Ticker

    Loading......

Zan Yi Tafiya Daga Bayelsa Zuwa Kaduna Shin Zan Iya Shan Azumi

ZAN YI TAFIYA DAGA BAYELSA ZUWA KADUNA, SHIN ZAN IYA SHAN AZUMI?

TAMBAYA (216)

Akwai yiwuwar gobe Asabar za a dauki azumi ni kuma goben zan dawo Kaduna daga Bayelsa, shin zan iya ajiye azumin sai bayan sallah na rama ?

AMSA

Waalaikumus salam, warahmatullahi, Waalaikumus salam

Babu wahala a cikin addini

Indai har za ka takura musamman la'akari da tafiyace daga kudancin Nigeria zuwa Arewaci to ya halatta ka ajiye azumin

Daga Bayelsa zuwa Kaduna tafiya ce ta kilometers 654, za ka iya ajiye shi, ka rama shi bayan sallah dogaro da fadin Allaah Azzawajallah:

( أَيَّامًا مَّعْدُودَاتٍ ۚ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ أُخَرَ ۚ وَعَلَى الَّذِينَ يُطِيقُونَهُ فِدْيَةٌ طَعَامُ مِسْكِينٍ ۖ فَمَن تَطَوَّعَ خَيْرًا فَهُوَ خَيْرٌ لَّهُ ۚ وَأَن تَصُومُوا خَيْرٌ لَّكُمْ ۖ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ )

البقرة (184) Al-Baqara

Kwanuka ƙidãyayyu. To, wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana a kan tafiya, sai (ya biya) adadi daga wasu kwanuka na dabam. Kuma a kan waɗanda suke yin sa da wahala akwai fansa; ciyar da matalauci, sai dai wanda ya ƙãra alhri to, shi ne mafi alhri a gare shi. Kuma ku yi azumi (da wahalar) ne mafi alhri a gare ku idan kun kasance kuna sani

Wallaahu taala aalam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments