RADDI GA PROF. MAQARI A KAN SAUKOWAR ALLAH ZUWA SAMA TA DUNIYA
Dazu dan'uwa Malam Nura ya turo min takaitaccen faifan bidiyo na Prof. Maqari, wanda a cikinsa yake inkarin saukowar Allah zuwa sama ta Duniya, yana tallata Mazhabarsu ta Tawilin Nassoshin Alkur'ani da Sunna.
To, ganin yadda ake ta yada bidiyon, ana fitinar
mutane a Addininsu da shi, ana jefa musu shubuha game da Siffar Allah da
girmansa, sai Malam Nura ya nemi a warware wa mutane shubuhohin da shi Maqari
ya yada.
To, farko dai Hadisin saukowar Allah Hadisi ne
Mutawatiri, wato wanda babu shakka wajen tabbatuwar Annabi (saw) ya fade shi.
Saboda Hadisi ne da Sahabbai 39 suka ruwaito shi, kuma cikin Malaman Hadisi Abu
Zur'ah, Ibnu Hibban, Ibnu Abdulbarr, al-Baihaqiy da al-Zahabiy duk sun tabbatar
da cewa Hadisi ne "Mutawatiri".
To irin wannan Hadisi kuwa dalalarsa ma yankakke
ne, wato babu kokonto a kan abin da Hadisin yake nuni gare shi. Shi ne abin da
ake cewa: (قطعي الثبوت والدلالة).
Ai abu ne da ya tabbata a hankalce; idan Nassi ya
zama (قطعي الثبوت) to dole ya zama (قطعي الدلالة). Abin
nufi, in dai ya tabbata bisa yakini, babu shakka cikin ingancinsa daga Annabi
(saw) to ai kuwa dole abin da Hadisin yake nuni gare shi ya zama tabbas babu
shakka ko kokonto a kansa.
Amma abin mamaki, wadannan mutane 'yan bidi'a,
wadanda ake kira da sunan "Asha'ira" a yau, sai suka ce: sun yarda
Alkur'ani da Hadisi Mutawatiri sun tabbata babu shakka (قطعي الثبوت), amma ba su yarda abin da yake nuni a kansa tabbatacce ne bisa
yakini ba. Don haka Alkur'ani da Hadisi Mutawatiri abin da suke nuni gare shi
zato ne (ظني الدلالة).
Wannan shi ne barna mafi girma da aka yi wa
Addinin Muslunci, aka zo aka ce: Alkur'ani da Hadisi Mutawatiri zato ne.
Wannan ya sa wadannan mutane suke Tawailin Ayoyi
da Hadisai Mutawatirai, balle Hadisai Ahaad, su zo su juya su, su fassara su
bisa ra'ayoyinsu, sabanin zahirin Nassin.
Miye dalilinsu? Shi ne Nassoshin sun saba ma
ra'ayoyi da ka'idojinsu na hankali. Don haka asali su hankulansu suke bi, a
maimakon su bi Alkur'ani da Sunna.
Wannan shi ne farkon abin da ya raba hanyar 'yan
bidi'a, da hanyar Ahlus Sunna. Su kam Alkur'ani da Sunna ne gaba da ra'ayoyinsu
da fahimtarsu.
To, Maqari ya fadi wasu shubuhohi, yana tambaya a
kansu ta hanyar hikaya, -wai- yake cewa
"An ce Allah yana saukowa, zuwa sama ta uku
ko? a tsakiyan dare... Ai zuwa sama ta daya. Sai su ce: a "Sulusul lailil
akheer"".
Sai ya ce
"Sai su fara tambaya to, wa ya bari a can
wajen, a lokacin da ya sauko, wajen ya zama babu shi ne?".
"Kuma "sulusul laili" din wani
gari? Tun da "sulusul lailin" daya ne yana canzawa, na wane
gari?".
"Sannan da ya sauko, can din sun koma saman
shi kenan? Sun zama a saman Allah kenan?".
To ka ga matsalar da Maqari ya samu, shi da sauran
'yan Mazhabarsa ita ce, suna kamanta Allah da mutum ne a kwakwalensu, suna
ganin cewa; saukowar Allah irin ta mutum ce. Shi ya sa suke yin irin wadannan
tambayoyi.
Mutum ne za ka yi irin wadannan tambayoyi game da
saukowarsa ba Allah ba. Saboda a saukowar mutum ne za a samu irin wadannan
abubuwa ba na Allah ba. Mutum ne muka san irin saukowarsa, amma saukowar Allah
ba mu san yadda take ba, balle mu yi tunanin za a samu wadannan abubuwa da ya
yi tambayoyi a kansu.
Misali: idan an ce: Alhaji Idi yana saukowa a
"sulusin" dare na farko, daga beni hawa na 12, zuwa hawa na 2, a nan
ne za ka yi wadancan tambayoyi, ka ce: Wa Alhaji Idi ya bari a can hawa na 12,
a lokacin da ya sauko, wajen ya zama babu shi ne?
Kuma "sulusul laili" na farkon wani gari
ne Alhaji Idi yake saukowa? Tun da "sulusul lailin" na farko daya ne,
yana canzawa, to na wane gari ne?
Sannan da Alhaji Idi ya sauko beni hawa na 2, can
sauran hawannin sun koma saman shi kenan? Sun zama a saman Alhaji Idi kenan?
To mutum ne za ka yi irin wadannan tambayoyi a kan
saukowarsa, ba saukowar Allah ba. Saboda siffofin Allah gaibi ne. Ba mu san
yaya yake yinsu ba, kuma bai ba mu labari ba. Kuma shi ba shi da makamanci,
balle mu yi irin tambayoyin da za mu yi a saukowar Alhaji Idi a saukowar Allah!
Allah ya ce
﴿لَیۡسَ كَمِثۡلِهِۦ شَیۡءࣱۖ﴾ [الشورى: ١١]
Saboda haka asali wadannan tambayoyi da Maqari ya
yi duka kuskure ne, don ya yi su ne bisa abin da ya zo a tunaninsa cewa:
saukowar Allah irin ta halittu ne, don su ne muka san cewa: idan sun sauko daga
sama to sun sauko gaba daya, ba su bar sauransu a can ba. Kuma su ne lokaci a
wurinsu guda daya ne, idan sun sauko a "sulusin" dare na Nigeria, to
a lokacin rana ne, ko safiya a wasu yankuna na duniya. Amma saukowan Allah, ba
mu sani ba. Amma dai mun san cewa: Allah mai iko ne a kan komai, babu abin da
zai gagare shi. Ma'ana; Allah shi ya halicci lokacin, yana da iko ya sanya
sulusin dare da yake saukowa ya zama duka sulusin dare ne a dukkan duniya. Yana
da iko a kan haka. Amma yaya yake saukowa, shin idan ya sauko sama ta daya,
sama ta biyu har zuwa ta bakwai, da Kursiyyi da al-Arshi duk suna sama da shi
kenan?
Sai mu ce mu ba mu sani ba, Allah bai ba mu labari
ba. Amma yana da ikon ya sauko sama ta daya, ba tare da sauran sammai sun zama
a sama da shi ba. Don shi mai iko ne a kan komai. Kuma shi mai girma ne, duka
sammai da kassai da halittu a tafin hanunsa suke.
Wallahi da a ce mutane sun san girman Allah da ba
su yi tunanin a saukowar Allah za a samu irin abubuwan da suke gani ana samu a
saukowar halittu ba.
﴿وَمَا قَدَرُوا۟ ٱللَّهَ حَقَّ قَدۡرِهِۦ وَٱلۡأَرۡضُ جَمِیعࣰا
قَبۡضَتُهُۥ یَوۡمَ ٱلۡقِیَـٰمَةِ وَٱلسَّمَـٰوَ ٰتُ مَطۡوِیَّـٰتُۢ
بِیَمِینِهِۦۚ سُبۡحَـٰنَهُۥ وَتَعَـٰلَىٰ عَمَّا یُشۡرِكُونَ ٦٧﴾ [الزمر: ٦٧]
Saboda haka duka wadannan shubuhohi ne masu rauni,
wadanda Maqari ya dauko daga magabatansa, yake maimaitawa, irin su Raziy, Ibnu
Jama'a da sauran Malaman Asha'ira, alhali tun tuni Malaman Sunna sun markade
wadannan shubohohi, sun warware su, sun tona asarinsu, suka nuna yadda suka
kunshi kamanta Allah da mutum.
Sai kuma Maqari ya yi wata magana wacce fadinta
kawai ta isa duk mai hankali ya fahimci bacinta. Inda ya nuna cewa: wai daga
karni na hudu, har zuwa karnin Ibnu Taimiyya, har wannan zamani, wai Malaman
Muslunci Tawili suke yi.
Ma'ana yana nufin, su wadannan Malamai da yake
nufi (Malaman Asha'ira), sun saba wa Malaman farko, a karni na daya har zuwa
karni na uku. Wato su wadannan Malamai ba su san Tawili ba, su suna aiki da
abin da ya zo a cikin Nassi ne. Ma'ana: tun da Allah ya ce yana da fiska, hanu,
kuma ya yi Istiwa'i a saman al-Arshi. Annabi (saw) ya ce: Allah yana da kafa,
kuma yana saukowa, to suna tabbatar da su a haka ne ba tare da Tawili da canza
maganar Allah da Manzonsa ba.
To don Allah, yaya za a yi wadanda suka sake
hanyar Sahabbai, da Tabi'ai da Tabi'ut Tabi'ina, su zama su ne a kan dadai?!
Yaya za a yi wadanda suka canza maganar Allah da
Manzonsa, suka canza abin da Malaman karni na farko da na biyu da na uku suke
kai su zama su ne a kan dadai?!
Wannan ba zai yiwu ba.
Don haka su wadannan Malaman karni na hudu iyo
baya - wadanda Maqari yake nufi - sun kirkiri bidi'a, sun zo da sabuwar hanya,
wacce ba a santa a karnoni ukun farko ba, alhali su ne karnoni mafi alheri da
shiriya kamar yadda Annabi (saw) ya fada.
To don Allah, saba hanyar Malaman karni na daya,
na biyu da na uku, abin yabo ne ko abin zargi?!
Amma shi Maqari har cika baki yake yi, wai sai ka
samu Malamai dari ko hamsin suna Tawili, kafin ka samu Malami daya da ba ya yi.
To ai wannan din ba gwaninta ba ne ya Prof.!
Wannan din abin zargi ne, saba tafarkin Muminan
farko ne. Shi ya sa Allah ya zargi wannan Manhaji, inda ya ce
﴿وَمَن یُشَاقِقِ ٱلرَّسُولَ مِنۢ بَعۡدِ مَا تَبَیَّنَ لَهُ
ٱلۡهُدَىٰ وَیَتَّبِعۡ غَیۡرَ سَبِیلِ ٱلۡمُؤۡمِنِینَ نُوَلِّهِۦ مَا تَوَلَّىٰ
وَنُصۡلِهِۦ جَهَنَّمَۖ وَسَاۤءَتۡ مَصِیرًا﴾ [النساء: ١١٥]
Don haka saba tafarkin Malaman karnoni ukun farko
abin zargi ne ba abin yabo ba. Saboda saba Ijma'i ne. Imam Abul Hassan
al-Ash'ariy ya ce
"الإجماع الثامن
وأجمعوا على أنه عز وجل يجيء يوم القيامة والملك صفا صفا،
لعرض الأمم وحسابها وعقابها وثوابها...
وأنه عز وجل ينزل إلى السماء الدنيا، كما روي عن النبي صلى
الله عليه وسلم...".
رسالة إلى أهل الثغر (ص: ٢٢٧ - ٢٢٩).
Ga shi karara saukowar Allah zuwa sama ta duniya
mas'ala ce ta Ijma'i, kamar yadda al-Ash'ariy da kansa ya hakaito.
To miye hukuncin wadanda suka saba Ijma'i?!
Saboda haka maganganun Prof. Maqari maganganu ne
marasa hujja. Kuma shubuhohi don yada barna da bata a cikin al'umma.
A cikin maganarsa ya ayyana ma'anar da ya bayar wa
saukowar Allah din, inda ya ce: -wai- abin nufi shi ne rahmar Allah tana kara
kusantar bayi!
Ta yaya ya gane wannar ma'ana?
Ma'ana kenan rahmar Allah ba ta kara kusantar bayi
sai a wannan lokaci?
Ta yaya ka san haka?
In ka ce daga Hadisin ne, sai mu ce: a'a, Hadisin
saukowar Allah da kansa aka ambata ba rahmarsa ba.
Prof. Maqari ya yi ta wasu maganganu wadanda babu
hujja a cikinsu ko kadan, sai kame-kame.
Saboda haka Tawilin da Prof. Maqari ya yi wa
Hadisin saukowar Allah zuwa sama ta duniya, ya ce: saukowar rahmar Allah ce ba
saukowar Allah ba, bidi'a ce da bata mummuna, da canza maganar Annabi (saw) da
saba hanyar Muminai, Malaman karnoni ukun farko, masu falala da alheri.
✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.