Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Iya Tsallake Masallacin Anguwanmu Don Yin Sallar Tarawih

TAMBAYA (224)

Assalamualaikum. Mln ya hukuncin Wanda yake tsallake masallacin dake unguwarsa ya yafi wani masallacin sallar tarawiyyi ko tahajjud

AMSA

Ya halatta ka je kowanne masallachi amman ya zamana limamin yana sallah ne irin yanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya koyar dogaro da hadisin: "Kuyi sallah kamar yanda kuka ga ina yi"

(Bukhari da Muslim)

Inda zaka zamo abin tuhuma shi ne idan kana cikin masallachin aka kira sallah sai kuma ka fita hakanan ba tare da wani dalili ba. Wannan ka aikata laifi saboda hadisi na 10,946 dake cikin Musnad na Imam Ahmad (Rahimahullah) wanda Abu Hurairah (Radiyallahu anhu) ya ce: Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya umarce mu da kada mu fita daga masallachi idan an kira sallah har sai anyi sallar tare da mu

Shu’ayb al-Arna’oot ya sahhaha hadisin a cikin Tahqeeq al-Musnad din sa

Ga kuma hadisin Abu’l-Sha’tha’ wanda ya ce: Muna tare da Abu Hurairah bayan an kammala kiran sallah a masallachi sai wani mutum ya tashi ya fita daga masallachin, sai Abu Hurairah ya dinga kallon sa har ya fice sai ya ce: Wannan mutumin ya bijirewa umarnin Abul Qasim (Sallallahu alaihi wasallam)

Dangane da fitowa kai tsaye daga gida zuwa masallachi kuma, akwai garabasar samun lada dayawa idan aka je masallachi mai nisa saboda duk sanda kayi taku daya Allaah zai sa a rubuta maka lada sannan a kankare maka zunubi daya kamar yanda muka karanta hadisin a cikin littafin SIFATU SALATIN NABY

Shiyasa malamai sukai magana akan illar yawaita gina masallatai da yawa a anguwa daya musamman na Juma'a domin kuwa hakan na iya janyo rarrabuwar kai da kuma bude kofar kungiyanci

Duk da cewar wasu suna ginawa ne don a raya dakunan Allaah to amman anan sai malamai suka ce mutum ya zabi masallachin da aka fi cika domin kuwa munada hadisin Ubayy Ibn Ka'ab (Radiyallahu anhu) wanda ya ce: Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: "Mutum ya yi sallah tareda wani shi yafi akan ya yi shi kadai, yin ta da wasu su biyu shi yafi akan ya yi da mutum daya, iya adadin yawan masu sallah shi ne yawan farin ciki da Allaah yake"

Abu Dawood (554) da an-Nasaa’i (843); Shaikh al-Albaani ya sahhaha shi a cikin Saheeh Abi Dawood

Wannan kuma ita ce amsar da Shaykh Muhammad ibn Saalih al-‘Uthaymeen (Rahimahullah) ya bayar a cikin: Ash-Sharh al-Mumti‘ ‘ala Zaad al-Mustaqni‘ 4/150-151

Wallaahu taala aalam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments