'YAN SALAFIYYA DA MURNAN TAWAYE WA SHUGABA?!
Abu ne sananne cewa Ingila ce ta je ta samu kasar Musulmi Larabawa Falasdinawa, ta share wuri, ta kafa kasar Izra'ila wa Yahudawa. To kamar haka Faransa ta je Syria ta dauko 'yan tsirarun kafirai, daga kan duwatsu, 'Yan Shi'a Nusairiyya, ta ba su mulkin Syria. Alhali Syria kasa ce ta Musulmai Ahlus Sunna. Ta yadda Faransa ta dinga daukar 'Yan Nusairiyyan, tana shigar da su aikin soja, inda suka yi yawa, suka yi karfi a rundunar sojin kasar, aka daga su, suka zama su ne manyan sojoji, su ne janarori, sannan aka yi ta kakkabe Sojoji Musulmai, har sai da karfin soji gaba daya ya koma hanun 'yan Shi'a Nusairiyyan.
Haka kuma suka yi kane-kane a cikin jam'iyyar
"Ba'ath", suka kori sauran Larabawa da suke ciki.
A shekarar 1966 aka yi juyin mulki a kasar, aka
nada Hafizul Asad a matsayin Ministan Tsaro. A shekarar 1970 kuma shi Hafizul
Asad ya mamaye karagar mulki, ya tabbatar da kansa a matsayin shugaban kasa.
Wannan Hafizul Asad din, mahaifin Bassharul Asad,
dukansu 'yan kungiyar Shi'a Nusairiyya ne. Kungiyar da ta shahara da Akidun
kafirci. Malamin Shi'a al-Naubakhtiy ya ce
"وقد شذ فرقة من القائلين بإمامة علي بن محمد (ت ٢٤٥ ه-) في
حياته، فقالت بنبوة رجل يقال له "محمد بن نصير"، وكان يدعي أنه نبي بعثه
أبو الحسن العسكري. وكان يقول بالإباحة للمحارم، ويحلل نكاح الرجال بعضهم بعضا".
فرق الشيعة للنوبختي (ص: ٧٨)
Ma'ana: Nusairiyya 'yan Shi'a Imamiyya ne, amma
sun fandare, tun Imaminsu Aliy bn Muhammad yana raye, wanda ya rasu a shekara
ta 245. Suka ce: -wai- wani mutum mai suna Muhammad bn Nusair Annabi ne, Abul
Hassan al-Askariy (Baban Mahdi) shi ne (Allahn) da ya aiko shi a matsayin
Annabi. Suna halasta haramun, har suna halasta auren namiji da namiji.
Matane ne masu miyagun Akidu masu yawa, wadanda
kowane daya kafirci ne. Daga cikinsu akwai
1- Akidar "Hululi" da
"Ittihadi", da Allantar da Sayyidina Aliyu, da sauran Imamai.
2- Soke farillan Addini, da halasta wa mutane
komai na haramun.
3- Akidar "Tanasukh", cewa: fatalwar
wanda ya mutu tana dawowa duniya ta shiga jikin wani mutum ya rayu.
4- Karyata tashi bayan mutuwa, da wuta da Aljanna.
5- Fassara Nassoshi da hukunce - hukuncen Muslunci
fassara ta "Badiniyya". Sai su ce: abin da ake nufi da Salloli biyar
shi ne Aliyu, Hassan, Hussain, Muhsin, Fatima.
Shi ya sa da aka tambayi Ibnu Taimiyya a kansu,
bayan an zayyana masa miyagun Akidunsu sai ya ce
"هؤلاء القوم المسمون بالنصيرية - هم وسائر أصناف القرامطة
الباطنية - أكفر من اليهود والنصارى، بل وأكفر من كثير من المشركين".
النصيرية لشيخ الإسلام (ص: ١٢)
Ma'ana: 'yan Shi'a Nusairiyya - da sauran 'yan
Shi'a Badiniyya - sun fi Yahudu da Nasara kafirci. Kai, sun fi da yawa cikin
Mushrikai kafirci.
Saboda haka bisa hakika 'yan Shi'a Nusairiyya ba
Musulmai ba ne. Faransa ce ta dauko su daga kan duwatsu, ta ba su mulkin Syria.
Saboda haka, mulkin da Hafizul Asada, da dansa
Bassharul Asad suka yi, Musulmai a Syria sun kasance ne a karkashin mulkin
Zindikai, wadanda sun cancanci hukuncin kafirci. Don haka alal hakika ba su da
hakkin shugabanci a kan Musulmai. Kawai Musulmai suna zaune ne a karkashin
mulkinsu bisa larura. Don haka duk lokacin da Musulmi suka samu karfin kawar da
su to wajibi ne su kawar da su.
A ka'idar Muslunci, ba a tawaye wa shugaba Musulmi
matukar yana tsayar da Sallah, komai zaluncinsa. Amma ya halasta a yi tawaye wa
shugaban da kafircinsa ya bayyana a fili, amma da sharadin idan ana da karfi da
iko. Wato idan tawayen zai samar da maslha, a kawar da barna, ya haifar da da
mai ido.
Amma matukar ba za a samu maslaha ba, barna za a
samu, ko kuma barnar ta fi maslahar da za a samu girma da yawa, to bai halasta
a yi wa wannan shugaba kafiri tawaye ba. Don gudun afkuwar barna da asarar
jinane da dukiyoyi.
Kuma ita maslaha da mafsada ba ka'ida ce guda daya
ba, a'a, ana gane maslaha da mafsada ne ta hanyar ijtihadi. Masana ne za su yi
dogon nazari, su lura da kowane lungu na matsalar, sai su iya gano sakamakon da
zai biyo bayan tawayen, na maslaha ko barna. Don haka ta yiwu a yi tawaye a
bara, ya zama barna da mafsada, sai a yi masa hukunci da rashin halasci, amma
idan aka yi a bana kuma sai ya zama alheri da maslaha. Sai ya zama halas, kuma
aiki mai kyau. Ba haka kawai "gauga'u" su tunzura mutane a fito zanga-zanga
ba, alhali babu shiri, ba nazari da hangen nesa, ba tanadin komai.
Saboda haka, abin da ya faru a Syria, na tawaye wa
Asad, shekara 13 da suka wuce, ba a samu maslaha a cikinsa ba, sai barna mai
girma. Kowa ya ga irin barnar da ta faru, abin da zai sa dole ana hangen nesa
sosai, kafin yin tawaye wa shugaba kafiri.
Amma abin ya faru yanzu kuma, kowa ya ga cewa an
samu maslaha da cin nasara, sakamakon karfi da iko, da shiri da hangen nesa,
bayan an tabbatar Asad karfinsa ya kare, kawayensa Rasha da Iran sun kwaye masa
baya, sun ki taimakonsa.
A takaice abin da wasu - musamman masu dauke da
gubar Akidar bore da "thaura" ta Sayyid Qutub - suke zato game da
'yan Salafiyya, masu haramta tawaye wa shugaba, na yin tufka da warwara, rashin
fahimta ce ga Manhajin na Salafiyya.
Amma sauran 'yan bidi'a kuma shagubensu ba abin
lura ba ne, saboda kiyayyarsu ga tafarkin Salaf ne ya saka su haka.
Saboda haka muna taya Musulman Syria murnan
nasarar tawaye da suka yi wa Asad, har Allah ya ba su nasara. Allah ya hada
kansu, ya ba su zaman lafiya.
✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.