Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Yi Kuskuren Rubuta Najasa a Maimakon Janaba

NA YI KUSKUREN RUBUTA "NAJASA" A MAIMAKON "JANABA"

TAMBAYA (228)

Assalamu alaikum wa rahmatullah, Malam ina neman karin bayani akan wannan amsar da ka bayar, ka kira maniyi najasa alhalin akwai sabnin malamai akan hukunci maniyi najasa ne ko ba najasa ba.

AMSA

Waalaikumus salam

Warahmatullahi

Wabarakatuhu

Tabbas na yi kuskure anan (TAMBAYA TA 223)

Kamata ya yi nace Malaiku ba sa shiga gida wanda akwai mai janaba ba wai mai najasa ba

Maybe typing error ne ko kuma shaidan ne ya mantar da ni

Hadisin yana cikin Sahih Abu Dawood na Shaikh Muhammad Nasiriddeen al - Albaany (Rahimahullah)

Zan gyara amsar a kundin adana Tambayoyi da Amsoshi in sha Allaah

Mun gode da gyara. Ya Allaah ka gyara zukatanmu

Jazakumullahu khaer😊

@Usmannoor Assafy

JUMA'A GA MAI KASARU

TAMBAYA (229)

Assalamu alaikum. Shin juma’a wajibi ce ga maiyin kasaru?

AMSA

Waalaikumus salam

Sallar Juma'a ba wajibi bane ga matafiyi. Wannan kuma shi ne fahimtar malaman mazhabobi guda 4

Abu Hanifah, Malik, al-Shafi’i da Ahmad

An yiwa Shaykh al-Islam Ibn Taymiyah (Rahimahullah) tambaya akan hakan a cikin al-Fatawa (24/178) sai ya ce: Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yaje Umrah sau 3, hajjin bankwana sannan kuma yaje yaqoqi sama da 20 amman ba a taba rawaito cewar ya yi sallar Juma'a ko ta Idi ba a wannan hali na tafiya. Abin da yake yi shi ne dai wannan raka'o'i 2 na kasaru"

Wallaahu taala aalam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments