Ticker

6/recent/ticker-posts

Mutum Zai Samu Ladan Yada Alkhairi Alhalin Shi Ba Ya Aikatawa

MUTUM ZAI SAMU LADAN YAƊA ALKHAIRI ALHALIN SHI BA YA AIKATAWA

TAMBAYA (215)

Assalamualaikum Mallam dafatan kawuni lfy Mallam inada tambaya

Mutum ya kasance Yana yada alkairi kumashi ya yi karancin aikatawa Kuma yanayin wasu laifuka daban to Mallam Allah zai bashi ladan daya alkairin da yakeyi nagode Mallam

AMSA

Waalaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu

Zai samu ladan wancan alkhairin haka kuma zai samu zunubban daya aikin indai bai yi Taubatun Nasuha ba

Dogaro da Ayar:

( فَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ خَيْرًا يَرَهُ )

الزلزلة (7) Az-Zalzala

To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi.

( وَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ شَرًّا يَرَهُ )

الزلزلة (8) Az-Zalzala

Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi.

Allaah ka tabbatar damu akan aikata ayyukan alkhairi da ikhlasi ka rabamu da zunubbai dakuma riya

Wallaahu taala aalam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments