Ticker

    Loading......

Shekarar Mu 3 Muna Soyayya Ko Zan Iya Rabuwa Da Shi

SHEKARAR MU 3 MUNA SOYAYYA, KO ZAN IYA RABUWA DA SHI

TAMBAYA (225)

Salam. Malam ina wuni ya ibada malam akwae Wanda yake Neman aurena Amman munfi shekara Ükku dashi Sai yace za a zo ayi magana kuma yana sona sosai dangin shi ma uwa Uba mahifiyarshi to malam zan iya na rabu dashi kokuwa zamu ci gaba da addua ne Nagode

AMSA

Waalaikumus salam

Baki fito da tambayar gaba daya ba. Da yace za a zo ayi magana, shin an zo ne ko kuma ana shirin zuwa ne. Ko kuma ya yi miki karya ne akan wani abu ? Mene ne dalilin da ya sa kike son rabuwa dashi ?

Shawarar da zan baki anan ita ce:

In dai kin yarda da dabi'unsa kuma yana da addini wannan ba za a ce ki rabu dashi kai tsaye ba

A cikin tambayar taki baki fadada bayanan ba don haka bazan san hukuncin da zan iya yankewa akan soyayyar ku ba

Idan har kunsan ba kuyi addu'an Istikhara ba a rashin sani to ku gaggauta yin ta don gudun ka da Allaah ya barku da zabin ku

Malamai suka ce ko ana gobe za a daura muku aure ana son ku sake yin addu'an Istikhara don ci gaba da bawa Allaah zabi

Muna rokon Allaah idan akwai alkhairin duniya da na lahira a cikin alakar taku Allaah ya tabbatar idan kuma babu Allaah ya musanyawa da kowannen ku da abin da zai zame masa khaeran

Wallaahu taala aalam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments