Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsakanin Sahihul Bukhari Da Sahihu Muslim Da Littafin "The Organon" Na Aristotle

TSAKANIN SAHIHUL BUKHARI DA SAHIHU MUSLIM DA LITTAFIN "THE ORGANON" NA ARISTOTLE

Yauzu me kake ganin zai faru idan muka ce karya ne, Aristotle ba shi da wani littafi mai suna The Organon, kawai wani ne ya sharara karya, ya kirkiri littafin ya jingina masa shi?

Yau tsakaninmu da Aristotle kusan shekara 2400 ne. Don haka ta yaya za mu iya tabbatar da cewa; wannan littafi na Aristotle ne?

Ko shakka babu wadanda suka yi Imani da Aristotle suke karanta littatafansa da maganganunsa suke girmama su za su ji ras! Har su ce: ta yaya za a yi kokarin inkarin littafin da mutane suka hadu a kan tabbatar da shi?!

To idan har za ka yarda da littatafan Aristotle, wadanda tsakaninmu da shi yau kusan shekara 2400, kuma idan an ce: ana so a tabbatar da dangantuwar littafin gare shi babu hanyar da za a bi wajen iya tabbatar da hakan face kawai abin da aka sani bisa gado, cewa; littatafansa ne.

Amma abin mamaki, mai tabbatar da wannan littafi na Aristotle shi ne kuma mai inkarin "Sahihul Bukhari da Muslim", alhali tsakaninmu da su shekara 1200 ne. Kuma Hadisan Annabi (saw) sun samu kulawar da babu wasu maganganu da suka samu irin wannar kulawa. An samu manyan Malaman Muslunci wadanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen kiyaye Hadisan da yi musu Hidima. Inda suka samar da ka'idoji da sharuda masu karfin gaske wajen tantance Hadisan. Suna da wani ilimi da ake kira da "Ilmur Rijaal", ilimin da yake mai da hankali a kan bin diddigin Maruwaitan Hadisi da tantance gaskiyarsu da amanarsu da karfin haddarsu da iya rike magana da ruwaito ta bisa yadda take, ba tare da canji ba.

Haka kuma Malaman suka himmatu wajen rubuta Hadisan cikin littatafai, wanda ya kasance tun a rayuwar Annabi (saw), inda ya yi izini ma daya daga cikin Sahabbai da rubuta Hadisansa. Haka kuma cikin ilmuka da Malaman Hadisin suka tanada don kwalkwale ingancin Hadisi akwai "Ilmul Ilal", wato ilimin sanin boyayyiyar matsala da illa da take cikin Hadisi. Saboda ta yiwu a samu Hadisi, a zahirinsa aga kamar ingantacce ne alhali yana da boyayyar matsala. Amma Malaman Hadisi ba su yi kasa a guiwa ba wajen bin diddigi da binciken kwakwaf ma Hadisan, don banbance Hadisan da suka tabbata daga Annabi (saw), daga wadanda babu tabbacin hakan.

Akwai wata ja'irar shubuha da mabarnata suke amfani da ita idan suna son boye gaskiya, su tallata barnarsu ga jahilai, sai su ce: ai akwai siyasa a cikin kaza da kaza.. To hatta rubuta Hadisan Annabi (saw) sai da aka jefe shi da wannar ja'irar shubuha. Aka ce: ai Sarakuna ne suka sa aka kirkira musu Hadisan don biyan bukatunsu na Mulki, aka rubuta su cikin littatafai. To ta yaya mai hankalin da ya san cewa; Imamu Malik wanda ya wallafa Muwadda' an yi masa bulala. Imamu Ahmad mai littafin al-Musnad an yi masa bulala, an daure shi a kurkuku. Imamu al-Bukhariy mai littafin "Sahihul Bukhari", an kore shi daga garinsu. Duka wadannan Malamai da ire - irensu sun fiskanci hakan ne ta bangaren Sarakunan zamaninsu.

To ta yaya mai hankalin da ya san wannan zai yarda da waccar ja'irar shubuha ta siyasantar da Addini, wacce mabarnata suke amfani da ita, don boye gaskiya, da tallata barnarsu a tsakanin jahilai?!

To idan kuma aka ce: To ina asalin littatafan da wadancan Malamai suka rubuta da hanunsu?

Idan ba a samu ba, to kenan zai zama wasu ne suka rubuta, suka jingina musu su.

To sai mu koma kan maganar farko, ta magana a kan littatafan Aristotle, ina asalin kwafi da Aristotle ya rubuta da hanunsa?

Idan babu, ta yaya aka yarda da littatafan, duk da cewa; ba a samu asalin kwafi na farko ba?

Kuma yanzu littatafan nasa da suke hanu duka tarjama aka yi daga yarensa na asali zuwa wasu yarukan daban, kuma kowa ya san yadda ake iya samun canje-canjen ma'ana a dalilin Tarjama. Saboda haka idan an ce: ai almajiransa ne suka nakalto daga gare shi, su ma almajiransu suka nakalto daga gare su, haka har aka rubuta su, har suka iso gare mu, to haka su ma Littafan Hadisi suke, irin su Bukhari da Muslim da sauransu. Duk da cewa; ba za ma a hada riwayar littatafan Aristotle da littatafan Hadisi ba, saboda Muwadda' Malik, kwafi mafi tsufa da aka samu tsakaninsa da Malik kusan shekara 100 ne kacal. Haka Sahihul Bukhari ma. Amma duk da haka kowane littafi an ruwaito shi ne da Isnadi tiryan-tiryan har zuwa kan mai littafin. Shi kuma da Isnadinsa a rubuce a kowane Hadisi har zuwa Annabi (saw). Sabanin littatafan Aristotle, wanda tsakaninsa da tsohon kwafi na littafin nasa ya kai shekara 1000 bayan mutuwarsa. Amma duk da haka masu shakka a kan littatafan Hadisi ba za ka samu suna shakka a kan tabbacin littatafan Aristotle ba, duk da banbance - banbancen yaruka da Tarjama da aka samu, da kuma yadda masu Tarjamar littatafan suke tassarufi da rubuta maganganunsa da ma'ana ba da lafazinsa ba, da sauran wasu abubuwa masu tasiri wajen canza ma'ana, kuma wadanda za su sa a yi shakka wajen ingancin Nassin da aka nakalto.

A takaice, duk mai basira idan ya yi nazarin littatafan Hadisi masu inganci zai ga cewa; babu yadda za a yi wata shubuha ta sukarsu ta yi tasiri.

✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments