TAMBAYA (222)❓
Assalamu alaikum warahmatullah malam yahidima damu Ubangiji ya saka dagidan aljannah firdaus mlm ina tare damara lfy jikinta akwai fitsari bata iya komai sai ammata amma tana hankalinta za a mata taimamane ko alwala,Allah yakara lfy
AMSA❗
Taimama za
ta dinga yi in Sha Allaah saboda fadin Allaah Azzawajallah:
( يَا أَيُّهَا
الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَقْرَبُوا الصَّلَاةَ وَأَنتُمْ سُكَارَىٰ حَتَّىٰ
تَعْلَمُوا مَا تَقُولُونَ وَلَا جُنُبًا إِلَّا عَابِرِي سَبِيلٍ حَتَّىٰ
تَغْتَسِلُوا ۚ وَإِن كُنتُم مَّرْضَىٰ أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ أَوْ جَاءَ أَحَدٌ
مِّنكُم مِّنَ الْغَائِطِ أَوْ لَامَسْتُمُ النِّسَاءَ فَلَمْ تَجِدُوا مَاءً
فَتَيَمَّمُوا صَعِيدًا طَيِّبًا فَامْسَحُوا بِوُجُوهِكُمْ وَأَيْدِيكُمْ ۗ إِنَّ
اللَّهَ كَانَ عَفُوًّا غَفُورًا )
النساء (43) An-Nisaa
"Yã ku
waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku
kusanci salla alhãli kuwa kuna mãsu mãye, sai kun san abin da kuke faɗa kuma haka idan
kuna mãsu janaba, fãce mai ƙẽtare hanya, har ku yi wanka. Kuma idan
kun kasance majinyata, ko kuwa a kan tafiya ko kuwa wani daga cikinku, idan ya
zo daga kãshi, kõ kuwa kun shãfi mãtã ba ku sãmi ruwa ba, to ku nufi, fuskar ƙasa mai kyau, ku yi shãfa ga fuskokinku da hannuwanku.
Lalle ne Allah Yã kasance Mai yãfẽwa Mai gãfara"
Idan ba za
ta iya ba sai a dinga yi mata sannan kuma za ta iya sallar a zaune ko a kwance
ko kuma idan duk ba za ta iya ba sai ta dinga kudurcewa a zuciyarta kamar yanda
ya tabbata a cikin littafin: "Sifatu Salatin Naby"
Wannan duk
saukine daga addinin Musulunci kamar yanda muka yi bayani a lecture mu ta farko
cikin littafin: "KURA KURAI 100 A CIKIN SALLAR MU"
Wasu suna
ganin idan suna kula da mara lafiya ba sai ya yi sallah ba alhalin yin sallah a
lokacin ta dole ne, ga mara lafiya, matafiyi ko mazaunin gida. Allaah
Azzawajallah ya ce:
( فَإِذَا قَضَيْتُمُ
الصَّلَاةَ فَاذْكُرُوا اللَّهَ قِيَامًا وَقُعُودًا وَعَلَىٰ جُنُوبِكُمْ ۚ
فَإِذَا اطْمَأْنَنتُمْ فَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ ۚ إِنَّ الصَّلَاةَ كَانَتْ عَلَى
الْمُؤْمِنِينَ كِتَابًا مَّوْقُوتًا
)
النساء (103) An-Nisaa
Sa'an nan
idan kun ƙãre salla, to ku ambaci Allah tsaye da zaune da a kan
sãsanninku. Sa'an nan idan kun natsu, to, ku tsayar da Salla. Lalle ne salla tã
kasance a kan mũminai, farilla mai ƙayyadaddun lõkuta.
Shaykh
al-Islam Ibn Taymiyah (Rahimahullah), a cikin Majmoo‘ al-Fatawa (22/293) dinsa
ya ce:
"Ya
halatta mara lafiya ko matafiyi ya hade sallar azahar da la'asar ko magariba da
Isha'i kamar yanda ya halatta a hadesu lokacin da ake ruwan sama. Duk wannan
sauki ne ga al'ummah"
Haka kuma
Committee Fatawa al-Lajnah ad-Daa’imah, a cikin mujalladi na 8 shafi na 83,
sunce ya halatta mara lafiya ya yi sallah a tsaye idan ba zai iya ba ya yi a
zaune, idan ba zai iya ba sai ya yi a kwance sannan da mara lafiya da matafiyi
za su iya hade sallolin Azahar da La'asar da kuma Magariba da Isha'i
Wallaahu
taala aalam
Amsawa:
Usman
Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.