowa wallafa littatafai. Shi ya sa almajiransa - musamman Ibnul Qayyim
- har wallafa littatafai suke yi na sunayen littatafan Ibnu Taimiyya (أسماء مؤلفات ابن تيمية). Amma duk yawansu, wadannan
'yan kadan din da almajiransa saka boye ne suka iso gare mu.
Ka je ka karanta Tarihinsa, don ka ga yadda aka yi
ta haramta littatafansa, aka yi ta kona su.
Almajirin almajirinsa Ibnu Abil Izz, ya yi sharhin
"Akidar Dahawiyya", wanda ya cika littafin da maganganun Ibnu
Taimiyya da Ibnul Qayyim, amma tsabaragen yadda aka tsangwame su, bai ambaci
sunan Ibnu Taimiyya ba, ko sau daya a cikin littafin, saboda tsoron kar a kama
shi. Alhali ya dauko maganganun Ibnu Taimiyya adadi mai yawa sosai. Ya dauko
maganganu a wurare 187, kuma za ka iya cewa: rabi, ko fiye, daga Ibnu Taimiyya
ne. Sai Imam Ibnul Qayyim ne kawai ya ambaci sunansa sau 2, alhali kusan rabin
maganganun da ya dauko daga gare shi ne. 'Yan kadan ne sosai ya dauko daga
wasunsu, irin Ibnu Kasir, da wasunsa, ba su da yawa, ya dauko daga gare su sau
1, ko sau 2, ko makamancin haka.
Shi ya sa Ibnu Abdilhadiy ya ce
"لما حبس تفرق أتباعه، وتفرقت كتبه، وخوفوا أصحابه من أن
يظهروا كتبه، ذهب كل أحد بما عنده وأخفاه، ولم يظهروا كتبه، فبقي هذا يهرب بما
عنده، وهذا يبيعه، أو يهبه، وهذا يخفيه ويودعه، حتى إن منهم من تسرق كتبه، أو تجحد
فلا يستطيع أن يطلبها، ولا يقدر على تخليصها. فبدون هذا تتمزق الكتب والتصانيف.
ولولا أن الله تعالى لطف وأعان، ومن وأنعم، وجرت العادة في حفظ أعيان كتبه
وتصانيفه، لما أمكن لأحد أن يجمعها".
العقود الدرية من مناقب شيخ الإسلام أحمد بن تيمية (ص: 81 -
82)
Sai ya yi bayanin yadda aka musguna wa almajiran
Ibnu Taimiyya, a kan rikan littatafansa.
Haka Ibnu Hamid al-Shafi'iy, ya so ya hadu da Ibnu
Taimiyya, amma bayan aikin Hajji, sai ya kama hanya zuwa Dimashq don ya hadu da
shi, amma sai labarin rasuwarsa ta same shi. Sai ya rubuta wasika ya aika wa
almajiransa, yana rubutawa yana kuka, a ciki yake cewa
"ووالله ما كتبتها إلا وأدمعي تتساقط عند ذكره، أسفا على
فراقه وعدم ملاقاته. فإنا لله وإنا إليه راجعون، ولا حول ولا قوة إلا بالله العلي
العظيم...
لكن لما سبق الوعد الكريم منكم بانفاذ فهرست مصنفات الشيخ
رضي الله عنه، وتأخر ذلك عني، اعتقدت أن الإضراب عن ذلك نوع تقية، أو لعذر لا
يسعني السؤال عنه، فسكت عن الطلب، خشية أن يلحق أحدا ضرر - والعياذ بالله - بسببي،
لما كان قد اشتهر".
العقود الدرية من مناقب شيخ الإسلام أحمد بن تيمية (ص: 521)
Sai yake ba su uzuri, a kan alkawari da aka yi, na
rubuta "Fihirasa" na littatafansa, amma ya yi shiru, bai tambaya ba,
don tsoron kada a cutar da wani a dalilinsa.
Haka Ibnu Murriy ma ya yi kyakkyawan fata a kan
littatafan, ganin yadda ake musguna wa mutane a kansu, ya ce: Da iznin Allah,
Allah zai kawo wadanda za su bayyana littatafan nasa, inda ya ce
"ووالله إن شاء الله ليقيمن الله سبحانه لنصر هذا الكلام
ونشره وتدوينه وتفهمه، واستخراج مقاصده واستحسان عجائبه وغرائبه، رجالا هم إلى
الآن في أصلاب آبائهم. وهذه هي سنة الله الجارية في عباده وبلاده، والذي وقع من
هذه الأمور في الكون لا يحصي عدده غير الله تعالى".
الجامع لسيرة شيخ الإسلام ابن تيمية خلال سبعة قرون (ص:
156)
La'alla Allah ya amsa addu'ar tasa, kuma ya
daukaka Saudiyya da wannan babban aiki.
To haka Asha'ira suka yi ta musguna wa Ibnu
Taimiyya da mabiyansa, aka haramta littatafansa.
Kai, ko a wannan zamanin an yada jita-jitan
Gomnatin Misra ta haramta littatafan Ibnu Taimiyya, Ibnul Qayyim, da Ibnu
Abdulwahhab da sauran Wahabiyawa; su Ibnu Baaz, Ibnu Uthaimeen, kai da kusan
dukkan Malaman da suke kirgawa cikin Salafawa.
Haka na taba ganin wani rahoton Aljazeera, na
haramta wadannan littatafai a Iraq.
Saboda haka wannan abin da Prof. ya fada, na
zargin Saudiyya da mamaye bangaren buga littatafai da yada su, su ma Asha'iran
sun yi irinsa, ko fiye da haka, a zamaninsu. Ibnu Abdilhadiy ya ce: shi bai san
wanda ya kai Ibnu Taimiyya yawan littatafai ba, amma za ka iya cewa tara bisa
goma na littatafansa an rasa su. Ina suke? Kusan duka Asha'ira sun kona, sun
lalata su. Je ka karanta littafin da na ambata na Ibnul Qayyim, na sunayen
littatansa, da na Ibnu Rushayyiq.
Saboda haka, ita Saudiyya rana ta samu, dole ta yi
shanya!
Kuma koyi ta yi da daulolin Asha'ira da sauran
'yan bidi'a.
Don haka mu a wajenmu, abin da Saudiyya ta yi, na
yada ingantaccen Muslunci, da Akidar Salaf Ahlus Sunnati wal Jama'a, abin a
yaba mata ne. Allah ya saka musu da alheri, a kan wannan babban aiki, na hidima
wa ilimi da Addini da Sunna.
✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.