Ticker

GAME DA MU


1.0 Matashiya
Tuni Hausa ta yi fintinkau ga sauran takwarorinta (Harsunan Nijeriya) ta fuskar yaɗuwa da kuma bunƙasa. Wannan ɗaukaka da harshen ya samu bai tsaya ga farin jini da sauƙin koyon da yake da shi ba kawai, har ma da gata da ya samu daga nazarce-nazarce da rubuce-rubucen da Turawa suka gudanar cikinsa. Wani dalili na bunƙasar harshen shi ne yadda ake nazarin sa a jami’o’in cikin gida da na ƙasashen waje daban-daban. A waɗannan ɓangarori, sai dai a ce Allah son barka.

A ɗayan ɓangare kuma, duniya juyi-juyi ce… Sauyin zamani, musamman abin da ya shafi intanet, ya ɓullo da wata barazana ga harshen. Haƙiƙa ya tabbata cewa, harshen da kaɗai cigabansa zai ɗore a halin yanzu shi ne, wanda a ƙalla, ake jin ɗuriyarsa a intanet. Kash! A wannan fanni kuwa, tuni aka yi wa Hausa fintinkau. Lallai kuwa, bai dace masu kishin harshen su yi ƙasa a guiwa ba wajen ganin harshen ya shiga jeriyar gudun ya-da-ƙanin-wani wanda ake falfalawa a wannan fanni. Saboda haka ne aka ƙuduri samar da kafar intanet da za ta riƙa tattara rubutun masana da manazarta harshen Hausa. Hakan zai samar da ƙarin kutsen harshen cikin sassan duniya tare kuma da samar da wata kafa ta binciken al’amuran da suka shafi harshen cikin sauƙi.

2.0  Ƙuduri
Ƙudurin wannan kafar intanet shi ne, tattara rubuce-rubucen masana da manazarta cikin harshen Hausa, domin yaɗa harshen da kuma sauƙaƙa wa masu neman bayanai game da lamurra daban-daban da suka shafi harshen.

3.0 Manufa
Wannan kafar intanet na da manufofi kamar haka:
  1. Sanya harshen Hausa cikin jerin harsunan duniya da ke taka rawar gani a kafar intanet.
  2. Samar da wani rumbu na rubuce-rubucen ilimi cikin harshen Hausa a kafar intanet.
4.0 Ayyuka
Ayyukan da wannan kafa za ta riƙa gudanarwa sun haɗa da:

  1. Tattara rubuce-rubucen masana da manazarta cikin harshen Hausa, shirya su tare da ɗora su a kafar intanet domin duniya ta riƙa gani da kuma amfani da su.
  2. Samar da bayanai kan harshe da al’ada da adabin Hausawa domin sanin marasa sani da ƙara sanin masu sani. 
  3. Karɓar tambayoyi daga masu ziyarar kafar tare da ƙoƙarin samar da amsoshinsu cikin lokaci. 
  4. Ɗora abubuwan nishaɗi cikin harshen Hausa waɗanda suka haɗa da labarai da wasa ƙwaƙwalwa da kacici-kacici da almara da makamantansu.
5.0 Kira
Ana maraba da rubutun Hausa na ilimi kowane iri domin sakawa a wannan kafa. Za a iya turo rubutun ta ɗaya daga cikin hanyoyin nan:
  1. official@amsoshi.com   
  2. Contact
Sannan muna maraba da shawarwari ko gyara game da kura-kuranmu.

Mun gode.

Post a Comment

2 Comments

  1. Naji dadin ganin wannan rubutun Allah yasa manyan mu hausawa zasu suyi kokari wajen sa harshen ajerin manyan harshen duniya Allah ya daukaka yaren hausa da hausawa

    ReplyDelete
  2. Abdulrashid S.Pawa Gusau14 August 2021 at 20:02

    Masha Allah. A gaskiya wannan kafa mai suna Amsoshi tana da matukar muhimmanci ba wai ga dalibai masu nazarin harshen Hausa ba a'a hatta ga duk wani mai amfani da harshen Hausa a ko'ina yake a fadin duniya zai amfana da wannan kafa wadda ta tara ilimi a cikinta. Don haka muke godiya ga wanda ya assasa wannan kafa wato Abu-Ubaida Sani Allah ya kara mai hazaka da basira amin. Bayan haka muna mika godiyarmu maras adadi ga malamai masana harshen Hausa musamman malami uban malamai wato Farfesa Aliyu Muhammad Bunza Allah ya karamai lafiya da tsawon rai da kuma, daukaka amin.
    Daga karshe ina ma wannan kafa fatan alheri, ni ne dalibin harshen Hausa Abdulrashid S Pawa Gusau (B.A Hausa. FUG graduand 2019).

    ReplyDelete

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.