Ticker

6/recent/ticker-posts

Miji Na Ya Neme Ni Bayan Sahur

TAMBAYA (217)

Assalamualaikum warahamatullahi ta'ala wabaraka tuhu mlm barka da war haka ya ibada Allah ya sa mu dace

Tambayata anan ita ce mlm bayan gama sahur mijinah ya nemeni misalin karfe biyar da minti goma nace mishi lokaci ya tafi yace ance ba a aje sahur sai biyar da Rabi Tou abun de har ya so zama matsala tsakaninmu sai na biye mishi har muka gama muka yi wanka biyar da arba in da Tara shin azimi na Yana nan ko kuwa

AMSA

Waalaikumus salam, warahmatullahi, wabarakatuhu

Azumi yana farawa ne da zarar alfijir ya keto sannan ya kare idan rana ta fadi

Jiya Ramadan na farko, karfe 5:30 alfijir yake ketowa

Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: "Idan Bilal ya kira sallah, ku ci ku sha, har sai kun ji kiran sallar Ibn Umm Makhtum"

(Bukhari da Muslim)

Bilal shi ne yake kiran sallah na farko yayinda Abdullahi Ibn Umm Mukhtum yake kiran sallah na biyu. Kuma baya kiran sallah na biyun har sai alfijir ya keto

Idan har ya yi mu'amalar aure dake bayan kiran sallah na farko to wannan ba laifi, azumin ku yananan amman in dai ya nemeki bayan kiran sallah na biyu (Wanda ana kiran ne da zarar alfijir na gaskiya ya keto) to anan ba ku da azumi la'akari da karfe 5:30 ya shiga. Kuma kin ce 5:40 ku ka yi wanka wanda hakan na iya nufin lokacin da kuke mu'amalar auren alfijir ya riga ya keto

Saidai fa idan mutum bai san hukuncin hakan ba amman in dai mutum yasan wannan hukuncin kuma ya yi gangancin shan ruwa ko kuma mu'amalar aure to azumin sa ya baci kuma duk da haka shari'ah ba ta bashi damar ci da sha ba sannan bayan sallah zai rama azumin nan

Imam an - Nawawy (Rahimahullah) ya ce: "...In dai mutum yana mu'amalar aure da matar sa sai alfijir ya keto to zai daina kuma azumin sa yananan amman in dai alfijir ya keto kuma ya ci gaba da mu'amalar to azumin sa ya baci kuma zai rama azumin"

al-Majmoo’ (6/329)

Idan kuma kuna kokwanto ne akan ketowar alfijir din to alhalin kun ji kiran sallar ladan to ba a gina hukunci akan kokwanto kuma azumin ku yananan saboda fadin Allaah Azzawajallah:

( أُحِلَّ لَكُمْ لَيْلَةَ الصِّيَامِ الرَّفَثُ إِلَىٰ نِسَائِكُمْ ۚ هُنَّ لِبَاسٌ لَّكُمْ وَأَنتُمْ لِبَاسٌ لَّهُنَّ ۗ عَلِمَ اللَّهُ أَنَّكُمْ كُنتُمْ تَخْتَانُونَ أَنفُسَكُمْ فَتَابَ عَلَيْكُمْ وَعَفَا عَنكُمْ ۖ فَالْآنَ بَاشِرُوهُنَّ وَابْتَغُوا مَا كَتَبَ اللَّهُ لَكُمْ ۚ وَكُلُوا وَاشْرَبُوا حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَكُمُ الْخَيْطُ الْأَبْيَضُ مِنَ الْخَيْطِ الْأَسْوَدِ مِنَ الْفَجْرِ ۖ ثُمَّ أَتِمُّوا الصِّيَامَ إِلَى اللَّيْلِ ۚ وَلَا تُبَاشِرُوهُنَّ وَأَنتُمْ عَاكِفُونَ فِي الْمَسَاجِدِ ۗ تِلْكَ حُدُودُ اللَّهِ فَلَا تَقْرَبُوهَا ۗ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ اللَّهُ آيَاتِهِ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ )

البقرة (187) Al-Baqara

An halatta a gare ku, a daren azumi, yin jima'i zuwa ga matanku sũ tufa ne a gare ku, kuma kũ tufa ne a gare su, Allah Yã sani lalle ne ku kun kasance kuna yaudarar kanku. Sabõda haka Yã karɓi tũbarku, kuma Yã yãfe muku. To, yanzu ku rungume su kuma ku nmi abin da Allah yã rubũta muku. Kuma ku ci kuma ku sha har sĩlĩli fari ya bayyana a gare ku daga sĩlĩli baƙi daga alfijiri, sa'an nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare. Kuma kada ku rungume su alhãli kuna mãsu itikãfi a cikin masallãtai. Waɗancan iyãkokin Allah ne: don haka kada ku kusancesu kamar haka ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa ga mutãne: tsammãninsu, zã su yi taƙawa.

Anyiwa Committe Fataawa al - Lajnah ad - Da'imah tambaya makamanciyar wannan saidai akan shan ruwa ne yayin da ladan yake kiran sallah kuma amsar da suka bayar ita ce:

"In dai mutum yasan da cewar alfijir ya keto ya sha ruwa to sai ya rama wannan azumin amman in dai alfijir bai keto ba to babu ramuwa akansa"

Fataawa Islamiyyah, 2/240

Sannan kuma idan ka fara cin abincin ne sai aka yi kira na biyu to shi ne shari'ah ta baka damar ka karasa amman anan baza a bawa miji dama ya ci gaba da mu'amalar aure da matarsa ba saboda ba a san tsawon wanne lokaci zai dauka ba

Idan gaba daya mutum bai san wadannan hukunce hukuncen ba to babu laifi akan sa, saidai an so ya rama wannan azumi don samun kwanciyar hankali da kuma kawar da kokwanto sannan mutum ya dage da tuba akan kuskuren da ya yi na rashin sanin abinda yake wajibi a cikin addininsa

Wallaahu ta'ala a'alam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments