Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Malam Ja'afar Da Albaniy Zaria Da Malamai Ire–Irensu Mujtahidai Ne?

SHIN MALAM JA'AFAR DA ALBANIY ZARIA DA MALAMAI IRE–IRENSU MUJTAHIDAI NE?

A kullum in an yi inkari ga 'Yan Kungiyar Salafiyyun masu guluwwi a Bidi'antar da Malaman Sunna da cewa; Malaman da suke bidi'antarwa Ahlus Sunna ne, kuma masu kuskure ne bisa Ijtihadi ba son rai ba, don haka bai halasta ku soke su ba, balle ku bidi'antar da su, sai su ce: ai su Malaman ba Mujtahidai ba ne, balle a ce sun yi kuskure.

To alal hakika wannan shubuha ce saboda jahilci, saboda su suna kallon sunan "Mujtahidi" ne bisa ma'anarsa ta Istilahin Malaman "Usulul Fiqh", ba a ma'ana ta Shari'a ba. Wannan shi yake nuna tsananin bukatar sanin hakikanin ma'anar "Mujtahidi" a Shari'a.

Asalin Ijtihadi da ake magana a kansa, wanda Allah yake yin uzuri ga ma'abocinsa, kuma yake gafarta kuskuren mai yinsa, ya ba shi lada daya a kan Ijtihadin nasa, shi ne Mujtahidi bisa ma'ana ta Shari'a - ba ma'ana ta Isdilahin Malaman Usulul Fiqh kawai ba -. Wato shi ne DUK MUMININ DA YA YI NUFIN BIN ALLAH DA MANZONSA (SAW), YA YI IYA KOKARINSA WAJEN DA'A MA ALLAH A KAN WANI ABU NA AIKI KO NA ILIMI A SHARI'A. TO IN YA YI KUSKURE SHI BA ABIN ZARGI BA NE A SHARI'A.

Wannan shi ne abin da Allah yake magana a kansa a cikin wadannan Ayoyi kamar haka:

1- Allah ya ce:

{لَا يُكَلِّفُ اللَّهُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا } [البقرة: 286]

"Allah ba zai dora ma wata rai ba face abin da za ta iya".

Saboda haka Allah ba zai kama rai a kan abin da ta yi iya kokarinta amma sai ta kuskure ba.

2- Shi ya sa a gaba ya ce:

{رَبَّنَا لَا تُؤَاخِذْنَا إِنْ نَسِينَا أَوْ أَخْطَأْنَا } [البقرة: 286]

"Ya Ubangijinmu kar ka kama mu da laifi in mun yi mantuwa ko mun yi kuskure".

Hadisi ya tabbata cewa; Allah ya amsa wannar addu'a.

Wannan ya sa Allah ya umurce mu da abin da za mu iya yi.

3- A inda ya ce:

{فَاتَّقُوا اللَّهَ مَا اسْتَطَعْتُمْ } [التغابن: 16]

"Ku ji tsoron Allah iya ikonku".

Abin da Allah ya yi umurni da shi cikin wannar Aya shi ne Ijtihadi, ma'ana; Mumini ya ji tsoron Allah iya iyawarsa, iya ikonsa. In ya yi kuskure bai isa ga asalin abin da yake dadai ba, Allah zai gafarta masa kuskuren nasa.

Da yake tafsirin Ayar, Ibnu Jarir ya ce:

وقوله: {فاتقوا الله ما استطعتم} [التغابن: 16] يقول تعالى ذكره: واحذروا الله أيها المؤمنون وخافوا عقابه، وتجنبوا عذابه بأداء فرائضه واجتناب معاصيه، والعمل بما يقرب إليه ما أطقتم وبلغه وسعكم.

تفسير الطبري = جامع البيان ط هجر (23/ 19)

Ma'ana; ku yi abin da za ku iya yi gwagwadon ikonku.

Al-Wahidiy ya hakaito daga Al-Rabee'i:

{فاتقوا الله ما استطعتم} [التغابن: 16] ما أطقتم، وقال الربيع: اتقوا الله جهدكم.

التفسير الوسيط للواحدي (4/ 309)

Ya ce: "Ku ji tsoron Allah iya Ijtihadinku".

Shaikhul Islami ya ce:

قال تعالى: {فاتقوا الله ما استطعتم} فإذا تفقه السالك وتعلم الأمر والنهي بحسب اجتهاده وكان علمه وإرادته بحسب ذاك فهذا مستطاعه. وإذا أدى الطالب ما أمر به وترك ما نهي عنه وكان علمه مطابقا لعمله فهذا مستطاعه.

مجموع الفتاوى (10/ 489)، جامع الرسائل لابن تيمية - رشاد سالم (2/ 113)

A wani wajen kuma ya ce:

وجماع هذا الأصل أن الله تعالى يقول: {فاتقوا الله ما استطعتم} [التغابن:16]، فمن كان من أهل الإيمان واجتهد في طاعة الله ورسوله علما وعملا فلا ملام عليه، بل يغفر الله له خطأه، ويثيبه على صوابه.

جامع المسائل لابن تيمية (8/ 441)

Don haka ashe kowane Mumini Mujtahidi ne, ba Mujtahidi shi ne wanda aka yi maganarsa a Usulul Fiqhi kawai ba.

Sai kuma Hadisai daga Annabi (saw).

1- Daga ciki ya ce:

عن ابن عباس أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: "إن الله تجاوز عن أمتي الخطأ والنسيان وما استكرهوا عليه"

صحيح ابن حبان - محققا (16/ 202)

"Lallai Allah ya yafe ma al'ummata kuskure da mantuwa da abin da aka tilasta musu a kansa".

Kuskure shi ne duk abin da mutum ya yi ba da ganganci ba, da nufin bin Allah da Manzonsa, gwargwadon iliminsa ba tare da sakaci ba, amma sai ya kuskure ma dadai.

2- Da kuma fadinsa (saw):

«إذا حكم الحاكم فاجتهد ثم أصاب فله أجران، وإذا حكم فاجتهد ثم أخطأ فله أجر»

صحيح البخاري (9/ 108) صحيح مسلم (3/ 1342)

"Idan Alkali zai yanke hukunci, sai ya yi Ijtihadi (ya yi iya kokarinsa bisa ilimin da yake da shi) sai ya dace da dadai to yana da lada biyu, in kuma ya yi hukunci da Ijtihadin amma sai ya yi kuskure to yana da lada daya".

Shaikhul Islami ya ce:

قد يخفى على الإنسان بعض سنة الرسول وأمره مع اجتهاده في طاعته، فلا يكلف الله نفسا إلا وسعها. ولهذا قال النبي صلى الله عليه وسلم: «إذا اجتهد الحاكم فأصاب فله أجران وإذا اجتهد فأخطأ فله أجر». أخرجاه في الصحيحين

الإخنائية أو الرد على الإخنائي ت زهوي (ص: 12)

Sai ya nuna cewa; Ijtihadi ya shafi kowane Musulmi, ba kawai Mujtahidin Usulul Fiqhi ba.

3- Da kuma fadinsa (saw):

«فإذا نهيتكم عن شيء فاجتنبوه، وإذا أمرتكم بأمر فأتوا منه ما استطعتم»

صحيح البخاري (9/ 94 - 95) صحيح مسلم (4/ 1830)

"In na hane ku da wani abu to ku nisance shi, in kuma na umurce ku da wani abun to ku aikata shi gwargwadon ikonku".

Ibnu Rajab Al-Hambaliy yana sharhin Hadisin sai ya ce:

الذي يتعين على المسلم الاعتناء به والاهتمام أن يبحث عما جاء عن الله ورسوله صلى الله عليه وسلم، ثم يجتهد في فهم ذلك، والوقوف على معانيه، ثم يشتغل بالتصديق بذلك إن كان من الأمور العلمية، وإن كان من الأمور العملية، بذل وسعه في الاجتهاد في فعل ما يستطيعه من الأوامر، واجتناب ما ينهى عنه، وتكون همته مصروفة بالكلية إلى ذلك؛ لا إلى غيره. وهكذا كان حال أصحاب النبي صلى الله عليه وسلم والتابعين لهم بإحسان في طلب العلم النافع من الكتاب والسنة.

جامع العلوم والحكم ت الأرنؤوط (1/ 244)

"Abin da ya wajaba a kan Musulmi ya kula da shi ya ba da himma a kansa shi ne ya yi bincike akan abin da ya zo daga Allah da Manzonsa (saw), (wato Alkur'ani da Hadisai), sa'annan sai ya yi IJTIHADI wajen fahimtarsu da isa ga ma'anoninsu, sa'annan ya shagaltu da gaskata su in lamura ne na ilimi (Aqida), in kuma lamura ne na aiki (Fiqhu) to sai ya yi iya kokarinsa ya yi Ijtihadi wajen aikata abin da zai iya yi na umurnin, da kuma nisantar abin da aka hana, wannan ya zama shi ne himmarsa. Kuma wannan shi ne halin Sahabban Annabi (saw) da wadanda suka bi su da kyautatawa wajen neman ilimi mai amfani daga Littafin Allah da Sunnar Manzonsa (saw)".

Ga shi a fili sai ya rataya Ijtihadin ga dukkan Musulmi. Wato kowa zai yi Ijtihadi, balle kuma Malamai.

Ibnul Wazeer Al-Yamaniy ya ce:

"قد ثبت في الصحيح عن رسول الله - صلى الله عليه وسلم - أنه قال: ((إذا أمرتكم بأمر فأتوا منه ما استطعتم)) فيجب بذل الاستطاعة في تعرف ما آتانا الله تعالى من معلوم ومظنون, فأعلى المراتب: أن نعلم اللفظ والمعنى, ودون ذلك: أن نعلم اللفظ ونظن المعنى. ودون ذلك: أن نعلم المعنى ونظن اللفظ أو نظنهما معا".

الروض الباسم (2/ 491) وانظر أيضا: العواصم والقواصم (2/ 365)

Wadannan Nassoshi su suka zo suke bayani a kan ma'anar Ijtihadi da Mujtahidi a Shari'a, kuma da bayanin hukuncinsa. Inda muka ga cewa; kowane Mumini Mujtahidi ne, wajibi ne ya yi Ijtihadi, ya yi iya kokarinsa wajen bin abin da Allah da Manzonsa suka yi umurni da shi, kuma wanda ya yi kuskure Allah zai yafe masa kuskuren, kuma zai ba shi lada daya a kan Ijtihadin nasa, kuma shi ba abin zargi ba ne, shi mai uzuri ne a Duniya da Lahira.

Don haka wannan shi ne Ijtihadin da Allah ya rataya yafiya ga kuskuren ma'abocinsa, ba sai Ijtihadi bisa ma'ana ta Istilahin Malamai Usulul Fiqhi ba.

Ga karin wasu bayanan daga maganganun Shaikhul Islami a kan haka:

Shaikhul Islami ya ce:

العجز يكون عذرا للإنسان في أن الله لا يعذبه إذا اجتهد الاجتهاد التام. هذا على قول السلف والأئمة في أن من اتقى الله ما استطاع إذا عجز عن معرفة بعض الحق لم يعذب به.

مجموع الفتاوى (5/ 563)

Ya nuna Ijtihadi ya shafi kowane mutum, ba Mujtahidin Usulul Fiqhi kawai ba.

Kuma ya ce:

من استفرغ وسعه في طلب رضا الله فاتقى الله ما استطاع كان من عباد الله الصالحين، وإن كان قد أخطأ في بعض ما اجتهد فيه

جامع المسائل لابن تيمية (7/ 105)

Kuma ya ce:

من كان قصده متابعته (الرسول) من المؤمنين، وأخطأ بعد اجتهاده الذي أستفرغ به وسعه غفر الله له خطأه، سواء كان خطؤه في المسائل العلمية الحبرية، او المسائل العملية

درء تعارض العقل والنقل (1/ 277)

"Duk Muminin da manufarsa ita ce bin Manzon Allah (saw) sai ya yi kuskure bayan Ijtihadinsa Allah zai gafarta masa kuskuren nasa, sawa'un a mas'alolin Ilimi (Aqida) ne ko na aiki (Fiqhu)".

Kuma ya ce:

المجتهد المستدل من إمام وحاكم وعالم وناظر ومناظر ومفت وغير ذلك إذا اجتهد واستدل فاتقى الله ما استطاع، كان هذا هو الذي كلفه الله إياه، وهو مطيع لله مستحق للثواب إذا اتقاه ما استطاع، ولا يعاقبه الله البتة

مجموع الفتاوى (19/ 216 – 217)، منهاج السنة النبوية (5/ 111)

A nan kuma ya tabbatar mana da cewa; Shugaba da Alkali da Malami da Mai Nazari da Mai Munazara da Mai Fatawa duka Mujtahidai ne masu yin Ijtihadi, matukar sun ji tsoron Allah sun cancanci lada, kuma Allah ba zai yi musu uquba ba.

Sa'annan shi Ijtihadin nan ba abu daya ne dunkulalle ba, da za a ce dole sai mutum ya same shi kafin ya zama Mujtahidi, abu ne da yake iya rarrabuwa, kowa Mujtahidi ne gwargwadon iliminsa da kokarinsa.

Shaikhul Islam ya ce:

والاجتهاد ليس هو أمرا واحدا لا يقبل التجزي والانقسام بل قد يكون الرجل مجتهدا في فن أو باب أو مسألة دون فن وباب ومسألة وكل أحد فاجتهاده بحسب وسعه

مجموع الفتاوى (20/ 212)

A wani wajen kuma ya ce:

وجمهور علماء المسلمين على أن القدرة على الاجتهاد والاستدلال مما ينقسم ويتبعض، فقد يكون الرجل قادرا على الاجتهاد والاستدلال في مسألة أو نوع من العلم دون الآخر، وهذا حال أكثر علماء المسلمين، لكن يتفاوتون في القوة والكثرة، فالأئمة المشهورون أقدر على الاجتهاد والاستدلال في أكثر مسائل الشرع من غيرهم

منهاج السنة النبوية (2/ 244 – 245)

Kuma ya ce:

والاجتهاد يقبل التجزئة والانقسام بل قد يكون الرجل مجتهدا في مسألة أو صنف من العلم ويكون غير مجتهد في مسألة أو صنف آخر

مختصر الفتاوى المصرية (ص: 555)

Kai har gama gari (a~mmiy) shi ma zai yi Ijtihadi gwargwadon abin da ya sani balle kuma malamin da koya ya yarda shi malami ne.

Ya ce:

وكذلك العامي إذا أمكنه الاجتهاد في بعض المسائل جاز له الاجتهاد فإن الاجتهاد منصب يقبل التجزي والانقسام فالعبرة بالقدرة والعجز وقد يكون الرجل قادرا في بعض عاجزا في بعض لكن القدرة على الاجتهاد لا تكون إلا بحصول علوم تفيد معرفة المطلوب

مجموع الفتاوى (20/ 204)

Saboda haka da wannan za ka san cewa; ashe in an ce; "Mujtahidi ba abin zargi ba ne", to ba kawai Mujtahidin da Malaman Usulul Fiqhi suka yi bayani ake nufi ba, a'a, Mujtahidi ya shafi dukkan Muminin da ya yi iya kokarinsa wajen bin umurnin Allah da Manzonsa, bisa iya iliminsa da kokarinsa. To in ya yi kuskure shi ba abin zargi ba ne, kuma Allah zai gafarta masa kuskuren.

To yanzu wanda ya san wannan, yaushe zai kalli Malaman Sunna, wadanda ake dauka a matsayin manyan Malaman al'umma a Nigeria, masu fatawa da jagoranci a ilimi ya dauke su a matsayin wadanda ba Mujtahidai ba?!

Bayan mun san hakikanin Mujtahidi a Shari'a, to menene hukuncin masu zargin mai kuskure a Ijtihadinsa, kamar yadda 'Yan Kungiyar Salafiyyun suke yi, suke zargin Malaman Sunna a kan kurakuransu bisa Ijtihadi wajen da'a ma Allah a Da'awa da inkarin Munkari?

Shaikhul Islami ya ce:

من جعل كل مجتهد في طاعة أخطأ في بعض الأمور مذموما معيبا ممقوتا فهو مخطئ ضال مبتدع.

مجموع الفتاوى (11/ 15)

"Duk wanda ya sanya kowane Mujtahidi mai kokari wajen da'a ma Allah wanda ya yi kuskure a wasu lamura ya sanya shi a matsayin abin zargi, abin aibantawa, abin tsananta masa kiyayya to shi mai kuskure ne batacce Dan Bidi'a".

Ya zama batacce Dan Bidi'a ne saboda ya kirkiri wata hanya da Manhaji da suka saba Manhajin Annabi (saw) da Sahabbansa na jarhin Mujtahidai, kuma ya saba ma nassoshin Alkur'ani da Sunna da suka gabata.

Da wannan za ka san kuskuren 'Yan Kungiyar Salafiyyun, masu zargi da da jarhi da bidi'antar da malaman Sunnan wadanda suka yi Ijtihadi a Da'awa kuma suka yi kuskure.

Wasu mas'aloli guda biyu da za su kara bayyana mana kuskuren wadannan 'yan kungiya su ne:

(1) Da suke Da'awar babu Mujtahidi a Nigeria, to shin babu alkalai ne a Nigeria?

Ko Alkalai ba Mujtahidai ba ne bisa nassin Hadisin Annabi (saw)?!

Kuma kowa ya san cewa; Malaman Sunnan da suke zargi suke bidi'antarwa, suke kira da sunaye na jarhi da bidi'antarwa; Sururiyya, Qutbiyyah, Hizbiyyun da Salafiyyar Ikhwaniyya da makamancin haka, wadannan Malamai sun fi da yawa daga cikin Alkalan da muke da su ilimi, da yawansu ba su wuce matsayin almajiran wadannan malamai ba. Amma a hakan 'Yan Kungiyar Salafiyyun suke raya cewa; Malaman da suke bidi'antarwan ba Mujtahidai ba ne, balle a yi musu uzuri.

(2) Su da suke kafa teburin lakcoci a Kaduna da kasar Ghana, da shafukansu na Facebook suna sukan Malaman Sunnan, suna bidi'antar da su, shin su sun kai matsayin Ijtihadin ne, sun zama Mujtahidai ne shi ya sa suke yanke hukunci da bidi'antar da Malaman?!

Alhali yanke hukunci a kan Addinin mutane ya fi yanke hukunci a kan lamuransu na Duniya girma da hatsari!

Kuma duka daliban ilimi sun san cewa; Bidi'antarwa bakin rijiya ne ba wajen wasan yaro ba ne.

To ka ga a lokacin da suke magana a kan Malaman Sunnan da kowa ya yarda Malamai ne, suke cewa; su ba Mujtahidai ba ne, su kuma a lokacin suka nada kawunansu a matsayin Mujtahidai masu yanke hukunci a kan Addinin Malaman da Bidi'antar da su.

Wane irin gafala ne haka, ka ce: Malaman ba Mujtahidai ba ne, amma kai kuma ka nada kanka matsayin Mujtahidi, alhali kai ba malami ba ne?!

Saboda haka da wannan za ka fahimci girman jahilci da kuskuren wadannan 'Yan Kungiyar da sunan Salafiyya.

Allah ya shiryar da mu gaba daya.

✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

       22 January, 2018

Mujtahidai

Post a Comment

0 Comments