Ticker

6/recent/ticker-posts

Manyan Malamai Ne Suka Tabbatar Da Sunan Kungiyar Salafiyyun

MANYAN MALAMAI NE SUKA TABBATAR DA SUNAN "ƘUNGIYAR SALAFIYYUN"

Ba mu muka kar zomon ba, rataya aka ba mu...

Don haka bai kamata a zarge mu ba, alhali mu kawai nakaltowa muka yi daga Manyan Malaman wannan zamani, kuma muka bi su a kan haka. Saboda mun gani a waki'i a zahiri; lallai an samu bullar wata Kungiya a tsakanin Ahlus Sunna, wacce take guluwwi da ta'assubanci ga Shaikh Rabee'i Al-Madkhaliy.

Ga jerin Malaman da maganganunsu kamar haka:

1- Shaikh Abdul'Azeez Ibnu Baaz (ra) ya ce:

أما الجماعات الأخرى فلا تتبع منها أحدا إلا فيما وافقت فيه الحق. سواء كانت جماعة الإخوان المسلمين أو جماعة التبليغ أو أنصار السنة أو من يقولون: إنهم السلفيون أو الجماعة الإسلامية أو من تسمي نفسها بجماعة أهل الحديث وأي فرقة تسمي نفسها بأي شيء فإنهم يطاعون ويتبعون في الحق

مجموع فتاوى ابن باز (7/ 120 - 122)

"Amma wasu kungiyoyin daban kar abi ko daya daga cikinsu sai dai a abin da ta dace da gaskiya a cikinsa, sawa'un KUNGIYAR IKHWANUL MUSLIMUNA CE, ko Kungiyar Tabligh, ko Ansarus Sunna, KO WADANDA SUKE CEWA: SU NE 'YAN SALAFIYYA, ko Al- Jama'atul Islamiyya, ko wacce take kiran kanta da Jama'atu Ahlil Hadith, da kowace kungiya da take kiran kanta da kowane suna, kawai ana yi musu da'a da biyayya ne a kan gaskiya".

Abin lura; bayan ya ambaci Jama'ar da take kan Siradul Mustaqeem, sai kuma ya ambaci wasu ya kira su da (الجماعات الأخرى) "wasu kungiyoyin daban", a cikinsu sai ya ambaci wadanda suke kiran kansu da sunan "Salafiyyun". inda ya ce: (أو من يقولون: إنهم السلفيون).

Don haka a nan Kungiyar Salafiyyun ta tabbata.

2- Shaikh Ibnu Uthaimeen (ra), shi kam ya fi kowa tona asirin Kungiyar ta Salafiyyun. Daga ciki ya ce:

إنه إذا كثرت الأحزاب في الأمة فلا تنتم إلى حزب، فقد ظهرت طوائف من قديم الزمان مثل الخوارج والمعتزلة والجهمية والرافضة، ثم ظهرت أخيرا إخوانيون وسلفيون وتبليغيون وما أشبه ذلك، فكل هذه الفرق اجعلها على اليسار وعليك بالأمام...

ولا شك أن الواجب على جميع المسلمين أن يكون مذهبهم مذهب السلف لا الانتماء إلى حزب معين يسمى السلفيين، والواجب أن تكون الأمة الاسلامية مذهبها مذهب السلف الصالح لا التحزب إلى من يسمى (السلفيون) فهناك طريق السلف وهناك حزب يسمى (السلفيون) والمطلوب اتباع السلف، إلا أن الإخوة السلفيين هم أقرب الفرق إلى الصواب ولكن مشكلتهم كغيرهم أن بعض هذه الفرق يضلل بعضا ويبدعه ويفسقه،

شرح الأربعين النووية للعثيمين (ص: 282 - 283)

"Lallai idan kungiyoyi suka yawaita a cikin al'umma, to kar ka dangantu ga wata kungiya. Hakika a zamanin da ya gabata kungiyoyi sun bayyana, irin Khawarijawa da Mu'utazila da Jahamiyya da Rafidha 'Yan Shi'a, daga karshe kuma 'Yan Ikhawan da 'Yan Salafiyyun da 'Yan Tablig da abin da ya yi kama da haka sun bayyana, duka wadannan kungiyoyin ka sanya su a hagunka, ka kama gaba...

Babu shakka lallai abin da yake wajibi a kan dukkan Musulmai shi ne Mazhabar Salaf ta zama ita ce Mazhabarsu, ba dangantuwa zuwa ga KUNGIYA da ake kira "SALAFIYYUN" ba, abin da yake wajibi shi ne; Mazhabar Al'ummar Musulmi ta zama Mazhabar Magabata na kwarai, ba yin kungiyanci ga wadanda ake kira "SALAFIYYUN" ba. AKWAI HANYAR SALAF DABAN, AKWAI KUMA KUNGIYA DA AKE KIRA "SALAFIYYUN" DABAN, abin da ake bukata kawai shi ne bin tafarkin Salaf. SAI DAI KUMA SU 'YAN UWA 'YAN SALAFIYYA SU NE SUKA FI KUSA DA DADAI A KAN SAURAN KUNGIYOYIN, sai dai mushkilarsu kamar ta sauran ce, cewa; sashe daga cikin wadannan kungiyoyi yana yin hukuncin bata ga wani sashen, yana bidi'anar da shi, ya fasikantar da shi".

Kuma ya ce:

وأما اتخاذ السلفية كمنهج خاص ينفرد به الإنسان ويضلل من خالفه من المسلمين ولو كانوا على حق، واتخاذ السلفية كمنهج حزبي فلا شك أن هذا خلاف السلفية،

لقاء الباب المفتوح (57/ 15، بترقيم الشاملة آليا)

"Amma rikan Salafiyya a matsayin wani Manhaji na daban, wanda wani mutum yake kadaituwa da shi (kamar a sanya bin wani Malami a matsayin shi ne Salafiyya), yana bidi'antar da wanda ya saba masa daga cikin Musulmai ko da sun kasance a kan gaskiya, da rikan Salafiyya a matsayin Manhaji na Kungiyanci, ko shakka babu wannan sabanin Salafiyya (ta gaskiya) ce".

Bayanan Shaikh Ibnu Uthaimeen a fili suke ba sa bukatar ta'aliki.

3- Shaikh AbdulMuhsin Al-Abbad Al-Badar ya ce:

ومما يؤسف له أنه حصل أخيراً زيادة الطين بلة بتوجيه السهام لبعض أهل السنة تجريحاً وتبديعاً وما تبع ذلك من تهاجر، فتتكرر الأسئلة: ما رأيك في فلان بدَّعه فلان؟ وهل أقرأ الكتاب الفلاني لفلان الذي بدَّعة فلان؟ ويقول بعض صغار الطلبة لأمثالهم: ما موقفك من فلان الذي بدَّعه فلان؟ ولابد أن يكون لك موقف منه وإلا تركناك!!!...

وهذا المنهج شبيه بطريقة الإخوان المسلمين...

ومرة أخرى رفقا أهل السنة بأهل السنة

"Yana daga cikin abin takaici, a karshen nan an samu karuwar abin da yake kara munana lamarin, ta hanyar sa wasu Ahlus Sunna a gaba, ana jarraha su da bidi'antarwa, da abin da yake biyo bayan hakan na kaurace musu. Sai suke yawan maimaita tambayoyi kamar haka: menene ra'ayinka a kan wane, wanda wane ya bidi'antar da shi?

Shin zan karanta littafi kaza na wane, wanda wane ya bidi'antar da shi?

Wasu daga cikin kananan dalibai suna fada ma abokansu: Menene matsayarka a game da wane, wanda wane ya bidi'antar da shi?

Dole ya kasance kana da matsaya a kansa, in ba haka ba kuma za mu ajiye ka a gefe!...

WANNAN MANHAJI YA YI KAMA DA MANHAJIN IKHWANUL MUSLIMUN...".

Abin lura a nan shi ne; Shaikh ya kamanta Manhajin Kungiyar Salafiyyun da na Ikhwan ne, saboda sun yi tarayya a cikin Kungiyanci da Ta'assubanci ga shugabanninsu.

4- Shaikh Rabee'i Al-Madkhaliy shi da kansa ya sallama Salafiyyun Kungiya ne inda ya ce:

هناك حزب الله ويفخر المؤمن بأنه حزبي حزبيته لله, الآن يقولون: السلفيون متحزبون, نعم, متحزبون - والله - متحزبون للحق لكتاب الله وسنة الرسول، وهذا شرف عظيم لمن يتحزب لله ولرسوله ولدينه الحق...

مجموع كتب الشيخ ربيع المدخلي (474/14)

"Akwai Kungiyar Allah, kuma Mumini yana alfahari da cewa; shi Dan Kungiya ne, kungiyancinsa ga Allah ne. Yanzu suna cewa; SALAFIYYUN 'YAN KUNGIYA NE, NA'AM, WALLAHI 'YAN KUNGIYA NE, suna kungiyanci ga gaskiya, ga Littafin Allah da Sunnar Manzonsa da Addininsa na gaskiya…".

To ga nan Shaikh Rabee'i da kansa ya yarda masu kiran kansu da sunan Salafiyyun Kungiya ne, saboda babu wanda ya isa ya yi inkarin waki'i da hakika sai mai "safsad'a".

Saboda haka, jama'a ku lura da siffofin Kungiyar Salafiyyun da Shaikh Ibnu Uthaimeen ya ambata a cikin maganganunsa, da kuma wadanda Shaikh Abbad ya ambata, sai ku duba ku ga Siffofin da wadanne Salafawa suka dace?

Kuma kowa ya ga yadda wadannan Malamai ukun farko da suka gabata suke jera Kungiyar Salafiyyun din kafada da kafada da Kungiyar Ikhwan, saboda kowa ya san babu kungiyar da ta kafa kanta a matsayin kishiya mai yakar Kungiyar Ikhwan kawai sai wadannan Salafawan masu kirkirarren Manhajin Jarhi da Ta'adili. Wannan ya sa suke yin jarabawa wa mutane don gane Dan Kungiyarsu ta hanyar tambayar mutum a kan Shaikh Rabee'i da kuma Sayyid Qutub. Wanda har ya kai ga suke daukar Kungiyar Ikhwan a matsayin kungiya mafi hatsari ga Muslunci, kuma suke daukar 'Yan Ikhwan din a matsayin mafi sharri fiye da Yahudu da Nasara, kamar yadda Shaikh Rabee'i yake cewa:

ﻓﺎﻹﺧﻮﺍﻥ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻮﻥ ﺃﺧﻄﺮ ﺍﻟﻔِﺮﻕ ﻋﻠﻰ ﺍﻹﺳﻼﻡ...

ﺍﻹﺧﻮﺍﻥ ﻳﻠﺒﺴﻮﻥ ﻟﺒﺎﺱ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﻭﻫﻢ ﺃﺷﺪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺴﻠﻔﻴﻴﻦ ﻣﻦ ﺍﻟﻴﻬﻮﺩ ﻭﺍﻟﻨﺼﺎﺭﻯ...

Alhali sauran kungiyoyi wadanda suke dangantuwa ga Salafiyya babu wanda yake daukar Kungiyar Ikhwan bisa irin wannan matsayi na kamanta su da kafirai ko ma fifita su a kansu sai su wadannan Kungiyar Salafiyyun din.

Don haka abu ne a zahiri, waki'i ya tabbatar da wannan Kungiyanci, babu mai inkarin waki'i kuwa sai wawa (سفسطي) mai rena wa mutane hankali, yana musun hakika.

Saboda haka, ko su yarda, ko kar su yarda, sunansu na yanka kenan; 'Yan Kungiyar Salafiyyun, kuma manyan Malaman wannan zamani ne suka rada musu wannan sunan, aka yanka ragon suna. Kuma in an yanka ba ta tashi.

✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani

       28 January, 2018

Salafiyya

Post a Comment

0 Comments