Ticker

    Loading......

Yana So Na Da Aure Amman Ya Ki Ya Nuna Min Danginsa

YANA SO NA DA AURE AMMAN YA ƘI YA NUNA MIN DANGINSA

TAMBAYA (251)

Asalamu alaikum malan ina wuni fatan kuncha kuwa lfy malan ina da tambaya muna soyaya da sarmayina kuma yana sona ya zo ka gabatar da kanchi an sanchi gidanmu anma ni kuma baitafa nuna mani dan ginchi ba kuma da aure yake sona chin zan iya tambaya chi

AMSA

Waalaikumus salam

Kin taba ganin inda ankayi cinikin biri a sama ?

Shawarar da zan baki anan ita ce

Ki ce masa ke ma kina bukatar sanin asalin sa da iyayen sa da kuma yan uwansa

Idan yace miki ba damuwa ba dole bane sai kin san su ba to daganan za ki gane cewar yana kokarin boye wani abun ne

Yar uwa, Allaah ya jikan ki da rahama. Shi lamarin aure fa ya zarce yanda kike tunani

An sha samun tambayoyi makamanta wadannan kuma karshe idan ba'ayi amfani da shawarar da aka bayar ba sai ka ga ana ta da na sanin wannan auren saboda an dora auren ne akan gwadabe da turbar rashin gaskiya

Don haka in dai kina son ki samu kwanciyar hankali to ki tabbatar da cewar kin san danginsa kamar yanda yasan naki

Wallaahu taala aalam

Masu bukatar shiga Telegram Class na littafin "KURA KURAI 100 A CIKIN SALLAR MU", ku shiga Telegram kuyi searching:

USMANNOOR ACADEMY

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments