𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam barka da warhaka, fatan anyi sallah lafiya Allah ya karɓi ibadunmu ya maimaita mana da Imani da lafiya ameen. Malam burina shi ne Allah ya bani miji mai addini, mai nagarta, Wanda zai mutuntani ya mutunta iyayena, ya rikeni da amana ya bani duk wasu hakokina da Allah ya ɗora masa gwargwadon iko, idan Allah ya azurtamu da samun zuriya zai tayani gurin tarbiyyarsu ya basu ingantaccen ilmi, koda Allah ya karɓi rayuwata nasan a hannun da nabar yarana. Shiyasa na natsu ganin cewar na samu mai nagarta da tsoron Allah koda kuwa baikai 💯 ba, duk da kuwa al'amarin sai da taimakon Allah amman shi aure ba ayi masa gaggawa. Amman malam matsala itace mahaifyata tana matsamani saboda ta kosa na yi aure, tun Ina hakuri Ina jurewa malam har na fara gazawa saboda tana cikin damuwa da ɓacin rai akan banyi aure ba, na yi kokarin ganin ta fahimce ni amman abun ya gagara. An taɓa sanya bikina da wani bawan Allah bikin ya rage saura lokaci kaɗan Allah ya yi masa rasuwa shekara huɗu da Suka wuce tun daga lokacin har yanzu Malam taki tamun uzuri kullum fadanta na kawo miji na yi aure. Akan wannan matsalar yanzu haka Ina kano gidan yayana saboda ba na son Ina ganinta cikin damuwa a dalilina, kusan wata2 kenan kano amman kusan duk lokaci da zan kirata na gaisheta sai ta cemani nafiddo mijin aure, karshen wannan watan zan koma gida amman malam wallahi Ina fargabar komata gida batare da na cika mata burinta ba, bason na yi kuskuren zaben abokin rayuwata kuma uba ga yayana amman wlh malam yanzu a shirye nake na auri koma waye na sadaukar da farin cikina domin nasata ta yi farin ciki. Akwai wata shawara dana Yanke na rasa wazan fada mawa ya bani shawara akai, idan na fadama yan'uwana fada za su yi mani. Akwai wasu mutane anan garin kano da suke haɗa aure(mai dalilin aure) suna saka phone number nasu a symbol ɗin da suke kafewa bakin titi na yi tinanin nakirasu su haɗani da wani. Abun tambayar anan shine shin mutanen kirki nazuwa a irin wannan gurin su nemi matar aure?. Malam dan Allah a taimake ni da shawara meya dace nayi, na yi istihara akan haka (zuwa gurin can) amman still har yanzu ba na jin sarewa akan hakan sannan har yanzu ina kan yin addu'ar Allah ya kawo mani mijin aure nakwarai. Nagode Allah ya karama Malam tsoron Allah.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikis
Salaam: In Sha Allah, Allah zai Amsa Addu'o'in ki, Kuma daman yakamata ace
kowacce Mace a duniya abun da yakamata ta sawa Ranta kenan, na zaben Abokin
Rayuwar ta, domin shi zaman Aure ibada ne za a je ayi sa bawai na Yini 1 ba, ba
na wata 1 ba, ba shekara 1 ba, na har abada ake so Kuma a gurin ne ake son a
samu Al'umma nagari a dalilin wannan Auren naku, tunda hakane! kenan yakamata
ace Mace ta zabarwa kanta irin Mijin da idan ta same shi sai dai mutuwa kaɗai zai raba su amma
bawai matsala ko kuntatawa ko Zaluncin Namiji ba.
Sa'annan Ina
Iyaye da ke kanki Budurwa yakamata a gane cewa fa shi Aure da mutuwa gaba ɗayan su lokaci ne
wadda Allah yake kaddarawa Bawan sa bawai yin mutum bane, wannan Kaddarawa da
Allah yake yiwa Bayin sa na Aure ko inda Allah zai amsa rayuwar Bawa, toh tun
kina cikin Mahaifiyar ki kika rubuta cewa ga Mijin da za ki Aura a rayuwar ki,
sa'annan babu wani wadda ya isa ya kawar da wannan Rana da lokacin da Allah ya
rubuta miki shi tun kina cikin Mahaifar ki, Wannan kaddarar dole ne sai lokacin
Auren ki ya yi kamar yadda Allah ya rubuta miki shi kafin nan zakiyi Auren ki.
Amma wallahi
duk yadda kika Kai ga son ki yi Aure, duk yadda iyayen ki suka kai ga son su
Aurar da ke ki huta kawai, domin Hankalin su na tashi idan sun gan ki, toh
indai lokacin da Allah ya rubuta miki bai yi ba, sa'annan Mijin da Allah ya
rubuta miki cewa shi za ki fara Auren sa a rayuwar ki bai zo ba, toh ko Samari
10 zakiyi a rayuwar ki, ba za ki taɓa Auren su ba, dole ne sai wannan lokacin ya zo, sa'annan
wannan saurayin da Allah ya rubuta miki shi, Allah ya kawo miki shi kafin nan
zakiyi Aure. Amma indai lokaci Rana, Date da time din da Allah ya rubuta miki
shi Bai yi ba, toh duk duniya su taru su ce matsalar su shine kiyi Aure, toh ba
za ki taɓa yin sa ba sai dai
kawai ayi ta Ganin laifin ki a iska amma sai lokacin ki yayi.
Ga misalin
nan a ce ai daman Allah ya kaddara miki cewa Auren ki, zakiyi sa ne a ranar
1/5/2025 kuma ga shi ke ko saurayi ma ba ki da shi, toh In Sha Allah kafin
lokacin nan ya yi tunda hukuncin Allah ne ya rubuta miki tun kina cikin
Mahaifiyar ki, misali nake bayarwa, toh sai ki ga Allah zai yi iKon sa a take
sai ki ga saurayin ya zo, sa'annan yace Bikin kada ya wuce date kaza, Bikin ki
da shi sai ki ga wallahi ba za ki taɓa wuce wannan ranar da Allah ya rubuta miki kai ko second
1 ba za ki wuce ba balle ma ace wai an daga. Sabida haka komai lokaci ne idan
kin ga ba ki yi ba, toh lokacin ki ne bai yi ba, amma idan lokacin Auren ki ya
yi dole ne sai kin yi. Babu wata Mace da zata Balaga Budurwa tana ji da lafiya
a jikin ta tana ji da Sha'awa ace a Zuciyar ta ba ta son Yin Aure wallahi babu,
ko iyayen ta ba su fi ta son ta ga yau dai gata a cikin gidan Mijin ta ba, sai
dai idan Bata da lafiya tana fama da Matsalar Jinnu, toh wannan daban ne an San
cewa bata da lafiya ne, Amma Mace Budurwa lafiyar ki qlau kina ci kina sha kina
da Sha'awa a jikin ki, duk inda take dole ne ta so ace yau tana gidan Mijin ta,
fiye da yadda iyayen ta da suke son ta yi Auren.
Wancan wadda
ya kawo komai a kanki Allah ya dauki rayuwar sa, Allah ya Jikan sa da Rahamar
sa, Allah ne ya kaddara Daman ba zai aure ki ba, kuma tun can daman ba shi ne
Mijin ki da Allah ya kaddara miki cewa za ki Aura tun kina cikin Mahaifiyar ki
ba, don haka babu yadda za a yi ya Aure ki, Amma da ace Allah ya kaddara cewa
lallai shi ne zai Aure ki a rayuwar ki, toh sai ki ga ya Aure ki kina gidan sa,
amma Allah ya ɗauki rayuwar sa a tare da ke kina matsayin Matar sa, don
haka iyaye su gane cewa komai fa Allah ya riga ya gama kaddarawa Bawan sa, duk
abun Bawa zai yi a rayuwar sa gaba ɗayan sa, toh Allah ya gama Hukuntawa Bawan shi komai
kawai lokacin sa yake Jira, don haka ba abun gaggawa bane.
Wallahi akan
kiyiwa Yar ki gaggawa ta je ta yi Aure da sati 1 ta gane cewa ta yi Kuskuren
yin Auren a rayuwar ta, gara kin bar ta, shin kin San halin da Mata suke shiga
a kwanan nan kuwa? Yan Mata da aka Aure su kafin Azumin nan! kin San wanne Hali
suke ciki a gidan Mazãjen su kuwa? Wallahi wata Macen a yanzu da za ki
tambayeta Ta zaba abu 1, zaman gidan miji ko ta dawo gidan su? Wallahi sabida
irin yadda Mazãjen suke kuntatawa rayuwar su da Zaluncin wasu Mazãjen, an Aure
su ne ba tare da sanin Haqqin Aure ko dokokin Allah ba sai soyayya kawai a
waje, sai kin samu Mata Sama da 80% sun ce miki Gidan iyayen su suke son
komawa, dalilin shine irin yadda Mazãjen suke Gallazawa rayuwar su suke cutar
da su, tun Auren su da sati 2 suka gane lallai sun yi Kuskuren Auren wannan
Namijin, toh don Allah Yar ki ne za ki so ace kin Sha wahala a kanta, kun haɗa karya da gaskiya
an Aurar da ita amma an je ana cutar da rayuwar ta? Kin bawa wani Kato wadda
bai San Darajar ku ba, bai San Darajar Matar sa ba, ya je yana cutar da ita
yana zuluntar ta, za ki so hakan don Allah?
Iyaye da ke
kanki Budurwa, yakamata a sani cewa idan Allah ya jinkirtawa Bawan sa samun
wani abu musamman irin wannan son yin Aure, toh wannan jinkirin fa yana zama
Alkhairi ne ga Bawa sosai bawai Sharri ba, bawai ki ce ai Allah ya manta da ke
ne ya sa kika gara samun Miji har gobe ba, a'a Alkhairi ne jinkirin Auren ki,
kuma ke kanki idan za kiyi tunani cewa a yanzu wata kila akwai qawayen ki da
suka yi Aure, wasu zata iya yiyuwa akwai waɗanda aka sake su
Auren ya mutu, Kuma da yin Auren su ko shekara 2 me kyau ba su yi ba, wasu ko
wata 6 ba'a yi a gidan Miji ba an fara samun matsala har an yi saki 2, wasu
kuma inda a ce za ki bincika yaya suke ji a gidan Mazãjen su? Wallahi daidaiku
ne za ki sun ce miki suna Jin daɗin zaman gidan Mijin su, amma da za ki tambaye su da yin
Auren su da rashin yin sa wanne yafi? Za su ce gara ma ba su yi ba, ko Kuma Ina
ma a Sake su su dawo gidan iyayen su yafi musu zaman gidan miji, wata fa tun da
ta yi Aure wallahi ba ta san menene daɗin Aure ko Yaya soyayya yake tsakanin Miji da mata ba,
Kuma Auren soyayya suka yi? Toh ki gaya min irin wannan Auren idan an yi
gaggawar yin sa, shin ya halin Mace zai zama don Allah? Iyaye a ji tsoron
Allah, kema Budurwa ki bi a hankali don Allah. Halin Mazajen yanzu wasu wallahi
duk tunanin ki sun wuce nan.
Toh kin ga
irin wannan in Allah ya jinkirta miki ba ki samu Mijin Aure da wuri ba indai
normal kike bawai Jinnu ne da ke ba, kawai abun da zakiyi ma Allah, shi ne ki
gode ma Allah akan wannan, sa'annan ki Kara da yin Addu'oi sosai ba dare ba
rana, bawai ki Rika tunani har ki tuno abun da zai sa ki Saɓawa Allah ba, bawai
iyaye ku Rika takurawa Yaran ku don me suka qi yin Aure Kun gaji da ganin su
Kuskure ne wannan, kawai ki ci gaba da yin Addu'a kina yiwa Allah godiya akan
wannan jinkirin da ya miki na rashin yin Auren ki a lokacin da kike so, idan kina
haka sai ki ga Allah ya ji kukan ki, ya tura miki da Miji irin wadda kike so a
rayuwar ki, kin yi Auren ki ba tare da an samu matsala ko da ace nan gaba ne.
Idan zakiyi
tunani ma ai ko a inda kike ko a Anguwar ku, ai akwai waɗanda suka fi ki da
komai na kyan Halitta ne, a shekaru da komai duk sun fi ki, amma har gobe wata
ma ko saurayi ba ta taɓa yin sa ba a rayuwar ta, su kuma su ce me? Sabida haka
ke kawai kiyiwa Allah godiya da kina samun waɗanda za su zo su ce
suna son ki, kawai lokacin Auren ne bai yi ba, sai ki gode ma Allah ba tare da
kin tuna komai a ranki ba, iyayen ki ma a maimakon fushi da suke yi da ke, da
Kara matsa miki da takurawa rayuwar ki, ai da Addu'a yakamata ace sun dage da
Yi miki bawai kullum ace ki fito da Miji ba, Auren da ake yi a yanzu wallahi
wahalar da wasu Matan suke Sha a gidan Miji idan kin ji abun bakin Ciki ne abun
takaici sai kin kwana bakiyi Bacci ba wallahi, da za ki bincika cikin su a
yanzu! za su ce Miki da ba suyi Auren ba, kin ga kenan yi da wurin ma wani
lokacin matsala ne babba ga rayuwar Mace karama a yanzu.
Sa'annan
yanzu kamar ke misalin an Aure ki an tafi da ke shekaran ki 1 tak a gidan Miji,
ko wata 6 a gidan Miji, wata kila kin Haihu ko kuma kina da Ciki sai Mijin ya
fara daga miki Hankalin ki, karshe ma wata kila yace ki je ya sake ki Ki tafi
gidan ku, don Allah yaya za ki ji a rayuwar ki kina karamar Yarinya? iyaye ya
za ku ji a ranku idan an Sako ta Ta dawo gaban ku a wata 1 ko shekara 1?
Misalin a ce kin yi Auren ne da wuri sai Hakan ya faru da ke, yanzu kin dawo
gidan ku ga Ciki ko Yaro a hannun ki, ya za ki ji a ranki toh? Za ki ce gara da
kika yi Auren ne domin kin haihu? ko kuma kina da Ciki kin San menene Aure, kin
San menene Jima'i yanzu kin more, ko kuma me za ki ji a rayuwar ki? Sa'annan da
aka sake ki a yanzu kin San zaman watanni nawa ko shekara nawa zakiyi kafin
wani Namijin ya zo yace Yana son ki da Aure? Ah yanzu ma kina Budurwa ga shi
kina korafin cewa kina cikin damuwa babu ma nemi iyaye sun saka ki a gaba, toh
Ina ga Kuma kin yi Auren ya sake ki ga Ciki ko Yaro a hannun ki, Nan Kuma wanne
irin damuwa za ki shiga? Sabida haka duk abun da zakiyi a rayuwar ki, toh ki
Rika tuna abu me kyau a Zuciyar ki, haka iyayen Yara ku Rika tuna alkhairi ga
Yaran ku Mata domin kuna cutar da su sosai wallahi, idan Allah ya hana ki abu,
toh godiya yakamata kiyi masa, sa'annan ki ji daɗin haka a ranki,
kina Farin ciki sai ki ga cewa Allah ya ba ki fiye da wannan da kika rasa a
rayuwar ki kin samu Mafi Alkhairi gare ki. Amma idan za ki Rika yin irin wannan
tunanin, iyaye za su rika yin irin wannan tunanin, toh fa Allah Yana iya
jarrabawa rayuwar ku, ki samu Namijin amma kuma wallahi za ki dawo kina nadamar
Auren sa a lokacin da Hakan ba zai amfane ki ba.
Sa'annan
Mace Budurwa ko Bazaura ba ki isa ki ɗauki Kanki, ki Aurar da kanki ba, dole ne sai Namiji ya
zo ya neme ki da Aure tukuna, Dan gara ma da a ce kina da dukiya ne kin ga kina
iya amfani da Kuɗin ki gurin yin Aure, sai ki biyawa Namiji komai ya Aure
ki, toh amma yin Hakan ma Kuskure ne domin ba za ki taɓa Jin daɗin zama da shi ba.
Kin ga kenan, yakamata ki bi komai a hankali kar kiyi gaggawa, shi Aure ba'a yi
masa gaggawa idan ma kin yi, toh za ki dawo kina Allah Wa dai da hakan idan
kina karatu a group ai kina ganin korafin wasu mãtan auren da Mazajen su kin ga
kenan da a ce daɗi suke ji da bahaka ba.
Baya ga
hakan kada ki yarda kiyi Kuskuren ɗaukar numbern wani Namiji akan Layi wai da sunan ya zo ya
Aure ki ke a shirye kike da yin Aure ko ta wanne hali ne, domin ai ga abun da
Mahaifiyar ki ta ke miki, toh su Mazan yanzu sun nema Mace da kansu, sun kashe
kuɗi da kansu, sun yi
soyayya da nuna kulawar su ga Mace a waje har zuwa Auren ta yaya ake karewa
idan zama ya yi zama a gidan Miji? Ki tambayi irin Auren da ake haɗawa a Kano ki ji
yaya Auren yake zama, balle ace kene da kanki za ki kira Namiji ki ce kina son
sa da Aure, ke ya Aure ki a shirye kike ya Aure ki, ko kuma ki ce a haɗa ki da mijin Aure,
wallahi kina iya rashin Sa'a ki samu Mijin da tun Daren farko ki fara neman
hanya, Yaya za a yi Auren ya mutu ki rabu da shi? Kuma ai kin ce kin yi
Istihara har yanzu ba ki abun hakan ya kwanta miki ba kin ga kenan sai ki
hakura da yin hakan.
Kuma ki lura
dakyau irin wannan Auren ana cutar da rayuwar Mace sosai, gorin duniyar nan zai
kare a kanki, Iyayen ki ba su ci ba, ba su Sha ba shi wadda ya Aure ki idan ya
tashi Zagin ki kab sai ya haɗa su har da dangin ki domin kin Zubar da Mutuncin ki ne
kin ce ya Aure ki Kuma ya Aure ki, duk wadda aka ce miki bai wahala ba a gurin
neman Mace, haka kawai ya samu Matar a iska, toh daker ne zai ga Darajar ki,
daker ne zai ga Mutuncin ki, daker ne zai ga Qimar ki, daker ne zai ga Martaban
ki, daker ne zai iya sauke Haqqoqin ki da Allah ya ɗaura masa a kansa
zai Zalunce ki ya cutar da ke ya kuntatawa rayuwar ki shi a gurin sa bai miki
komai ba Kene ma yake Jira ki ce ya yi hakuri, domin kullum gani zai yi ai kene
kika nema da ya Aure ki, domin kin gagara samun Mijin Aure, shi Taimakon ki
yayi, don haka daker ne za ki samu kulawa da irin soyayyar da kike so Namiji ya
miki a rayuwar ki, domin kene kika kawo kanki kika ce a Aure ki toh ya Aure ki
sai tashin hankali daban-daban.
Amma idan
Namiji ya wahala a soyayya, ya Sha fama sosai a gafen neman ki kafin nan ya
samu kika zama Matar sa, ya kashe kuɗin sa sosai a kanki kafin kika zama Matar sa, toh dole ne
ya San Darajar ki da duk abun da na lissafa miki, idan kuma ya San Darajar ki
da duk abun da na lissafa miki, toh Wallahi ba zai taɓa yarda ya cutar da
ke ba, ko ya zulunce ki, ke kullum kina cikin kunci da kuka da Bakin Cikin
rayuwa da shi ba za ki taɓa Jin haka ba. Babu laifi Mace ta cewa Namiji tana son sa
da Aure amma wannan sai kin tabbatar da cewa me tsoron Allah ne, me Addini ne,
me riko da gaskiya da Amana ne, me son ibadar Allah ne sosai kin san shi farin
sani sosai kullum kina kallon sa ko kina Jin motsin sa, nan ne sai kiyiwa kanki
kwaɗayin ya Aure ki,
sai ki gaya masa cewa kina son sa don Allah ya Aure ki.
Amma irin
wannan na haɗin da ake yi, ko kira numbern wani don a haɗa ku, toh kina iya
dawowa kiyi nadamar Auren sa, ki gwammaci gara kin mutu da irin wannan rayuwar
Auren, kin gwammaci gara kin zauna a Hakan akan ki Aure shi, don haka kada kiyi
wannan Kuskuren, ita Mahaifiyar ki zan Karɓi numbern ta na
fahimtar da ita, idan ta ji shikenan idan ba ta ji ba, toh sai mu ce Allah ya
tsare ya shirya amma dai za a yi Abin da Bai dace ba.
Irin hakan
ne yake jefa Yan Mata sosai zuwa ga Halaka, yakamata iyaye Mata da Maza ku ji
tsoron Allah wallahi, ke kanki ba'a miki haka ba, sabida haka Bai kamata ki
takurawa Yar ki, ki ce dole-dole sai ta fitar da Mijin Aure ba, a halin da ta
ke Ciki Yanzu na halin wasu Mazan kin ga kina iya jefe rayuwar ta Cikin halaka
sosai, ta je ta aikata abun da bai dace ba, ku dawo gaba ɗayan ku kuna
takaicin wannan, don haka maganin bari ko yin da na sani a rayuwa, toh kada a
fara yin sa kawai, don Allah Iyaye a kiyaye, fatan kin gane ko????
WALLAHU
A'ALAM
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.