Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene Ne Maganin Tsoro?

TAMBAYA (213)

Malam Dan Allah a taimaka min da addu'a Wadda zan yi da dare ya yi tsoro ke taso min wlh

AMSA

Tsoro Halitta ce kowa yanada

Amman ko kinsan da cewar ana iya sarrafa tsoro ?

Kuma ba wahala. Kenan abin sa Kai ne kawai

Tsoro da Larabci shi ake Kira da Khauf Kuma ya rarrabu gida 3:

1) Haram (Haramun)

2) Mubah (Ba dole ba) da kuma

3) Wajib (Dole)

Inda zai zama Haramun shine tsoron da zai kai ka ga fidda tsammani daga Rahamar Allaah ko Kuma tsoron Aljani zai iya cutar dakai

Inda Kuma zai zama Mubah bi ma'ana ba dole ba shine: Aure, Tafiya, Kwanciya bacci, Cin abincin halal, saka tufa ta halal da sauransu

Sai Kuma Wajib wato abinda ya zama dole. Shi ma Kuma ya rarrabu gida 2 ne: Fard al-ayn (kamar: Sallah, Azumi, Zakkah) da Kuma Fard al-kifayah (kamar: binne mamaci) akwai Kuma Wajib 'ayn (Kamar Neman ilimi dogaro da hujjar Aya ta farko da aka fara saukarwa a Qur'ani) da Kuma Wajib kifaya (Kamar gina masallachi)

Akwai Kuma tsoron na Dabi'a Shima ya halatta kamar tsoron Mutuwa, Wuta, Maqiyi, Zaki ko Maciji (Kamar yanda Annabi Isah Alaihis Salam yaji tsoron sanda lokacinnan da ta zama Macijiya)

Matakin farko na rabuwa da tsoro shine jin tsoron Allaah a matsayin Sa na Mahalicci

Domin kuwa yawan aikata Zunubbai na fili da Kuma musamman na boye (daga Kai sai Allaah) yana da alaqa da rashin jin tsoron Allaah Al-Jabbaru yayinda Kuma ya zamana mutum ba zai ji tsoron al-Khaliqu ba to sai Mai halittar ya hadashi da tsoron Makhluqai (wato ababen halitta) wannan dalilin ne ya sa kike yawan jin tsoron

Mafita anan shine ki ji tsoron Allaah shi kadai sai ya cire Miki tsoron halittunSa

Ki yawaita karanta Suratu ad-Dhuha domin kuwa dalilan saukar ta (asbabun nuzul) yanada alaqa da damuwa da Ma'aiki Sallallahu alaihi wasallam ya shiga sakamakon tsagaita yi masa wahayi. Shiyasa Allaah Azzawajallah ya ce:

( مَا وَدَّعَكَ رَبُّكَ وَمَا قَلَىٰ )

الضحى (3) Ad-Dhuhaa

Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.

Sai kuma ki tuno da addu'ar da Annabi Sallallahu alaihi wasallam yake yawaita karantawa akan tsoro

اَللّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْهَمِّ وَالْحُزْنِ، والْعَجْزِ والكَسَلِ والبُخْلِ والْجُبْنِ، وضَلْعِ الدَّيْنِ وغَلَبَةِ الرِّجَالِ.

Allahumma innee a'oothu bika minal-hammi walhuzn, wal'ajzi walkasali walbukhli waljubn, wadal'id-dayni waghalabatir-rijal.

Ya Allah! Ina neman tsarinka daga damuwa; da bakin ciki, da gajiyawa, da lalaci, da rowa, da rinjayen mazaje.

Hisnul Muslim

Ki yawaita karanta addu'ar Ma'abocin kifi wato Annabi Yunus Ibn Mat'a, a lokacin da kifi ya hadiyeshi sai ya ce:

"La'ilaha illa antas subhanaka inni kunta minazzalimeen"

Kuma ki yawaita karanta addu'ar da Annabi Ibrahim Alaihis Salam ya karanta a likacin da za a jefa shi cikin Wuta:

"Hasbiyallahu wani'imal wakeel"

Da ni dake mu ji tsoron Allaah a cikin ayyukan mu na fili da Kuma musamman na boye (Kamar lokacin da muke danna waya mu kadai ba tareda wani ya ganmu ba). Duk da cewar ba Makhluqin da yake garinmu to ammanfa al-Khaliqu yana ganin mu Sarai

Ya Allaah ka yafe mana

Wallaahu ta'ala a'alam

*Amsawa:_

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments