Ticker

6/recent/ticker-posts

Miji Na Ba Ya Wankan Janaba Da Wuri Har Sai Asubah Ta Yi

TAMBAYA (223)

Nifa mlm abun da nake son yagane idan ya yi sunna da matarshi yaje ya kawar da najasa Amman bashi sai lokacin sallah ya yi sai ya yi wanka yaje sallah da asuba

AMSA

Ya halatta ya jinkirta dinnan

Musamman ma idan ya zamana babu ruwa ko kuma idan ya taba ruwan zai cutu

Mustahabbi ne da ke da mijin kuyi akwala kafin ku koma bacci. Wannan shi ne fahimtar ijma'in malamai. Haka kuma Imam an - Nawawy (Rahimahullah) ya ce: Akwai maganganun malamai akan wannan mas'ala

(Al-Kafi, 1/173; al-Muhadhdhab, 1/33; al-Mughni, 1/229)

A takaice dai ba damuwa bane ba don mijinnaki ya kwana da janaba, domin kuwa Nana Aisha (Radiyallahu anha) ta ce:

"Idan Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yana son yin bacci alhalin a jikinsa akwai janaba, yana wanke gabansa ne sannan sai ya yi alwala irin wadda yake idan zai yi sallah"

(Bukhari da Muslim)

Haka kuma Abdullahi Ibn Umar (Radiyallahu anhum) ya ce: Sayyadina Umar ya ce: Ya Rasulullah, shin ya halatta dayanmu ya yi bacci alhalin yana cikin janaba ?

Sai Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: "Eh, idan ya yi alwala ba"

(Muttafaqun alaihi)

Hikimar yin alwalan kafin a kwanta shi ne: hakan yana rage janabar kuma jiki sai yafi samun nutsuwa

Tuntuni muka wuce wannan karatun a cikin littafin: "MU'AMALAR AURATAYYA A MUSULUNCI", don haka karki damu idan har baiyi wankan da wuri ba

Saidai duk da haka anfi son a dinga wankan akan lokaci saboda ba a son ko da yaushe mutum ya kasance cikin janaba ko don tuna cewar Malaikun Rahama ba sa zuwa gidan da akwai mutum mai najasa har fa sai ya gusar da ita

Wallaahu taala aalam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments