Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene Ne Ta'addanci A Wajen 'Yan Boko Aqida Masu Tsattsauran Ra'ayin Kyamar Addini?

MENE NE TA'ADDANCI A WAJEN 'YAN BOKO AQIDA MASU TSATTSAURAN RA'AYIN ƘYAMAR ADDINI?

Tsakani da Allah, su fa wadannan 'Yan Boko Aqida masu tsattsauran ra'ayin kyamar Addinin Muslunci, a bisa hakika ba Ahlus Sunna (Wahabiyawa) suke tsangwama suke kalu-balanta ba, Allah da Manzonsa (saw) suke kalu-balanta, saboda duka abubuwan da suke kira da sunan Ta'addanci a cikin Alkur'ani da Sunna suke. Wato abubuwa kamar haka:

1- JIHADI:

Akwai Ayoyi masu yawa a cikin Alkur'ani da suka yi umurni da yaki da Jihadi fiy Sabilillahi, da yabon Muminai masu Jihadin. Daga ciki Allah ya ce:

{وَقَاتِلُوا فِي سَبِيلِ اللَّهِ وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ } [البقرة: 244]

Ya ce:

{ إِنَّ اللَّهَ اشْتَرَى مِنَ الْمُؤْمِنِينَ أَنْفُسَهُمْ وَأَمْوَالَهُمْ بِأَنَّ لَهُمُ الْجَنَّةَ يُقَاتِلُونَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ فَيَقْتُلُونَ وَيُقْتَلُونَ وَعْدًا عَلَيْهِ حَقًّا فِي التَّوْرَاةِ وَالْإِنْجِيلِ وَالْقُرْآنِ } [التوبة: 111]

Ya ce:

{وَجَاهِدُوا فِي اللَّهِ حَقَّ جِهَادِهِ } [الحج: 78]

2- KIN KAFURAI:

Allah ya wajabta mana kin kafurai; Yahudawa da Nasara da Mushrikai. Allah ya ce:

{ يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا الْكَافِرِينَ أَوْلِيَاءَ مِنْ دُونِ الْمُؤْمِنِينَ } [النساء: 144]

Ya ce:

{يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا الْيَهُودَ وَالنَّصَارَى أَوْلِيَاءَ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ وَمَنْ يَتَوَلَّهُمْ مِنْكُمْ فَإِنَّهُ مِنْهُمْ إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ } [المائدة: 51]

3- KASHE WANDA YA YI RIDDA:

Allah ya yi umurni da mutuwa a kan Muslunci, ya ce:

{ يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ حَقَّ تُقَاتِهِ وَلَا تَمُوتُنَّ إِلَّا وَأَنْتُمْ مُسْلِمُونَ} [آل عمران: 102]

Don haka duk wanda ya yi ridda daga Muslunci ya canza Addini to za a kashe shi. Annabi (saw) ya ce:

«من بدل دينه فاقتلوه» صحيح البخاري (9/ 15)

Kuma ya ce:

"لا يحل دم امرئ مسلم، يشهد أن لا إله إلا الله وأني رسول الله، إلا بإحدى ثلاث: النفس بالنفس، والثيب الزاني، والمارق من الدين التارك للجماعة" صحيح البخاري (9/ 5)

4- TSAYAR DA HADDIN ZINA, SATA DA KISAN KAI...

A kan zina Allah ya ce:

{ الزَّانِيَةُ وَالزَّانِي فَاجْلِدُوا كُلَّ وَاحِدٍ مِنْهُمَا مِائَةَ جَلْدَةٍ وَلَا تَأْخُذْكُمْ بِهِمَا رَأْفَةٌ فِي دِينِ اللَّهِ إِنْ كُنْتُمْ تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ } [النور: 2]

Bazawari kuma za a kashe shi, kamar yadda Annabi (saw) ya fada:

«خذوا عني، خذوا عني، قد جعل الله لهن سبيلا، البكر بالبكر جلد مائة ونفي سنة، والثيب بالثيب جلد مائة، والرجم» صحيح مسلم (3/ 1316)

Annabi (saw) ya yi umurni da a jefe wani bazawari bayan ya yi ikrarin zina:

عن أبي هريرة رضي الله عنه، قال: أتى رجل رسول الله صلى الله عليه وسلم وهو في المسجد، فناداه فقال: يا رسول الله، إني زنيت، فأعرض عنه حتى ردد عليه أربع مرات، فلما شهد على نفسه أربع شهادات، دعاه النبي صلى الله عليه وسلم فقال: «أبك جنون» قال: لا، قال: «فهل أحصنت» قال: نعم، فقال النبي صلى الله عليه وسلم: «اذهبوا به فارجموه»

صحيح البخاري (8/ 165) صحيح مسلم (3/ 1318)

A kan sata kuwa Allah ya ce:

{وَالسَّارِقُ وَالسَّارِقَةُ فَاقْطَعُوا أَيْدِيَهُمَا جَزَاءً بِمَا كَسَبَا نَكَالًا مِنَ اللَّهِ } [المائدة: 38]

A kan haddin kisan kai da kisasi kuwa Allah ya ce:

{وَكَتَبْنَا عَلَيْهِمْ فِيهَا أَنَّ النَّفْسَ بِالنَّفْسِ وَالْعَيْنَ بِالْعَيْنِ وَالْأَنْفَ بِالْأَنْفِ وَالْأُذُنَ بِالْأُذُنِ وَالسِّنَّ بِالسِّنِّ وَالْجُرُوحَ قِصَاصٌ } [المائدة: 45]

To amma su 'Yan Boko Aqida masu tsattsauran ra'ayin kyamar Addini suna jin tsoron kar su bayyana kyamarsu ga Alkur'ani da Sunna a fili sai suka fake da zargin littatafan Malaman Ahlus Sunna (Wahabiyawa), alhali duk wani abu da Ahlus Sunna suka fada to za ka samu suna kafa hujja ne da Ayar Alkur'ani ko Hadisin Annabi (saw).

To su abin da suke so shi ne; da za su samu dama da sun canza Alkur'anin nan kamar yadda aka gurbata Bible.

Da za su samu dama da sun goge Ayoyin kyamar kafurai da na Jihadi da tsayar da haddin Ridda da Zina da Sata da sauransu.

To saboda babu yadda za su yi, shi ya sa suka fake da nuna kyama da kiyayya ga Ahlus Sunna da tuhumarsu da Ta'addanci, don su isa zuwa ga hadafinsu.

MATSAYAR MUTANE GAME DA WADANNAN NASSOSHI:

1- AHLUS SUNNA (Wahabiyawa): suka ce: ana yin Jihadi da tsayar da haddi na kisa da sauransu ne a karkashin Gomnati da take da shugaba mai iko da mulki, yake da jami'an tsaro da alkalai da kotuna da kurkuku, mai gudanar da shugabancin kasa gaba daya bisa Shari'ar Muslunci.

2- 'YAN BOKO HARAM: suna daukar doka a hanunsu, suna yin Jihadi da ya saba Shari'a, suna tsayar da haddi karkashin shugaban kungiyarsu.

3- 'YAN BOKO AQIDA masu tsattsauran ra'ayin kyamar Addini: su ba su yarda da wadancan Nassoshi ba, suna ganin ba su dace da zamani ba, yin amfani da su ci baya ne da rashin wayewa a rayuwa. Kuma suna ganin aiki da wadannan nassoshi shi ne tsattsauran ra'ayin Addini, kuma su suke haifar da Ta'addanci.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

11 February, 2018

Ta'addanci

Post a Comment

0 Comments