Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Za Ka Bi Mazhabar Malikiyya Ido Bude

YADDA ZA KA BI MAZHABAR MALIKIYYA IDO BUƊE

Asali ba a wajabta mana bin kowa ba sai bin Alkur’ani da Sunna, da Ijma'in Muminai. Shi ya sa Imam al-Shafi'iy ya ce

"إنما العلم اللازم الكتاب والسنة، وعلى كل مسلم اتباعهما.

قال: فتقول أنت ماذا؟

قلت: أقول ما كان الكتاب والسنة موجودين فالعذر عمن سمعهما مقطوع إلا باتباعهما".

الأم للشافعي (7/ 280)

"Kawai Ilimin dole a kan mutum shi ne Alkur'ani da Sunna, wajibi ne a kan kowane musulmi ya bi su.

Sai aka tambaye shi: to kai miye ra'ayinka?

Sai na ce: matukar Alkur'ani da Sunna suna nan to an yanke hanzari ga duk wanda ya ji su dole sai dai ya bi su".

To ka ga Imam Shafi'iy, almajirin Imam Malik ne, kuma jagoran Mazhabar Shafi'iyya, amma yake nuna cewa; matukar ka samu Aya ko Hadisi a kan mas'ala, to ba ka da sauran uzuri, dole ne ka bi su, ka yi aiki da su.

To yanzu don Allah idan ka samu Hadisi tabbatacce, sai ka ki binsa, sai ka bi ra'ayin Malik, miye sunanka?

Kafin mu rada maka suna bari ka ji matsayinka daga maganar Imam Malik, inda aka ruwaito

"عن معن بن عيسى قال: سمعت مالك بن أنس يقول: «إنما أنا بشر، أخطئ وأصيب، فانظروا في رأيي؛ فكلما وافق الكتاب والسنة فخذوا به، وكلما لم يوافق الكتاب والسنة فاتركوه».

جامع بيان العلم وفضله (1/ 775)

"Daga Ma'an bn Isa, ya ce: Na ji Malik bn Anas yana cewa: Ni mutum ne, ina yin dadai kuma ina kuskukre, don haka ku yi nazari a cikin ra'ayoyina, duk abin da ya dace da Alkur'ani da Sunna to ku yi riko da shi, duk abin da bai dace da Alkur'ani da Sunna ba to ku bar shi".

To yanzu idan ka ga Hadisi ya tabbata, sai ka doge a kan ra'ayin Malik ko Malikiyya, shin ka yi biyayya wa Imam Malik a cikin wannar maganar tasa?

Don haka sunanka ya zama MAI SABA WA MALIK!

Ko shi Imam Malik din Alkur'ani da Sunna yake bi, idan ka ga ya saba ma wani Hadisi to imma bai samu Hadisin ba ne, ko kuma ya samu Hadisin, amma ya saba aikin mutanen Madina ingantacce, musamman idan Hadisin mutanen wani yankin ne can daban, musamman Iraq. Ko kuma Hadisin bai inganta a wajensa ba. Amma da zaran ya samu Hadisin, kuma ya tabbata a wurinsa to nan da nan zai bar ra'ayinsa, ya karbi Hadisin ya yi aiki da shi.

Ga misali kamar haka

Imam Ibnu Abdilbarr ya ce

"ذكر أحمد بن وهب قال: حدثني عمي عبد الله بن وهب قال: سئل مالك عن تخليل أصابع الرجلين في الوضوء، فقال: ليس ذلك على الناس.

فأمهلته حتى خف الناس عنه، ثم قلت له: يا أبا عبد الله، سمعتك تفتي في مسألة عندنا فيها سنة، قال: وما هي؟ قلت: حدثنا ابن لهيعة والليث بن سعد عن يزيد بن عمرو المعافري عن أبي عبد الرحمن الحبلي عن المستورد بن شداد القرشي قال: "رأيت رسول الله يتوضأ فيخلل بخنصره ما بين أصابع رجليه".

قال فقال لي مالك: إن هذا لحسن، وما سمعت به قط إلا الساعة.

قال ابن وهب: ثم سمعته بعد ذلك يسأل عن تخليل الأصابع في الوضوء فيأمر به.

وروى غيره عن ابن وهب: فرأيته يعمل به، ولم يقل بأمره".

التمهيد لما في الموطأ من المعاني والأسانيد (24/ 258 - 259) اختلاف أقوال مالك وأصحابه (ص: 40)

"An ruwaito daga Abdullahi bn Wahab ya ce: an tambayi Malik a kan tsettsefe yatsun kafa a alola. Sai ya ce: babu shi a kan mutane.

Sai Ibnu Wahab ya ce: sai na bari sai da mutane suka watse, sai na ce masa: Ya Abu Abdillah, na ji ka kana fatawa a wata mas'ala, alahali muna da Hadisi a kanta.

Sai Malik ya ce: wane Hadisi ne?

Sai na ce: Ibnu Lahi'ah da al-Laith bn Sa'ad sun ba mu labari daga Yazid bn Amri al-Mu'afiriy, daga Abu Abdirrahman al-Hubulliy, daga al-Mustaurid bn Shaddad al-Qurashiy, ya ce: "Na ga Manzon Allah yana alola yana tsettsefe yatsun kafansa da 'yar karamar yatsar hanunsa".

Sai Malik ya ce min: Lallai wannan Hadisi ne mai kyau, amma ban taba jinsa ba sai yanzu.

Ibnu Wahab ya ce: sai daga baya na ji ana tambayarsa game da tsettsefe yatsun kafa yana yin umurni da shi.

A wata riwayar kuma cewa ya yi: sai ya gan shi yana aiki da Hadisin, amma bai fadi cewa yana umurni da shi ba.

To ya kai dan Malikiyya, ka ga dai yadda Imamu Malik din namu yake da Hadisi, matukar Hadisi ya tabbata a wajensa to zai yi aiki da shi.

Saboda haka wannan shi yake nuna yadda Ahlus Sunna suke bin Mazhaba, da zaran Hadisi ya tabbata to sukan ajiye ra'ayin Malikiyya wanda ya saba wa Hadisin.

Don haka yadda ake bin Malikiyya ido bude, shi ne ka sanya Alkur'ani da Hadisi su ne abin bi, don haka da zaran ka ga Hadisi ya inganta a wata mas'ala, kuma akwai banbanci tsakanin Hadisin da ra'ayin Malikiyyar, to ka bar ra'ayin Malikiyyan, ka yi riko da Hadisin, ka yi aiki da shi.

Kuma fa kar ka manta, ba dukkan ra'ayoyin Malikiyya a yau su ne ra'ayin Malik ba, akwai ra'ayoyi da yawa Malaman baya ne suka yi Ijtihadi suka tabbatar da su. Don haka ta yaya za ka gabatar da ra'ayin wani wanda ba Malik ba a kan Hadisi, alhali shi ma Malik din cewa ya yi: idan ra'ayinsa bai dace da Alkur'ani da Sunna ba to kabar shi, to ina kuma ga ra'ayoyin Malaman da suka zo bayan Malik?!

Shi ya sa mu 'yan Malikiyya muke jin takaici idan muka ji mutum yana raya bin Malikiyya, amma kuma ya saba wannan Manhaji, ya koma taqlidanci da ta'assubanci wa Mazhabar.

✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments