Ticker

6/recent/ticker-posts

'Yar'uwa Ki Ji Tsoron Allah

'YAR'UWA KI JI TSORON ALLAH!

Akwai wata mummunar Fikra wacce take ta kara yaduwa a cikin mutane, musamman mata da kuma matasa maza, fikrar da take da tushe daga Akidar Murji'a. Amma yanzu an dauko ta ne cikin sabuwar riga, daga kungiyoyin Fikrorin Turawa, wadanda 'Yan Boko Aqida suka yi dakonsu, suke yada su cikin al'ummar Musulmi.

Wannar fikra ita ce fikrar bai ma kowa 'yancin aikata abin da yake so, cikin aiyukan da Allah ya hana aikatawa, na alfasha da munkari.

A yanzu ba dama ka yi inkarin mummunan aiki ga wata mace, kamar dora hotunan tsiraici, ko bidiyon rawa a dandalin sada zumunta, face ta yi maka martani da cewa

"Kabarinka daban, nawa daban".

Ko ta ce

"Kar ka shiga rayuwata, ka yi harkarka, na yi nawa".

Ko ta ce

"Ni ban shiga rayuwar kowa ba, kar kowa ya shiga rayuwata".

Ko ta ce

"Ku kyale kowa ya yi rayuwarsa yadda yake so".

Ko kuma ta ce

"Imani fa a zuciya yake".

Ko ta ce

"Kai wa ya san abin da kake aikatawa a boye".

Ko ta ce

"Rahmar Allah tana da fadi".

Da sauran ire-iren wadannan kalamai, suna nan da yawa.

To ya ke 'yar'uwa, na san dai kin san cewa Allah ya haramta alfasha da munkari.

Kuma kin san Allah ya tanadi azaba ta Lahira a kan haka, ko ma tun daga nan Duniya.

Kuma kin san mutuwa ba ta sallama, balle bayar da sanarwa idan za ta zo.

Kuma kin san Allah ya wajabta hani a kan mummunan aiki da inkarin munkari.

Kuma kin san bayyana mummunan aiki da sabo a fili suna cikin aiyukan da Allah ya fi yin fushi da su, kuma yake hana afuwarsa ga masu aikatawa.

'Yar'uwa, ko kin san dalilin da ya sa Allah ya tsine wa Kafiran Bani Isra'ila kuwa?

Ko kin san dalilin da ya sa Allah ya daukaka al'ummar Annabi Muhammad (saw), ya fifita ta a kan sauran al'ummomi kuwa?

Allah ya tsine wa Kafiran Bani Isra'ila ne saboda ba sa hana juna aikata munanan aiyuka.

Allah ya daukaka al'ummar Annabi Muhammad (saw) ne, ya fifita ta a kan sauran al'ummomi saboda suna umurni da kyakkyawa, suna hani ga mummuna, suna Imani da Allah?

To idan fa muka canza, muka dena umurni da kyakkyawa, da hani ga mummuna, to fa zamu rasa falalar al'ummar Annabi (saw), mu cancanci irin tsinuwar da Allah ya yi wa Kafiran Bani Isra'ila.

Haba 'Yar'uwa, ko ke ma kina da mummunar Akidar nan ce, ta cewa: masifun da suka same mu a yau, na Kidnapping, rashin tsaro, bala'in talauci da tsadar rayuwa da samun shugabanni marasa tausayi ba su da alaka da munanan aiyukan da muke aikatawa ne?!

Allah fa ya fada mana a wurare da yawa a cikin Alkur'ani, cewa; bala'o'i da suke faruwa sababinsu shi ne miyagun aiyukan da muke aikatawa ne.

Annabi (saw) ya yi mana misali mai kyau don mu gane. Wato misalin masu hana ki aikata munanan aiyuka na alfasha da munkari, ta yadda ya yi mana bayanin cewa; kamar fasinja ne a cikin jirgin ruwa mai hawa biyu, hawa na sama da na kasa. To idan mutanen hawa na kasa suna bukatar ruwa, a maimakon su hawo sama, su samu hanyar fita su debo ruwan, sai suka ce: bari mu bula jirgin ta kasa, ruwan ya shigo mana ba tare da mun damu wadanda suke hawa na sama da mu ba.

To yanzu, shin ya kamata a kyale wadanda suke hawa na kasa su bula jirgin, don ruwa ya shigo musu?

Idan fa aka kyale su suka bula jirgin, to ruwa zai shiga jirgin ya cika shi, daga nan kuma sai jirgin ya yi kasa ya nitse a Teku, kowa ma ya mutu a huta.

Lallai hani a kan munanan aiyuka shi yake kare al'umma daga halaka da bala'o'i iri-iri.

Don haka 'yar'uwa ki ji tsoron Allah! Ki dena aikata mummunan aiki, balle ki yada, ballantana kuma har ki yi mummunan martani ga mai hana ki aikatawa.

✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments